Kididdgar da hukuma mai kula da shiga da ficen kaya ta Iran ta bayyana cewa, kudaden da kasar ta samu a watanni hudu na farkon shekarar Iraniyawa, ( Daga 20 ga watan Maris zuwa yanzu) sun kai dalar Amurka biliyan 11 da miliyan 655.
Kamfanin dillancin labarun Mehr na Iran ya ambato hukumar shiga da ficen kayayya ta kasa tana cewa; nauyin kayan da aka fitar da su, sun kai ton miliyan 34 da dubu dari 347 akan kudi dala biliyan 11 da miliyan 655.
Dangane da kayan da aka shigo da su kuwa daga waje, kididdigar ta ce, sun kai ton miliyan 9 da dubu 13, da kudin da su ka kai dalar Amurka miliyan 13 da miliyan 29. Rhoton ya kuma bayyana kasar China a mastayin farko mai sayen haja daga Iran da kudinsu sun haura dala biliyan 3 da miliyan 511, sai kuma kasar Iraki da take binta da sayen haja ta biliyan 1 da miliyan 9.5. Kasa ta uku kuwa wajen sayen hajar Iran ita ce, Hadaddiyar Daular Larabwa da kimarsu ta kai kimar biliyan 1 da miliyan 592. Kasa ta hudu kuwa ita ce Turkiya wacce ta sayi haja daga Iran da kudin da sun kai dala miliyan 937,, sai kuma Afghanistan da kudin da sun kai dala miliyan 510.