Majalisar kungiyar ta “Brics” wacce Iran memba ce a cikinta ta yi zamanta na farko a cikin wannan shekara ta 2024 inda ta tattauna halin da ake ciki a Gaza, tare da yin kira da a kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa.
A jiya Alhamis da dare ne dai majalisar kungiyar ta “Brics” ta yi taronta a kasar Rasha, wanda ya kunshi sabbin kasashe mambobi 10, inda bayan maraba da su aka kuma tattauna yakin Gaza, da bijiro da bukatar ganin an dakatar da laifukan da HKI take tafkawa.
Wanda ya wakilci Iran a wurin wannan taron shi ne Ibrahim Rizai wanda mamba ne a kwamitin alakar waje da Rasha a majalisar shawarar musulunci ta Iran, ya kuma yi bayani akan manyan laifukan yakin da HKI take tafkawa Gaza, tare da bukatar ganin ana kawo karshensu.
Da yake magana ta bayan fage da manema labaru, wakilin na Iran Ibrahim Rizai ya ce, daya daga cikin muhimman ayyukan da suke a gaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran shi ne kawo karshen kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi a karkashin umarnin Amurka.
Wani sashe na jawabin wakilin na Iran shi ne yin kira ga ita kanta kungiyar ta “Brics’ da ta yi amfani da matsayar da take da ita domin rage jinginuwa da dogaaro da cibiyoyin tattalin arziki na kasashen turai.
Haka nan kuma Rizai ya bukaci ganin kungiyar ta karfafa kanta da kafa kawancen kalubalantar munanan manufofin yammacin turai.