Kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta fara tattaunawa don samar da makamashi wanda ko wace kasa a duniya tana iya samunsa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasdar Iran ya nakalto sanarwan da kasashen kungiyar suka fitar dangane da haka a taron kwanaki biyu da suke gudanarwa a kasar Rasha. Kungiyar ta bayyana cewa makamshi shi ne ginshiki na raya tattalin arziki a duniya, kuma ba wata kasar da zata sami ci gaba sai tare da asashen makamashi.
Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar sun bayyana haka a taronsu na jiya litinin 10 watan Yuni da muke ciki. Sun kuma kara da cewa da farko suna bukatar samar da makamashi a cikin kasashen kungiyar.
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ne yake jagorantar taron ministocin na wannan karon a birnin Nizhny na kasar Rasah. Kuma sauran kasashen kungiyar sun hada da Brazil, Russia, India, China, da kuma Afirka ta kudu. Sai kuma kasashen da suka shiga kungiyar a farkon wannan shekarar kuma sun hada da Iran, Habasha, Masar, da kuma Hadaddiyar daular larabawa. Kungiyar sun bukacu Saudia ta shiga kungiyar a cikin shekara ta 2023.
Ya zuw ayanzu dai kungiyar Brics ta wuce sauran kungiyoyin tattalin arziki a duniya wadanda kasashen yamma suke mamaye da su.