Tashar talabijin din HKI ta 12; ta bayar da labarin dake cewa, ana tsammanin cewa kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas za ta fitar da sunayen Karin farusunonin da za ta kara sani a yau Juma’a.
Fira ministan HKI Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa zai yi aiki da sharuddan yarjejeniyar da aka cimmawa ta musayar fursunoni a tsakaninsu da kungiyar Hamas, ta hanyar shiga tsakanin kasahen Katar da Masar.
A gobe asabar ne dai ake tsammacin sakin wani Karin fursunoni daga kungiyar Hamas, domin yin musayarsu da wasu fursunonin Falasdinawa dake kurkukun HKI.
Gabanin musayar fursunoni na farko da aka yi a makon da ya gabata, kungiyar gwgawarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce, a karo na biyu za ta hada da wasu fursunonin mayakan Hizbullah da HKI ta ce, tana rike da su.
A shekaran jiya Laraba kungiyar Ansrullah ta kasar Yemen ta sanar da sakin matukan jirgin ruwan da take rike da shi, tun a farkon yaki a karkashin cimma matsaya da kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas.
Da akwai daruruwan Falasdinawa da suke a cikin gidajen kurkukun HKI da kafi yawancinsu ana tsare da su ne ba tare da an yi musu shari’a ba, da su ka hada kananan yara da mata.