shaikh Nazem al-saeedi babban kwamanda a kungiyar al-nujaba movementa ta kasar iraki ya jinjinawa alummar kasar game da tsayin Dakar da suna nuna wajen gudanar da zanga zangar lumana don tilastawa gwamnatin kasar barin jiragen saman kasar iran su ci gaba da sauka a birnin Najaf mai tsarki, bayan dakatar da su da ta yi sakamakon takunkumin da amurka ta sanya wa iran
a cikin wani bayani da ya fitar a jiya juma’a al-saeedi yace na gode ma dukkan wadanda suka kasance a zaman drishan da aka yi a filin saukar jiragen sama na birnin Najaf mai tsarki domin nuna rashin amincewa da matakin da gwamnati ta dauka, da kuma nuna goyon bayansu ga gaskiya da kuma yan uwansu kuma makwabtansu.
haka zalika yayi gargadi ga Amurka da sauran yan koranta cewa alummar iraki ba za su ji kyashin daukar mataki mafi karfi ba a nan gaba idan amurka ta ci gaba da killace filin saukar jiragen sama na kasar Iraqi, ya kamata kowa ya sani cewa babu wanda ke da ikon kakabawa kasar iraki wata doka ko a bita idon rufe, kuma babu ja da baya game da kare martabar kasar
kuma wannan mayar da martani ya zo ne bayan sanarwar da ofishin fira ministan kasar Iraqi ya fitar a jiya juma’a na nuna amincewa da jiragen saman kasar iran su ci gaba da zirga zirga a kasar har sawu 40 a kowacce rana a filin saukar jiragen sama na birnin Najaf mai tsarki