Kotun Afirka ta Kudu ta samu madugun adawa da laifin harba  bindiga a bainar jama’a a 2018

A wannan Laraba ce wata kotu a Afirka ta Kudu ta samu madugun ‘yan adawa Julius Malema da laifin harba bindiga a bainar jama’a a

A wannan Laraba ce wata kotu a Afirka ta Kudu ta samu madugun ‘yan adawa Julius Malema da laifin harba bindiga a bainar jama’a a shekarar 2018, hukuncin da zai iya sa a hana shi shiga majalisar.

Malema ya harba bindiga sama a lokacin bikin cikar shkaru biyar da kafa jam’iyyar Economic Freedom Fighters (EFF)  a lardin Eastern Cape, wanda ya saba wa dokar hana sarrafa bindigogi. Idan har aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari, Malema, wanda ya shafe sama da shekaru 10 yana dan majalisa, za a dakatar da shi  daga ci gaba da zama mamba a majalisar dokoki a karkashin kundin tsarin mulkin kasa.

A rahoton kamfanin dillancin labaran Reuters Mai shari’a Twant Olivier ta ce, kwanaki uku bayan yanke hukuncin, “Malema ya aikata laifin mallakar makami ba bisa ka’ida ba, da mallakar harsashi ba bisa ka’ida ba, harba  bindiga a wani wuri na zama ko taruwar jama’a, da kuma jefa mutane ko kaddarorinsu a cikin hadari. Yayin da aka wanke mai tsaron lafiyarsa, Adrian Snyman, wanda ake zargi da mika masa makamin.

Alkaliyar kotun ta ce za a bayar da rahoton yanke hukunci a ranar 23 ga watan Janairu.

A nasu bangaren, jam’iyyar Malema ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa wannan ya tabbatar da cewa wannan wata farfaganda ce ta yunkurin dakile da kuma karya shugaban EFF ko ta wane hali, domin yin tasiri a cikin harkokinsa na siyasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted