Kungiyar Hamas Ta Yi Gargadin Mugun Nufin Gwamnatin Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi gargaɗi game da sake dawo da manufofin Isra’ila na kakaba yunwa a Gaza A cikin wata sanarwa da

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta yi gargaɗi game da sake dawo da manufofin Isra’ila na kakaba yunwa a Gaza

A cikin wata sanarwa da ƙungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta fitar ta bayyana cewa: “Matakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta ɗauka a halin yanzu shi ne sake dawo da mummunan manufofinta na kakaba yunwa a kan mutanen yankin Gaza, kuma hakan ya nuna rashin ƙarfin gwiwar ƙasashen duniya da kuma haɗin gwiwar Kwamitin Tsaro da cibiyoyinta na hana wannan mummunan manufa ta Isra’ila.”

Kungiyar Hamas ta bayyana cewa: Rashin hukunta sojojin mamayar Isra’ila bisa laifukan kakaba masifar yunwa kan Falasdinawa da suka aikata a baya ya ƙarfafa ta kan ƙoƙarin sake maimaita irin wannan laifi.

Ƙungiyar ta yi kira ga ƙasashen Larabawa musamman hukumominsu da kuma kungiyoyin jama’a da su dauki matakin ganin sun hana mahukuntan Isra’ila maimaita wannan munanan  manufofinta na kakaba masifar yunwa kan al’ummar Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted