Hamas Ta Ce An Fara Tattaunawa Tare Da HKI Kan Tsakana Wuta A Doha A Yau Asabar

Wani babban jami’in kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza ya bada sanarwan cewa an fara tattaunawa da HKI ta kawo karshen wannan yakin a birnin doha ba tare da shimfida wasu sharudda ba. Shafin yanar gizo na labarai Arabnews ya nakalto Taher Annunu daga daga cikin manya-manyan jami’an kungiyar ta Hamas yana fadar haka. […]

Adadin shahidai a yakin Gaza ya kai 53,119 tun daga Oktoba 2023

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza ya kai 53,119 tun daga ranar 7 ga Oktoba, 2023. Adadin ya karu ne sakamakon wasu hare-haren Isra’ila na baya baya nan wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa 93 wayewar […]

Isra’ila ta yi barazanar kashe al-Houthi na Yemen saboda goyan Falasdinu

Gwamnatin Isra’ila ta yi barazanar kashe jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Abdul-Malik al-Houthi, idan har Sana’a ta ci gaba da kai hare-hare da makami mai linzami kan Isra’ilar don goyon bayan Falasdinu. Ministan harkokin soji na gwamnatin, Isra’ila Katz ya ce idan har Yemen ta ci gaba da ayyukanta “za su sha azaba mai […]

Iran ta ce babu wata rubutaciyar shawara da ta samu daga Amurka

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa babu wata rubutaciyar shawara data samu daga Amurka. Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya musanta ikirarin samun rubutaccen sako daga Amurka kan yarjejeniyar nukiliya. “Iran ba ta sami wata rubutacciyar shawara daga Amurka ba, kai tsaye ko a kaikaice,” in ji Araghchi a cikin wani sakon da […]