Koriya ta Kudu : Majalisa ta tsige shugaba Yoon Suk-yeol

Majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta zartar da kudurin tsige shugaban kasar Yoon Suk-yeol saboda gazawar da ya yi na kafa dokar soji a ranar

Majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta zartar da kudurin tsige shugaban kasar Yoon Suk-yeol saboda gazawar da ya yi na kafa dokar soji a ranar 3 ga watan Disamba.

‘Yan majalisa 204 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin yayin da 85 suka ki amincewa a sakamakon da shugaban majalisar ya sanar yau Asabar.

Kafin nan dai dubun dubatar masu zanga-zangar ne suka taru a wajen majalisar dokokin kasar suna jiran kada kuri’a.

Kusan kashi 80% na mutanen Koriya ta Kudu sun yi kira da a tsige shugaba Yoon daga mukaminsa bayan yunkurin ayyana dokar soji a ranar 3 ga watan Disamba.

Yanzu dai an dakatar da Yoon Suk-yeol, har zuwa lokacin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin amincewa ko akasin korar tasa.

Kotun na da nan zuwa kwanaki 180 na bayyana ra’ayinta..

Yanzu dai Firaminista Han Duck-soo ne zai yi rikon kwarya..

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments