Kungiyar Hadin Kan Kasashen Sahel (AES), wadda ta kunshi Mali, Nijar, da Burkina Faso, ta yi Allah wadai da “kame shugaban Venezuela Nicolás Maduro da matarsa da Amurka ta yi.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta AES ta danganta lamarin da “mummunan aiki da ya saba wa dokokin kasa da kasa.”
Haka zalika kasashen wadandu suk sojoji ke mulki sun nuna damuwa game da sakamakon irin wannan aikin ga zaman lafiyar duniya, tare da nuna goyan bayansu ga kasar Venezuela da al’ummarta.
Sun kuma yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya da ya “yi Allah wadai da matakin sojan na Amurka” da kuma yin aiki don “dawo da dokokin kasa da kasa.”
Dama dai kafin hakan Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini game da matakin Amurka na kame shugaban Venezuela Nicolas Maduro da matarsa a ranar cikin daren Juma’a wayewar ranar Asabar.
A ranar 3 ga watan Janairu ne AMurka ta kai jerin hare hare kan kasar ta Venezuela, tare da kame shugaban kasar Nicolas Maduro da matarsa.
Amurka ta gurfanar da su a gaban wata kotun birnin New York kwanaki biyu bayan kame su tana mai zargin Maduro da safarar miyagun kwayoyi.