Kungiyar Hamas wacce takr iko da Gaza kuma take gwagwarmaya da HKI tun shekara ta 2023 a baya-bayan nan, ta bayyana cewa ba za ta ajiye makamanta ba sai an kafa kasar falasdinu mai zaman kanta, wanda yin watsi ne da bukatar HKI na shafe kungiyar daga doron kasa.
Shafin labarai na Internet Arab News na kasar Saudiya ya nakalto kungiyar tana fadar haka bayan da taron tattaunawa ta tsagaita budewa juna wuta na kwanaki 60 ya tashi baram-baram a birnin Doha na kasar Qatar.
Labarin ya kara da cewa, a ranar Talatan da ta gabata ce, kasashen Qatar da Masar suka amince da ra’ayin samar da kasashe biyu a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, a matsayin hanya Tilo ta warware rikicin Falasdinawa da yahudawan HKI, sannan a lokacin ne Hamas zata mika makamanta ga gwamnatin jeka na yika ta Palasdinawa waccea take samun goyon bayan kasashen yamma da kasashen larabawa.
Amma kungiyar Hamas ta amsawa wadannan kasashe kan cewa kungiyar ba zata taba ajiye makamanta ba, sai bayan an kafa kasar Falasdinu mai cikekken yenci da kuma birnin Qudus a matsayin babban birnin Qasar.
HKI tana ganin duk wata yarjeniyar da za’a cimma da Hamas idan bai hada da karbe makamanta b aba abin amincewa ne gareta ba.