Kudaden da sojojin Afirka suka kashe a bara ya karu da dala biliyan 52 a shekarar 2024

Adadin kudaden harkar soji a nahiyar Afirka a bara, musamman a Aljeriya da kasashen kawancen Sahel, ya karu. A cewar wani bincike da Cibiyar Nazarin

Adadin kudaden harkar soji a nahiyar Afirka a bara, musamman a Aljeriya da kasashen kawancen Sahel, ya karu.

A cewar wani bincike da Cibiyar Nazarin Zaman Lafiya ta Duniya ta Stockholm (SIPRI) ta gudanar, kashe kudaden soji a Afirka ya karu zuwa dala biliyan 52.1 a shekarar 2024 a fadin Nahiyar, wanda ya karu da kashi 3 bisa 100 a shekarar 2023 da kuma karuwar kashi 22 cikin 100 a shekarar 2015.

A cewar rahoton na SIPRI, kudaden da ake kashe wa sojojin na Arewacin Afirka ya kai dala biliyan 30.2 a shekarar 2024, ya kuma karu da kashi 4 cikin 100 a shekarar 2024.

Kudaden da Aljeriya da Maroko kadai suka kashe ya kai kashi 90% na adadin kudaden da yankin ya kashe.

A Kasashen kudu da hamadar sahara, Adadin kudin da ake kashewa na soji ya ragu da dalar Amurka biliyan 21.9 a shekarar 2024, dan kadan ya ragu da kashi 3.2 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar 2023 da kashi 13 cikin 100 idan aka kwatanta da 2015.

Kasar Afrika ta Kudu, wadda ta fi kowacce kasa kashe kudi a fannin soji a wannan yanki, an rage kasafin kudin sojojinta na shekara ta hudu a jere, zuwa dala biliyan 2.8 a shekarar 2024, raguwar kashi 6.3 cikin 100 daga shekarar 2023 da kuma raguwar kashi 25 cikin 100 daga shekarar 2015.

Bayanin ya ci gaba da cewa kudaden soji da kawancen kasashen yankin Sahel na AES sukayi wato Mali da Burkina Faso da Nijar sun kashe dala biliyan 2.4 don harkar soji a shekara ta 2024.  

Wadannan kasashe sun yanke hadin gwiwa da Faransa a fannin tsaro.

Burkina Faso ta kara yawan kudaden da take kashewa a wannan fanni da kashi 108 cikin 100 tsakanin shekarar 2021 zuwa 2024, yayin da Nijar ta karu da kashi 56 cikin 100 tsakanin shekarar 2022 zuwa 2024. Haka abin yake ga Chadi, wadda ta kawo karshen hadin gwiwarta da Faransa a cikin 2024.    

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments