Kissoshin Rayuwa Zahra (s) 61

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahad Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai  cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimatuz Zahra(s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a), shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, mun tsaya inda muka bayyana yadda Ummu Salma Ummul muminina ( Ra) matar manzon All..(s) ta maida martani wa Khalifa na farko a kan wasu kalamai wadanda basu da ce ba ga shugaban matan Aljanna, Fatimah (s), wadanda suke nuna rashin tsarkinta. Ta bayyana cewa a cikin tsarki ta tashi, a cikin tsarki ta girma sannan itace shugaban matan aljanna. Sannan ta goyi bayanta kan cewa annabawa ana gadonsu, don da ba’a gadonsu da kuwa manzon All..(s) zai fada mata, don wajibi ne ya fada mata, saboda kada ta nemi gadonta a bayansa.

Amma tunda bai fada mata ba, to haka hukuncin gado tsakanin annabawa da yayansu daya da na sauran mutane a cikin al-ummunsu. Daga karshe ta bukace su da su ji tsoron All..su kuma tabbatar da cewa manzon All..(s) yana ganinsu, kuma ba za su ji dadin haduwa da shi a ranar kiyama ba.

Sannan munyi maganar yadda mutanen Ansar da farko, sannan matan Ansar da muhajirun suka je wajen Zahra (s), inda suka bata hakuri kan abinda ya faru bayan wafatin manzon All..(s), musamman dangane da kauracewa iyalan gidan manzon All..(s) da suka yi, sannan suka kara da cewa, da Baban Hassan Aliyu dan Abitalib(a) ya fada masu yadda al-amarin yake tun farko, da basu zabi waninsa ba.

Amma Zahra (s) ta kare Baban Hassan Imam Ali (a),  tunda a sanda wadannan mutane suka yi abinda suka yi, shi baban Hassan (a) baya cikin yanayin da zai zo, ya yi jayayya da su kan khalifancin manzon All..(s) da su ba.  Tunda shi ne yake kula da jana’izar manzon All..(s).

Banda haka, umurnin manzon All..(s) ne gare shi, kan kada ya rabu da shi bayan wafatinsa sai ya sanya shi a kabarinsa.

A cikin shirimmu na yau zamu dora daga inda muka tsaya, a cikin shirimmu da ya gabata, inda Zahra (s) take wa Matan Ansa da Muhajirun Magana, a lokacinda suka je wajenta don neman uzuri ga mazajensu wadanda suka ki amsa kiranta (s), na taimakawa Iyalan gidan manzon All..(s).

A ci gaba da Khudubarta ga matan sahabbai, Zahra (s) ta bayyana matsayin iyalan gidan manzon All..(s), da kuma yadda All..ya zabe su, don jagorancin al-ummar babanta. Ta bayyana matsayin Amirul muminina (s), da yawan ilminsa da kuma tsaron All.., har’ila yau da kuma musibun da zasu sami wannan al-ummar na rashin gabatar da shi a matsayin Khalifan manzon All…(s).

Ta bayyana yadda addanin musulinci, bayan ya kasance addinin zaman lafiya da aminci, zai juya ya zama, addin mai jawowa masulmi da wadanda ba musulmi ba bala’i, da musibu, saboda yadda sarakuna zasu sauya shi, su shigar da ra’ayinsu. Sannan za’a sami azzaluman shuwagabanni wadanda za su aikata zalunci mai yawa da sunan addini.

Har’ila yau ta ce wadanda za su zo nan gaba, a cikin wannan al-ummar zasu dandani azaba da wahalhalu saboda abinda magabatansu suka aikata. Azaba da zubar da jini da zalunci za su zama jiki a cikinta al-ummar musulmi.

Abinda ya faru a zamanin Khalifa na uku, Uthman dan Affan kekyawar misali ce. Malaman tarihi sun bayyana cewa,  Khalifa Uthman ya yi wasu ayyuka wadanda suka sabawa Alkur’ani mai girma da kuma sunnar manzon All..(s) mutane suka yi masa tawaye, bayan ya yi amfani da karfi a kansu, ya kori wasu daga Madina Kamar Abuzar Alghifari, ya sa aka yiwa wasu duka, kamar Abdullahi dan Mas’ud da kuma Ammar dan Yasir. A lokacinda musulmi suka kosa da shi, sai suka kashe shi. Da haka kuma zaman lafiya da amince suka kare a cikin musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Haka ma Talha da Zubai sun yi tawaye wa Imam Aliyu dan Abitalib (s) a lokacinda ya karbi ragamar shugabancin Al-ummar Musulmi, bayan barna na tsawon kimanin shekaru25, wadanda shuwagabnnin da suka gabace shi suka aikata. Sun haddasa masa manya manyan yake yake a Basra ko Jamal. Sun ingiza mutane suka kashe Uthman dan Affan sannan suka je Basra suna neman Jininsa. An kashe Uthman a Madina, sannan suka je Basra suna neman jininsa. An kashe akalla mutane dubu 15 a cikin musulmi a wannan yakin.

Sannan bayan haka Mu’awiya dan Abisufyan tare da taimakon Amru dan Asi suka tada fitina da sunan neman jinin Uthman, suka kuma jagoranci yakin Siffin tsakaninsu da Imam Ali (a) a nan ma, aka kashe akalla mutane dubu 90 a cikin musulmi.

Sai yakin Nehrawan, inda Imam Ali (a) ya yaki Khawarijawa, ya kuma kashe mutane akalla 4000. Kafin su kashe shi ko ya yi shahada a karshin rayuwarsa a hannunsu.

Sannan a lokacinda Mu’awiya dan Abisufyan ya sami iko a kan mutanen sham, ya aiki Busru dan Artah zuwa Madina da Makka da Yemen inda ya yi ta kashe mutane musulmi a kan hanyasa, da kuma cikin wadannan yankuna. Mafi yawansu shi’ar Aliyu dan abitalib (a) ne. A cikin wannan zubar da Jinin ne, Busru ya kashe mutane musulmi kimani dubu 146.

Wannan adadin wadanda aka kashe ne kawai, banda wadanda suka ji Rauni ko kuma matan da aka kashe wadanda suka rasa mazajensu. Wato zawarawa da kuma marayun da Busru ya haddasa a wadannan yankuna.

Wadannan kashe-kashen sun farune daga kissan Uthman da kuma shahadar Imam Ali (a) wato shekaru kimani 4 kacal.

Amma kisan ta kare? Ba haka ba, yanzu ne ma aka fara. Don Fatima (s) a lokacinda take fadawa matan Ansar da kuma Muhajirun, wadanda suka ziyarce ta, tana ganin hakikanin abinda zai faru, don haka, ta san haka zai faru kuma shi yasa tace, ‘wadanda za su zo baya zasu dandana wahalar abinda magabatansu suka aikata’.

Duk wanda ya karanta tarihi zai fahinci hakan, musamman a zamanin sarakunan Bani Umayya, ko Abasiyawa, wadanda ba ruwansu da jin dadin musulmi. Abinda ya damesu shi ne kujerar sarautarsu. Babu ruwansu da musulmi ya kwana da yunwa, ko ya sami abinci. Sun yi sanadiyyar mutuwar mutane musulmi, don kare kujerarsu ko don biyan bukatun wadanda suke tare da su ne kawa.

Daga cikin ayyukan zubar da jinin musulmi ba tare da wani dalili ba wanda wadannan sarakuna suka yau, akwai ‘Waki’ar Hurra’ inda Yazid dan Mu’awiya ya aiki Muslimu dan Ukba da sojoji, suka kara da mutanen Madina wadanda suka yiwa Sarki Yazid Tawaye, bayan ya kashe Imam Hussain (a) a Karbala. Muslimu ya fito zuwa Madina da mayaka dubu 30, Kafin ya fita zuwa Madina Yazid dan Mu’awiya (L) ya fada masa cewa, idan ya sami nasara a kan mutanen Madina, ya halattawa sojojinsa garin na tsawon kwanaki uku, su yi abinda suka ga dama.  kama daga dabbobinsu, dukiyoyinsu  da makamai da sauransu.

Mutanen Madina sun hadu da rundunar Muslimu a wani wari da ake kira Hurra a wajen Madina shi yasa ake kiran yakin da sunan ‘yakin Hurrah’.

An kashe daruruwan mutanen Madina, wadanda suka kasance yaya da jikokin sahabban manzon All..(s) ne a lokacin, muhajirun da Ansar. Sannan sauran kuma suka tarwatse suka gudu suka koma madian   

Sojojin Sham sun kashe mutanen Madina, har sai da wasunsu suka fake da kabarin manzon All..(s), amma basu tsira ba, har sai da jininsu ya cika wurin kabarin da jininsu. Duk tare da girman da kabarin musulmi yakeda shi a wajen musulmi.

Daga nan sai mai shelan Muslimu dan Ukbah ya shelanta cewa ya halattawa sojojinsa Madinan manzon All..(s) su yi abinda suka ga dama na kwanaki uku. A nan sojojin sham suka fara kwasar dukiyoyi da fayen mata da kissan wanda suka ga dama.

Malaman tarihi sun bayyana cewa a shekarar,  sai da mata badare, kimani 300, wadanda basu taba aureba, suka dauki cikin shegu, kuma suka haifi yara kimani dubu guda wadanda ba’a san iyayensu maza ba.

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, wasu daga cikin sojojin sun yiwa mata Fyade har a cikin masallacin manzon All..(s).

Sun ce daya daga cikin sojojin Sham ya shiga gidan Abu ayyubal Ansari(a) daya daga cikin fitatun sahabban manzon All..(s), wanda ya tsufa sosai a lokacin, har ya makance, ya kutsa a cikin gidansa don daukar ganimar abinda ya samu a gidan.

Sai ya  samishi yana zaune a kasa, sai ya gudanar da bincike a gidansa, da kuma mutanen gidan, bai sami kome ba. Saboda wasu sojojin sun rikashi zuwa.

A nan sai wannan sojan ya zu wajen Abu-ayyukan Ansari ® ya fara jan kashin gemunsa da hannunsa, yana fisgewa daya bayan daya, da karfi, sai dattijin ya na cewa masa, nine Abuayyubal Ansari sahabin manzon All..(s), amma wannan mutumin sham bai damu da abinda yake fada ba.

Yayi abinda ya ga dama a gidan. Sannan ya ga tattabaru a cikin gidan, sai ya kakkashesu ya jefa a cikin rijiya.

A wani wajen wani sojan sham ya shiga wajen wata mata a cikin, madina ya sameta zaune a kasa tana sahayar da jiririnta nono sai ya kama kafafuwan yaron ya fisgeshi daga hannu mahaifiyarsa sai ya jefa shi a jikin bongo, mahaifiyar tana ganin yaron nan ya zubar da jinni har ya mutu.

Sannan bayan kwanaki uku Muslimu dan Ukba ya tara sojojinsa da kuma mutanen madina inda ya tilasta masu bai’a a gareshi a matsayin bayin Yazid dan Mua’wiya, sannan suka fita daga Madinan manzon All..(s). Ya bar mutanen Madina suna kuka, don sojojinsa sun kwace duk abinda suke da shi, sannan sun barsu da gawakin daruruwan mutanen da dubban marayu da zawarawa. Innalillahi wa inna ilaihi Ra’ji’un.

Duk abinda Zahra (s) ta fadawa matan madina a lokacin da al-ummar ta yi watsi da iyalan gidan manzon All..(s) sun tabbata a fili.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

======================================.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments