Kungiyar tarayyar turai ta dauki wannan matakin na saye da shigar da zinariyar da ta fito daga kasar Sudan domin rage yadda wutar yaki take ci gaba da ruruta.
Matakin da aka sanar da shi a jiya Litinin ya kunshi saye, jigila, aikewa da sanadarorin “Mercury” da ” Cyanide” zuwa kasar Sudan da su ne ake amfani da su wajen hako ma’adanai.
Zinariyar kasar Sudan tana taka gagarumar rawa wajen taimakawa masu jagorantar yaki a kasar a tsakanin sojoji da kuma rundunar kai daukin gaggawa.
Tun daga barkewar yaki a cikin Sudan a 2023 dubban mutane ne su ka rasa rayukansu, yayin da wasu miliyoyi su ka zama ‘yan hijira.
MDD ta bayyana cewa kasar Sudan tana fuskantar matsala agaji mafi girma a duniya.