224-Asalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwashiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.
////….Madala, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan dan Fatima (s) diyar man manzon Allah(s) da muke kawo maku, mun tsaya inda muke ci gaba da kawo maku sahabban manzon All…(s) da kuma wasu fitattun mutanen masoyan Amirul muminina Aliyu dan Abutalib (a), wadanda Mu’awiya dan Abusufyan ya kashesu saboda sun ki zagin sa (a). na gaba gaba da su su ne Hijru da mutanen hijru 6. da kuma wasu wadanda ba su ba.
Mun ambaci Rashidul Hijri, da Amru dan Al-Hamkul Khuzaa’i. Wanda ya taba shayar da manzon All..(s) Madara, sannan yayi masa addu’a inda a cikinta ya roki All..ya jiyar da shi dadin da kurcciyarsa. Sai All..Ya karbi addu’ar, wanda Amru dan Al-Hamkul Khuzaa’i. ya kai shekaru kusan 80 babu farin gashi ko alamun tsufa a wajensa da suka fito a wajensa.
Sannan bayan wafatin manzon All..(s) ya kasance cikin zababbun sahabban Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a). Ya kasance cikin sahabbansa mafi kusa da shi. Imam Ali (a) yayi masa addu’a ya ce: {Ya Ubangiji ! Ka haskaka zuciyarsa da tsoron ka, da shiriya zuwa tafarki madaidaiciya} . Imam Ali (a) yana girmama shi, yana daukaka shi, yana gabatar da shi kan wasu da dama. Hakika wata rana ya fada masa cewa: {Ina ma a ce ina da irin 100 a cikin sojojina!} . Sannan wata rana ya fadawa Imam Ali (a) yana bayyana amincea da shugabancinsa da kuma sonsa gareshi yana cewa ‘Na rantse da All..Ya Amiral muminina, ban soka don duniya ba, ko don samun matsayi cikinta ba, Lalle ina sonka ne saboda abubuwa 5, kai ne wanda ya fara Imani cikin musulmi, dan ammin manzon All..(s), mafi daukaka cikin muhajirun da Ansar, mijin shugaban mata (a) baban zurriyarsa da ta rage. Da na hau manya manyan duwatsu, da kuma na kutsa cikin manya manyan tekuna da duk wannan kadan ne, saboda yawan hakkinka a kai na’.
A cikin maganarsa ya bayyana mika kai ga shugabancin Amirulmuminina (a). da imaninsa da kuma neman yardar All.. da dukkan wannan da kuma gidan Lahira.
A lokacinda Mu’awiya ya karbi shugabanci, ya kuma dora Ziyad dan Sumayya a kan mutanen Kufa ya kuma fara binsu daya bayan daya yan kashewa, sai Khuzaei ya ji tsoron zamansa a Kufa, don haka ya gudu ya tafi garin Mada’in. Ya kuma fita tare da Rafa’ah dan Shaddad. Sun dan dade a Mada’in sannan suka gudu zuwa garin Musil na kasar Siriya, kafin su shiga Musil, sun shiga wani kogo kusa da garin don su huta, amma sai wasu mutane a yankin suka lura da samuwarsu a cikin wani kogo a a wani dotsen da yake kusa da garin na Musil.
Daga nan sai labari ya kaiwa ma’aikacin Mu’awiya a Musil Bal’atu dan Abu abdullahi, sai ya taho masu daga wata jama’a daga cikin mutanensa. Sai Amru da mutumin sa suka fito daga kogon.
Sai dai shi amru bai da karfi don shayar da shi guba, sai ya tsaye bai je ko ina ba. Amma abokinsa Rafa’ata yana cikin kurucciyarsa, ya cewa Amru zan yi yaki a madadinka. Sai Amru ya ce masa, yaki ba zai amfaneni ba, ka kubutar da kanka, ka tsere ka tsirar da kanka, idan zaka iya.
Sai rafa’ata ya kai masu hare hare ya tarwatsasu, don ya iya kibiya, daga nan sai ya tsare, sun bi shi amma sun kasa kama shi. Amma Amuru ya shi hannun ma’aikatan Mu’awiya suka shigo da shi garin Musil, ba wanda ya san shi, sun bukaci ya bayyana kansa ya ki.
Ya fada masu cewa ‘Ni mutum ne, wanda barinsa ya fiye maku alkhairi, idan kun kasheshi zaku kara cutuwa’.
Daga nan sai suka fara shakka cikin al-amarinsa, sai suka tura shi tare da masu tsaro zuwa wajen Abdurrahman dan Abdullahi Athaqafi wanda shi ne walin Mu’awiya a Musil a lokacin. A lokacinda Abdurrahman ya ganshi sai ya gane shi. Daga nan sai ya aikawa Mu’awiya dan Abusufyan. Ya kuma fada masa inda suka kama shi. Sai Mu’awiya ya bashi amsa da cewa, ai shi ne ya soki Khalifa Uthman da kibiya har sau 9 don haka bama son mu wuce gona da iri, shima a soke shi da kan kibiya har sau 9.”.
Sai Abdurrahman ya fito da shi ya kuma bada umurni a soke shi da kibiya sau 9, amma Amru ya mutu a sokan farko ko na biyu.
Sai suka yanka kansa suka aikawa Mu’awiya, wanda ya bada umurni a zagaya kasar sham da kansa, don kowa yaga abinda suka yiwa wanda yake da hannu a cikin kissan Khalifa Uthman.
Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa, kansa ne na farko wanda aka zazzagaya da shi daga gari zuwa gari a musulunci. Sannan yabada umurnin a kaiwa matarsa Aminatu diyar Sharid wacce take tsare a lokacin a cikin gidan yarinsa.
Sai aka zo da kansa aka ajiye a cikin dakin da ake tsare da ita ba tare da ta sani ba. A lokacinda ta juya sai taga kansa, sai ta yi koka kamar zata haukace, sai daga baya ta nutsu ta ci gaba da koka tana cewa.
Kaiton bakin ciki na, saboda karancin shekarunsa a cikin gidan kaskanci, saboda kunci da zaluncin sarki, kun koreshi daga gareni na lokaci mai tsawo, sannan kuka bani shi kyauta matacce, to ina maraba da wanda ban kasance mai kinsa ba, kuma a yau ma ba zan manta dashi ba.’.
Sai ta juya ga jami’an tsaron da ya kawo kan tana ce masa, : Ya mai manzo Ka koma da shi wajen Mu’awiya ka ce masa: …All..ya maida yayanka marayu, ya rabaka da matarka kuma kada ya gafarta maka zunubanka’.
Sai manzon ya koma wajen Mu’awiya ya fada masa abinda ta fada, sai Mu’awiya ya yi fushi, ya kuma bukaci a kawo masa ita. A lokacinda aka kawo ta, sai yace: Ya ke ‘makiyar All..ka ce kika fidi kalmomin da suka iso gareni?
Sai ta amsa ba tare da jin tsoro ba: Ee, nina, ba tare da barranta kaina daga maganarba, ko neman uzuri wajenka ba. Bana musanta cewa nine na fada, kuma na rantse da All.. na yi kokarin a addu’a .kuma All..zai dauka mana fansa daga gareka, ….”.
Sai wani da ake kira Ayyas Dan Hasil, ya zo kusa da Mu’awiya ya ce: Ka kasheta Ya Amirul Muminina!, mijinta bai fita cancantar kisa ba.
Da taji abinda Ayyas ya fada sai ta ce masa: All..ya halakaka, kanason ya kashe ni kamar yanda ya kashe mijina a jiya, ba abinda kakeso sai ka zama azzalumin a bayan kasa. Ba ka son ka zama cikin masu gyara. ‘
Sai Mu’awiya ya yi dariya, ya ce mata, ki tafi kada a sake jin labarinka a cikin kasar sham.
Na rantse zan fita kuma ba zaka taba jina a sham ba. Sham ba abin so ne a wajena ba…
Kasan Amru dan Alhamqul Khuza’ii ya zama babbar musiba a cikin musulmi, saboda shi sahabin manzon All..(s) ne.
Da dama daga cikin sahabban manzon All..(s) sun yi inkarin abinda Mu’awiya yayi, daga cikinsu har da Imam Al-Hussain Dan Ali (s) wanda yake Madina a lokacin. Ya rubuta wasika zuwa ga Mu’awiya yana inkarin abinda yayi na kashe Amru da Alhamqul Khuzai. Ga nissan wasikar kamar yanda take.
“ ..shin ba kaine ka kashe Amru da Al-Hamaqul Khuzaie ba, sahabin manzon All..(s) bayan All..salihi?, wanda bautar All..ya karar da jikinsa sannan ya rame ba. Launin jikinsa sai da ya zama fatsifashi bayan da ka amintar da shi ka kuma yi alkawali daga All.., wanda da za’a yi wa tsuntsu wannan alkawalin da ya sauka kasa daga kan dutse ya zo wajenka? Sannan ka kashe shi. Don tsoro ga Ubangijin ka. Don kuma rashin daukar alkwarin da muhimmanci?’.
Sai kuma Awfi dan Hisen, Awfi bin Hisen yana daga cikin wadanda suke adawa da siyasar Umayyawa. Kuma aibata salon mulkinsu. Yana kuma yada laifukansu a cikin mutanen Kufa. Labarinsa ya kai kunnen Ziyada dan Sumayya sai ya aika a zo masa da shi. A lokacinda labari ya isa kunnen Awfi sai ya boye. Sai ya ziyad ya bada umurnin dukkan mutanen su fito. Su zo wajensa. Sai kawai ya ga Awfi ya wuce kusa da shi, sai yayi shakkan waye ne? sai ya ce wa wadansa suke tare da shi, waye wannan?
Sai suka ce masa. Awfi dan Hisnu ne. sai yace a zo masa da shi.
Da aka zo da shi sai yace masa: Ya zo maka da makha’inci yana takawa da kafafuwansa. Sai ya juya y ace masa. Menene ra’ayinka dangane da Uthman. ?.
Sai yace: Surukin Manzon All…(s), dkan diyarsa.
-Me zaka ce dangane da Uthman? Mai yawan kyuata kuma mai hakuri. Me zaka ce dangane da ni? Kuma labari ya zo mani kana fada a Basra kan cewa, sai nak ama kubutacce da mai laifi, sannan mai zuwa da wanda yake tafiya.
Sai yace na fadi haka. Sai awfi yace, khuduba ce, ta bijiromani. Sai ya ce : babu bambanci tsakanin mai kodaitar da yaki da wanda yake yakin. Sai ya bada umurnin a kashe shi. .
A nan Awfi ya yi jihadi da harshensa, kamar yadda hadisin Manzon All..(s) yake cewa : Mafificin Jihadi shi ne fadar Kalmar gaskiya a gaban sarki azzalumi. Kuma mafificin shihidai shi ne mutumin da ya yi Magana a gaban Saraki azzalumi sannan ya bada umurnin a kashe shi.