Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 159

159-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka

159-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da a mu a cikin shirimmu na yau.

////…Madalla. Masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata. Mun kawo maku wasikar da Imam Al-Hassan(a) ya rubutawa Mu’awiya dan Abu Sufyan wanda yayi tawaye wa mahaifinsa imam Ali(a) bayan an masa ba’a a madina da sunan neman jinin Khalifa uthman. Don haka Imam Alhassan ya gaji mahaifi a wannan jayayyar, ya bukaci Mu’awiya ya dawo ya mika kai ya hada kan musulmi.

Kafin haka Imam Al-hassan ya tunatar da shi abubuwan da suka faru bayan wafatin manzon Allah (s) ta yadda musulmi larabawa suka fara jayayya a tsakaninsu kan wanda zai karbi shugabancin Muhammad (s) a bayansa. Bayan jayayya mai yawa sai mutanen ansar suka barwa muhajirun wadanda kuma kuraishawa ne. suka yi bai’a wa Khalifa na farko.

Ya kuma tabbatar da cewa kuraishawa sun zalunci ahlulbaiti a lokacinda suka ki mayar masu da hakkinsu bayan sun bukaci hakan. 

Sannan munji yadda kafin Imam Al-Hassan (a) mahaifinsa Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) ya kawo wannan batun a cikin wasikar da ya rubutawa mutanen kasar Masar bayan ya karbi khalifanci inda, yad aga bayyana wannan al-amarin, kan cewa kuraishawa sun kwace hakkinsa, na shugabanci, duk da cewa kafin wafatin manzon All..(s) bai tsamman zasu yi haka. Amma da suka yi kuma shi yaki ya bisu, amma da ya ga cewa abinda suka yi yasa larabawa suka ridda su fice daga addinin musulunci, suna ma kira ga rusa addinin Mohammad (s), sai ya ga cewa dolene ya taimakawa musulunci da musulmi don kada musibun su yi masa yawa, idan musulunci ya rushe ko ya sami tawaya.

A cikin shirimmu nay au zamu fara kawo maku wasikar Mu’awiya dan Abu Sufyan bayan ya karbi ta Imam Alhassan ya kuma karantata. Inda yake cewa

(Bayan haka. Hakiki na fahinda abinda ka fada dangane da manzon Allah (s) shi ne ya fi cancanta falala gaba daya daga na farko zuwa na karshe, sannan ka ambaci jayayyar musulmi kan shugabanci a bayansa, ka kuma bayyana tuhumarka ga Abubakar Assidiku da Umar, da kuma Abu Ubaida dan Jarrah amintacce, da salihan bayi cikin wadanda suka yi hijira, ban ji dan kayi haka ba. Don lalle a lokacinda al-umma ta yi jayayya kan shugabanci a tsakaninta, ta ga cewa kuraishawa ne suka fi cancanta da lamarin, sai kuraishawa da Ansar da masu falala a cikin addini daga cikin musulmi suka ga cewa zasu shugabantar da wanda ya fisu ilmi a cikinsu, kuma basu yi kuskure ba, don da sun san wani mutum wanda ba Abubakar ba, wanda zai kare hurumin addinin musulunci, da basu barshi suka zabi Abubakar ba.

Sannan a yau indan mun dawo Tsakani na da kai, al-amarin yana nan kamar yadda suka kasance, da na san cewa kai ne mafi sanin al-amuran shugabanci, kuma ka fi dacewa da shugabancin wannan al-ummar, kuma ka fi kyautata shugabanci, ka fi iya kaidi wa makiya, ka fi iya tara haraji, da na mika maka shugabanci bayan mahaifinka. Sannan mahaifinka ya yi makirci wa Uthman har aka kashe shi yana matsayin wanda aka zalunta, sai Allah ya nemeshi da jininsa, wanda Allah ya neme shi da wani abu ba zai kubuce masa ba, sannan ya kwacewa al-umma al-amarin shugabancinta, ya rarraba hadin kanta, sai wadanda suke dai-dai da shi a matsayi a cikin wadanda suke da sabika a shiga musulunci, da yin jihadi, da kuma dadewa a cikin musulunci, suka saba masa, yayi iddi’a’ii kan cewa sun kwance bai’arsa, ya yakesu ya kuma zubar da jinni, ya kuma halatta huruminsu, sannan ya zo mana yana iddi’a ‘iin bai’arsa a kammu, amma yana son ya mulke mu ne a dole, mun yakeshi ya yake mu.         )

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments