Kungiyar Hamas wacce take fafatawa da HKI a Gaza, da kuma yankin yamma da kogin Jordan ta bayyana cewa, HKI tana shirin kara mamayar kasashen larabawa tare da kasar Falasdinu da ta rika ta mamaye.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Usama bin Hamdan wakilin kungiyar a kasar Lebanon yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa: Ya yi wannan maganar ne, bayan ya ga wasu shafukan sadarwa na gwamnatin HKI dauke da wasu hotuna wadanda suka nuna taswiran kasashen larabawa, daga cikin har da Falasdinu, Jordan, Lebanon da Siriya a matsayin Isra’ila baba.
Hamdan ya kara da cewa wannan taswiran ya nuna cewa HKI wata kasa yarmulkin mallaka ce wacce take son ta mamaye Karin kasashen larabawa tare da taimakon kasashen yamma.
Daga karshe kungiyar ta bukaci kasashen larabawa, musamman kungiyar kasashen larabawa, da kuma kungiyar kasashen musulmi su dauki matakan gaggawa don kawo karshen burin HKI na mamayar Karin kasashen larabawa.
Labarin ya kammala da cewa, Bezalel Smotrich ministan cikin gida na hKI ya fidda wannan taswiran ne bayan da HKI ta bayan da hKI ta kara jaddada bukatar fadada kasar a cikin kasashen larabawa.