Kungiyar Amnesty International Ta Zargi Isra’ila Da “Kisan Kare Dangi” A Gaza

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta zargi Isra’ila da “yin kisan kiyashi” kan Falasdinawa a

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta fitar da wani rahoto wanda a cikinsa ta zargi Isra’ila da “yin kisan kiyashi” kan Falasdinawa a zirin Gaza.

Wata bayan wata, Isra’ila ta dauki Falasdinawa a Gaza a matsayin rukuni na wadanda ba su cancanci a mutunta ‘yancinsu da mutuncinsu ba, in ji Sakatare Janar ta kungiyar, Agnès.

Rahoton mai shafuka 300, ya fitar da sakamakon binciken na tsawon watanni 10 da akayi a Gaza da kuma nazarin jawaban jami’an Isra’ila.

Kungiyar ta Amnesty ta ce ta dogara ne kan sharudda da Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan kisan kare dangi ta shata.

A cikin rahoton, Amnesty International ta yi nuni da “hare-haren da gangan kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa, yin amfani da makamai masu fashewa a wuraren da jama’a ke da yawa”, da kuma cikas ga isar da agajin jin kai a cikin yankin da kuma tilastawa kashi 90 cikin dari na jama’ar yankin gudun hijira.

Tun bayan fara yakin ramuwar gayya da Isra’ila ta kaddamar, mutane 44,532 ne sukayi shahada a Gaza, wadanda yawancinsu fararen hula ne, a cewar bayanai daga ma’aikatar lafiya ta Hamas a Gaza, wadanda kuma Majalisar Dinkin Duniya ke cewa abin dogaro ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments