rahotanni sun nuna cewa Asusun ajiyar kudaden waje na Nijeriya ya kai dala biliyan 54, matakin da bai taba kai wa ba cikin kusan shekaru 18, lamarin da ke nuna karuwa a yawan kudaden waje da kasar take da su.
Wannan karin kudin ajiyar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauye a kasuwar canjin kudi da kuma kokarin gwamnati na kara yawan kudaden waje.
Masana tattalin arziƙi na kallon karin ajiyar kudaden waje a matsayin wata dama da za ta iya karfafa karfin tattalin arzikin Nijeriya wajen biyan bukatun kudaden waje, da tallafa wa kasuwanci da kuma rage matsin lamba kan Naira.
Duk da haka, karin kudin ajiyar ba shi kadai yake tabbatar da ingancin karfin tattalin arziki ba. Muhimmin abu shi ne yadda gwamnati za ta iya amfani da wannan karfin ajiyar wajen samar da kayayyaki, da fitar da kaya zuwa kasashen waje da kuma tabbatar da dorewar ci gaba da samun kudaden waje.