227-Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhakabarkammu dasake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa, shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafai, da fatan masu sauraro zasukasance tare da mu.
////…. Madalla, Idan masu sauraro suna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo mako sirar Imam Alhassan Al-Mujataba (a) dayan Fatimah (s) diyar manzon Alla..(s), inda muka tsaya akan yansa Mu’awiya dan Abusufyan ya kashe wasu shiar amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).
Ya daure wasu ya sa wasu suka kauracewa daular musulunci gaba daya, suka koma cikinn ajamawa, wasu kuma ya azabtar da su ko ya tsorata su. Daga cikin wadanda ya tsorata akwai Ibn Mohammad ibn Abi Khuzaifa,Abdullahi dan Hashimul Mirkaal, wand muka ce babansa Hashimul Mirkaal kwamandan sojojin Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) a Yakin siffin ne, kuma yayi shahada a yakin.
Amma kafin haka ya yaki mutanen sham har sai da Mu’awiya ya tabbatar da cewa Aliyu (a) ya sami nasara a kansa. Ya kuma fara shirin gudu daga yakin, sai Amru dan Asi ya zo masa da wani kaida na daga Mushafi saboda raba kan sojojin Imam Ali(a) ya kuma samu. Da Haka Mu’awiya ya tsira a yakin Siffin.
Amma dan Hashimul Mirkal, Mu’awiya ya rubutawa Dan Sumayya ma’aikacinsa a Kufa ya je ya kamoshi a cikin gidan wata mata Almakhzumiyya a unguwarsu a Kufa ya kuma aikashi zuwa Sham a cikin mummunan Hali, mukace ya Isa Sham a ranar Jumma’a. ranar da Mu’awiya yake ganawa da manya-manyan Quraishawa da na kasar Iraki.
Da ya ganshi ya ya juya wajen Dan Asi yace ka san wannan matashin , dan Asi yace ban ganeshi ba, ya ceshi ne, wanda babbansa yake fada a siffin, sai ya jawo baitocin Hashimul Mirkal, a nan ne sai Amr ya gane shi sannan yayi ta jayayya da Abdullahi ya bukaci Mu’awiya ya kasashe saboda shi.
Daga karshe mu’awiya ya yanke jayayya a tsakaninsu sai yayi Afwa ga Abdullahi dan Hashimul Mirkal wanda ya koma Kufa daga bayan.
Amma awasu ruwayoyi bai yi masa Afwa ba sai dai ya jefa shi a kurkuku na wani lokaci.
Abdullahi dan Hashim Alo-Mirkal bai yi wani laifi ba, sai sonsa ga Amirul Muminina Aliyu dan Abitalib (a). Bai yi wani laifiba sai don yana son iyalan gidan manzon All..(s). dan Abusufyan baya son ganin masoyansa suna zaune lafiya.
03-Abdullah dan Khalifah Aiyada yace a kama shi, yansanda sa suka kamashi amma yan kabilarsa suka kubutar da shi a lokacinda labara ya zo masa sai ya kira Adi dan Hatam Attaei wanda ya zo amma ya ki amincewa ya mikawa ziyada Abdullahi, shi ma ya jefa shi a kurkuku, sannan daga bayamutanen yemen da Rabii suka bayyana masa hatsarin kama Adiy, sai ya sake shi, sannan y ace masa kada ya sake ganin Abdullahi a cikin Kufa. Adiy ya amince ya tura Abdullahi dan Khalifa zuwa yankin Jabalai. Inda ya aiwatar dasauran rayuwarsa. Ya mutu a Jabalain na kabilar Tay kafin halakar ziyad.
04-Sasa’atu dan Saukhan, yana daga cikin shuwagabannin Larabawa, yana daga cikin masu fasahar magana da kuma balagha, ya musulunci a zamanin manzon All..(s), amma bai sami ganinsa ba, saboda karancin shekarunsa.
Amma ya zo madina a cikin khalifancin Umar, sai ya sameshi yana raba kudade ga musulmi, wadanda yawansu ya kai dirhami miliyon guda. Ya raba masu sai wani abu ya rage, sai suka yi sabani kan yanda za’a raba sauran. Sai Khalifa ya hau kan minbari, ya yi khuduba a cikinta yana cewa,: Ya ko mutane hakika wasu kudade sun rage bayan kun karbi hakkokinku, ya zaku fada?
A nan sai Sasa’ah dan Sauhan ya tashi ya tsaya ya mayar masa magana, yana inkarin zabin da ya bawa sahabbai kan abinda za’a yi da saurab. Yana cewa: ‘Ya shugaban mumunai, ai zaka yi shawara da mutane ne a inda ba’a sauko da ayar al-kur’ani kansa ba. Amma a cikin al-amarinda All..ya saukar da Alkur’ani kansa, ya sa shi a wurin da ya sashi, ka sa shi inda All..Ta’ala ya sa shi. Sai Umar ya kyautata ra’ayinsa, yace: Ka yi gaskiya, kai nine ni kai ne: sai sauka ya kuma rabawa musulmi sauran kudaden.
Sannan a lokacinda Amirul muminina ya karbi khalifancin musulmi, ya luzumce shi,, ya kuma zama cikin zababbun makusantansa, wadanda suka fahinci matsayinsa na gaskiya, wato shi’arsa.
Imam Sadik (a) yana fada dangane da shi {Ba wanda ya san hakkin Amirul muminina(a) sai Sasa’atuh da wadanda suke tare da shi}. Sasa’atu yayi rashin lafiya, Amirul muminina (a) ya ziyarce shi(s), sai ya ce masa: {Ya sa’asaah!, kada ka dauki ziyarata gareka, wata daukaka ce gareka kan mutanenka, } Sai yace: Haka ne, sai dai ina daukarta a matsayin ni’imar Allah ce da falalarsa gareni”.
Sai Imam yace: {Lallei idan ka kasance kamar yanda na sanka, kai ba mai dorawa wani nauyinka ne, kuma mai taimakawa mutanene} .Sai Sa’asa’ah ya ce: ‘Kuma kai ya Amirul Mumina masanin All.. kuma mai tausayi da rahamane ga muminai’.
Sannan saboda kyawun ra’ayinsa da hankalinsa, Imam Ali (a) yakan aike shi zuwa zuwa wasu waurare masu muhimmanci, kamar yanda ya taba aikarsa zuwa wajen Mu’awiya dan Abusufyan tare da wata wasika. A lokacinda ya isa wajen Mu’awiya, sai fada, don daukaka kansa da kuma yabonsa kansa ‘Kasa ta All..ce, ni kuma khalifansa ne, duk abinda na dauka daga cikin dukiyar All..nawa ne, abinda na bari kuma ya halatta a gareni..’
Sai Sa’asa’ah bai ji dadin kalaman Mu’awiya ba sai ya tashi ya karanta wata kisida wacce take cewa: Gurin ranka ba zai cika ba, saboda jahilcinka ya Mu’awiya! Kada ka yi sabo!
Sai mu’awiya bai ji dadi ba. Sai yace masa. Kai ma ka’iya magana? Sai Sa’asa’ah ya mayar masa yana cewa: Ana samun ilmi ne da karatu, wanda bai sani ba jahili ne. Lalle kana bukatar in saka maka da sakamakon aikinka.
Sai sa’asa;ah yace: Wannan baya hannunka, yana hannun wanda baya jinkirtawa rai idan ajalinta ya zo. Sai Ma’awiya yace: Wa ya isa ya shiga tsakanina da kai?. sai yace: Wanda yake shiga tsakanin mutum da zuciyarsa. Mu’awiya: Ka yelwata cikinka don magana, kama yanda cikin rakumi yake da yelwa don daukar alkama. Sai Sa’asa’ah yace: Cikin wanda baya koshi yana da yelwa, kuma wanda baya tarawa ya yi addu’a a kansa.
Wannan ya nuna cewa, Sa’asa’ah mutum ne mai fasaha, saboda yana maidawa mu’awiya magana dai dai kalaman da yayi amfani da su. Sannan wannan muhawarar ya nuna cewa baya jin tsoron sarakuna.
Mu’awiya yayi khuduba, bayan da al-amarin shugabanci ya koma hannunsa, sai Sa’asa’a ya tashi yayi ta’aliki kan dukkan kalma ko jumlolin da ya fada a khudubarsa..
A cikin shirimmu na gaba da yardar All..zamu kawo maku da ta’alikin da yayiwa khudubar Mu’awiya.