222-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Almujtab (a) dan \fatima (a) diyar Manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun tsaya inda muka yi maganar yanda Mu’awiya dan Abusufyan ya sa aka kashe Hijru dan Adiy daya daga cikin sahabban Manzon All..(s) tare da wadanda suke tare da shi 6 saboda sun ki su zagi Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).
Mun ji yanda aka kawosu kasar sham cikin sarkoki, Mu’awiya yace a kashesu idan basu zagi Amirulmuminina Aliyu dan Abutalib (a) su kuma barranta kansu daga gareshi, amma suka ki, wadanda suka amince suka yi abinda suke so sai aka barsu, wadanda suka ki kuma aka kashe su daya bayan daya bayan a haka kaburburansu a gabansu.
Mun bayyana cewa a lokacinda aka zo kan Hijru dan Adi ya bukaci yayi alwala yayi sallah suka bashi damar yin haka. Sannan suka kashe shi. Maganarsa ta karshe da wadanda suka kashe shi shi ne, kada ku kwance ni cikin daga sarkokin da aka daureni da su, kada ku wanke jinin da ya zuba a kan jikina, zamu hadu da Mu’awiya nan ba da dadewa ba.
Sannan mun fara maganar mutane 6 wadanda aka kashesu tare da Hijru dan Adiy, inda muka ambaci Abdurrahman dan Hassanul Anzi. Wand kafin a kashe shi sai da ya kaishi gaban Mu’awiya mai yuwa ya yafe masa. Amma a lokacinda ya zo gaba ma’awiya sai ya tambaye dangane da Imam Ali(a) sai ya yabe shi. Sai ya dawo kan Uthman sai ya bayyana cewa shi y afara bude kufar zalunci. Sai Mu’awiya ya sa aka maida shi Kufa inda \ziyad dan Sumayya ya sa aka binneshi da ransa .
Sai kuma Safiyyu ibn Fusail. Wanda kafin Ziyad ya tura shi sham, an tsegunta masa cewa yana son aliyu dan Abitalib(a). Sai ya sa aka zo da shi. Sai ya tambaye shi ra’ayinsa dangane da Abuturab, sai yace bai sanshi ba. Sai ya ce ka sans hi. Sai yace kasan Aliyu dan Abutalib (a) sai yace, ya sanshi kuma shi ne baban Hassan da Hussain (a). sai Ziyar Yace shi ne Abu turab. Sai shugaban yansanda ya ce masa amir yace shi ne ka ce ba shi ba, sai yace idan Amir yayi karya sai in goyi bayansa. ?
Sai ziyad ya yi fushi, ya kuma ce masa wannan kari kenan a cikin laifukanka. Sannan ya tura shi sham.
A nan ne sai Ziya yace, dansanda ya bashi sanda wanda ya dake shi da ita har yayi kasa da shi.
Yana dukansa, amma Safiyyu dan Fusail yana cewa na kyautata Magana kan bawan All..muminai.
Sai ya sa yansanda suka dake shi har suka kwantar da shi a kasa. Daga nan sai yace a barshi. Sai ya sake tambayarsa kan cewa, waye Aliyu dan Abutalib a wajenka, sai Safiyyu yace wallahi da ka yayyakani da zarto da kuma wuka ba zaka ji fiye da abinda kaji ba.
Sai yace: wallahi sai ka la’aneshi ko in buge wuyarka. Sai safiyyu yace, to kuwa zaka buge wuyar baki ji ta daga baki na ba. Idan ka dage sai ka bugeta lalle na yarda da All.. kai kuma ka zama shakiyyi.
Sai ya ce a jefa shi cikin gidan yari wanda babu haske. Daga karshe ya aika shi tare da hijiru. Inda Mu’awiya ya bada umurni aka kashe shi.
03-Sai kuma Qabisatu dan Rabi’ah, wanda shi ma yana daga cikin wadanda Mu’awiya dan Abu sufyan ya kashe tare da Hijru. Shugaban yansandan kufa ya tura shaddaad dan Al-Haitham yak ama shi a boye, a lokacinda Qabisatuh ya fahinci abinda yake nufi sai ya dauki takobinsa don kare kansa. Ganin haka wasu daga cikin danginsa sun zo sun tsaya tare da shi don kare shi. Amma shaddad ya fahinci cewa ba zai iya kama shi da sauki wadanda suna kare shi ba, sai yace wa Qabisah, me ya sa zaka kashe kanka al-hali kana da aminci a jininka da dukiyar ka? Saboda yaudara.
A lokacinda mutanensa suka ji haka, sai suka yaudaru, sannan suka ce masa idan gaskiya ne kana cikin aminci a jini da kuma dukiyarka me yasa zaka kashe kanka ka kashe mu?.
Sai Qabisah yace masu: Kaitionku, lalle wannan dan shegen dan karuwa wallah idan na fada hannunsa ba zan fita daga hannunsa ba sai ya kashe ni. Amma gaskiyar al-amarin su ma suna jin tsoron ziyad da kuma Banu Umayya, don sanin sharrinsu, don haka sun gabatar da wannan uzurin ne don su ma su tsira. Da haka kuma suka kyaleshi shaddad yak ama shi ya mikawa Ziyad.
A lokacinda aka kai shi gaban Ziyad sai ya ce masa; Wallahi sai na saka cikin wadanda suke tada fitina suna kira zuwa ga tawaye ga Amir. Sai Qabisah ya ce masa, ban zo maka ba sai da aminci.
Sai kawai yace masu su kaishi gidan yari. Daga karshe ya hada shi tare da hijiru zuwa sham. A kan hanyarsu sai suka wuce ta gidansa, mata da yayansa suka fito suna kuka suna bayyana bakin cikinsu. A nan sai ya bukaci jami’an tsaro su kai shi kusa da su, sai ya je ya basu hakuri, ya kuma yi addu’a All..ya kiyaye su, y ace masa yana datan abubuwa 2 duk masu kyau ne ko yayi shshada, ko kuma a sake shi ya dawo cikinsu.
Sai suka wuce har suka kai Murj Azrah inda ya kasance cikin wadanda suka zabi shahada.
Akwai sauran wadanda suka yi shahada da Hijiru, amma ba’a sami cikekken bayani dangane da rayuwarsu ba. Kuma sun hada da.
4-Shuraik Bin Shaddad Hadrami, 05-Kuddam dan Hayyam Al-Anzi, )6-Mehrez ibn Shihab Attamimi.
Wadannan sune jama’an da suka gabatar da rayukansu don kare addininsu. Tare da Hijru dan Adi. Sun gabatar da kansu a matsayin layya don kare gaskiya. Sun kasance cikin bayin All.. salihai. Basu yi wani laifi bas ai don suna son iyalan gidan Manzon All…(s) sun ki su barranta kansu daga garesu.
Bayan wannan layyar da Mu’awiya dan Abu sufyan da Ziyad dan Sumayya suka yi. Sai labarin ya zama kamar aradu a cikin al-ummar musulmi a lokacin. Da dama daga cikin sun kadu da jin abinda ya faru da Hijru. Saboda sahabin Manzon All..(s) ne ya kuma an sanshi da alkhairi.
Hijir bai yi kome ba in banda umurni da kekyawar aiki, da kuma hana daga mummuna. Ya tashi ya tilastawa Ziyad yin sallar Jumma’a a cikin lokaci. Sannan ya ji Ziyad yana zagin Amirulmuminina Aliyu dan Abi talib (a) kan mimbarin musulmi a Kufa sannan ya tashi yayi inkarin hakan.
Don haka fitattuna sahabban Manzon All..da dama sun bayya fushinsu ga mu’awiya saboka kissan Hijru dan Adi da mutanen da suke tare da shi.
01-Daga cikinsu akwai: Imam Al-Hassan (a). Imam Alhassan (a) ya rubuta wasika zuwa wajen Mu’awiya a sham, yana nuna masa rashin amincewarsa da fushinsa saboda kashe Hijru dan Adi da sahabbansa. Ga nassin wasikar kamar yanda yake.
{.. Ba kaine ka kashe Hijiru dan’uwan Kindah ba, masu sallah masu kuma bauta kuma, masu inkarin zalunci ba. Suna kuma inkarin Bidia sosai. Kuma basa jin tsoron zargin mai zargi ba. Ka kashesu don zalunci, ka keta huruminsu bayan ka dauki alkawali zaka amintar da su, ….}. Imam (a) ya tabbatar masa cewa abinda ya yi sabon All..ne babba.
02-A’isha ummil muminina matar Manzon All..(s). Daga cikin wadanda suka yi inkarin kisan Hijru da sahabbansa, akwai Aisha matar manzon All..(s). wacce a lokacinda Mu’awiya ya shiga wajenta bayan ya kammala aikin Hajja sai tace masa: Shin baka jin tsoron na boye wani da zai kashe ka?
Sai fada mata da wasa: Na shiga gidan Aminci.. sai tace: Baka ji tsoron All..ba, ka kashe Hijru da mutanensa?
02-A’isha ta sha nanata batun kissan Hijiru. Kuma duk sanda ta yi haka, sai ta ruwaito hadisan da taji wajen manzon All..(s) dangane da falalarsa. Daga cikinsu tace : Na ji manzon All..(s) yana cewa: Da sannu za’a kashe wasu mutane a Azraa, wadanda All..zai yi fushi saboda su, a wani wurin tana fada, bayan ta aibata mutanen kufa: Na rantse da All..da Mu’awiya ya san cewa mutanen Kufa suna da wadanda zasu kare shi, da bai yi kokarin kama Hijru ba, da mutanensa ba ya fito da su cikinsu ya je yakashesu a sham ba.
Sai dai dan maciyin hanta ya san cewa mutanen kufa sun tafi, (sun mutu). Amma na rantse da All.. su ne kwakwalen larabawa, .. sune malamai… har zuwa karshen maganarta.
03-Arrabi’u dan Ziyad, Arrabi dan Ziyad Albisry ma’aikacin Mu’awiya a Khurasan, lalle a lokacinda ya ji mummunan labarin kissan Hijru da mutanensa, ya yi kamar hankalinsa ya tafi don bakin ciki, sai yana cewa, . An ci gaba da kashe larabawa bayansa.- wato bayan kissan Hijru- da sun tada yaki bayan kissansa a kan banu umayya ba basu sake kashe wani ba irin wannan kissan ba. Sai dai sun amince suka kaskanta.).
Arrabii ya yi gaskiya, da mutanen Kufa sun hana shuwagabannin Banu Umayya kashe Hijru da mutanensa, da sarakunan banu Umayya ba zasu iya kashe yentattunsu da kuma zababbunsu ba. , amma sun amince da kaskanci da mika kai, basa son mutuwa kan tafarkin All..sai al-amarinsu ya zama mai sauki ga sarakuna suka kaskanta. Umayyawa sun yi ta yin abinda suka ga dama a cikinsu, na kaskantasu da rena al-amarinsu.
Arrabi, ya ci da zama cikin bakinciki, har zuwa ranar jumma’a yayi khudu, sannan yayi sallah. Yacewa mutane na gaji da rayuwa, idan na yi addu’a, ku ce amin., sai yace: Ya Ubangiji idan kasan akwai alkhairi cikin Arrabi ka dauki ransa da gaggawa. Bai bar taron ba sai ya mutu.