Jim kadan bayan da kungiyar kai Dauki Gaggawa ta kasar Sudan ta sanar kafa gwamnatin mai mambobi 15, kungiyar tarayyar Afirka ta mayar da martanin kin amincewa da ita.
Bugu da kari kingiyar ta tarayyar Afirka ta kira yi kasashen da suke mambobi a cikinta da kuma kungiyoyin kasa da kasa da kar su amince da halarci wannan gwamnatin.
Har ila yau kungiyar ta tarayyar Afirka ta kuma yi gargadin cewa matakin da kungiyar ta RSF ta dauka zai iya tarwatsa Sudan ya kuma rusa Shirin zaman lafiya wanda dama yana tangal-tangal.
Kungiyar ta RSF ta bayyana Muhammad Hassan al-Ta’aysh a matsayin Fira ministan, sai kuma Janar Muhammad Dagalo a matsayin shugaban kasa.
Kasar Sudan ta fada cikin yaki ne tun a 2023 a tsakanin sojoji da rundunar kai daukin gaggawa RSF.
Sojojin kasar dai su ne ke iko da babban birnin kasar Khartum da kuma mafi yawancin yankin Arewacin kasar, gabashinta da kuma tsakiyarta. Ita kuwa kungiyar RSF tana iko da yankin Darfur da wani sashe na Kurdufan.
Kungiyar ta tarayyar Afirka ta bayyana cewa, kafa gwamnatin adawa a Sudan zai kara zurfin matsalar da ake fama da ita, kuma baranza ce ga fatan da ake da shi na kawo karshen rikicin.