Shugabar kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta soki Amurka kan yi wa kotun katsalandan a binciken da take yi tare da yin barazana ga alkalan ta.
Shugabar kotun, Tomoko Akane ta shaidawa wakilan kasashe mambobin kotun 124 a birnin Hague cewa kotun na fuskantar “matakan tilastawa, barazana, matsin lamba, da ayyukan zagon kasa”.
Akan ta yi tsokaci ne kan kalaman dan majalisar dattawan Amurka Lindsey Graham, wanda ya kira kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa a matsayin “abin dariya mai hadari” tare da yin kira ga majalisar dokokin Amurka da ta sanya wa mai shigar da kararta takunkumi.
A baya Graham ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa: “Ina gaya wa kawayen Amurka Canada, Ingila, Jamus, da Faransa cewa idan suka taimakawa kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Amurka ma za ta saka musu takunkumi.”
A baya-bayan nan ne dai kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta bayar da sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan yakin gwamnatin kasar Yoav Gallant kan aikata laifukan yaki a Gaza.
Kasashen duniya da dama sun yi marhabin da hukuncin kotun ta ICC, kuma dayewa sun sanar da cewa za su aiwatar da hukuncin tare da kama Netanyahu da Gallant da zarar sun sanya kafa a kasashensu..