Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 219

220-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu dawarhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissashi wadanda suka zo

220-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu dawarhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissashi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu laiattafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

////…. Madalla, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da mukekawo maku. A cikin shirimmu da ya gabata mun tsaya inda muka fara kawo maku, yanda Mu’awiya dan Abusufyan yasabawa sharadin sulhu na farko wanda Imam Al-Hassan (a) ya shardanta masa kafin ya mika masu shugabancin al-ummar musulmi. Wanda kuma shi ne rashin zagin mahaifinsa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).

Ya zuwa yanzu mun ga yanda Mu’awiya ya sabawa wannan sharadin tun ranar fako da mika masa shugabancin Al-Ummar Musulmi. Sannan yanda ma’aikatanasa suka bi shi, ko kuma ya tilasta masu zaginsa da kuma iyalan gidan sa tsarkaka (s).

Sannan mun ji yanda wasu sahabban manzon All..(s) suka ka yi inkarin zagin Amirul muminina (a). daga cikinsu akwai Sa’ad dan Abi Wakkas, da Abdullahi dan Abbas, da Ummu sallam, ummilmuminina ®. Da wasu da dama.

Har’ila yau munji yanIbn Abbas yayi jayeyye da shi Mu’awiya a Makka a lolacin Hajji, sannan mun ji yanda Mu’awiya ya bayyana hakikanin manufofinsa dangane da Iyalan gidan manzon All..(s). Wato banu Hashing aba dayansu, sannan Amirul muminina da Ahlubaitinsa. Munji yanda Mu’awiya yake gurin fassara al-kur’ani mai girma da ra’ayinsa ba tare da fassarar manzon All..(s) ba.

Babban burinsa ne ya batar da sunan Amirulmuminina (a) kwata kwata a cikin al-ummar Musulmi. Ta hanyar kaskanta shi da iyalan gidansa, wadanda sune iyalan gidan manzon All..(s).

Amma sai gashi tun ba’a je Lahira ba All..ya kaskanta Mu’awiya dan Abusufyan ko a kabarin sa da ke birnin Damashqa, ba wanda yake kula da shi, kabarinsa yan cikin wani juji ko bola, wanda ba wanda yake son zuwa kusa da shi. Wannan a yayinda mutane daga koina a duniya suna zuwa birnin Najaf suna dawafin kabarin Amirulmuminina(a). suna neman al-barkansa, ilmin da ya bari ya zama abin tunani da tattaunawan malamai da masu tsoron All..cikin musulmi da wadanda ba musulmi ba.

Sharifu Radhi daya daga cikin jikokinsa ya tattara bayanansa, da wasikunsa ga ma’aikatansa da Khudubobinsa a wurare daban daban a cikin dan lokacin da ya sami damar shugabancin al-ummar musulmi a cikin littafin Nahjul Balagha.

Sharif radhi ya tattara khudubobi kimani 200 kacal, amma wasu malaman tarihi sun bayyana cewa khudubobin Amirul muminin wadanda mutane suka haddace sun kimani 400.

Ibn Abil Hadid daya daga cikin malaman Mutazila ya yi wa littafin Nahjul Balagha sharhi, har na mujalladai 10.

Hatta a cikin wadanda ba musulmi ba, an sami larabawa wadanda suka yi rubutu a kan rayuwar Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) da ilminsa da halayensa. Daga cikinsu akwai Jorck Jodad mutumin kasar Lebanon wanda ya rubuta littafi mai suna ‘Sautul adalatul Insanin” dangane Imam Ali (s).

A yau zamu fara magana a kan shararidi na biyu wanda Mu’awiya dan Abusufyan ya saba daga cikin sharuddan da ya amince zai kiyayesu idan ya karbi shugabancin al-ummar Musulmi. Wanda kuma shi ne. bashi harajin (Dar Ebjard)  ko Dar Ebgar da harshen farisanci. A halin yanzu wannan wurin yana cikin lardin Farsa na kusancin kasar Iran. Wurin yana da ganuwa mai kama da da’ira don kare shi daga makiya a lokacin. Amma a halin yanzu wurin tarihi ne, kuma mutane sukan je yankin don yawon bude ido. Sannan akwai gonaki kewaye da wurin.  

Imam Al-Hassan (a) ya bukaci ya bashi harajin Dar Ibjard ne don ya dauke talauci wa shi’arsa ko mabiyansa. Amma Mu’awiya ya ki cika masa wannan Alkawarin. Tabari ya nakalto cewa mutanen Basra sun hana a bawa Imam (s) harajin wannan yankin. Da umurnin Mu’awiya.

Kuma kawo zai fahinci abinda ya sa Mu’awiya ya hana shi harajin wannan wurin, wanda shi ne kada yayi karfi ya kwace mulki a hannussa.

03-Daya daga cikin manya manyan sharuddan da Imam Al-Hassan (a) ya dauka daga Mu’awiya kafin ya mika masa shugabancin al-ummar Musulmi it ace, kada ya takura shi’arsa da kuma shi’ar mahaifinsa Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a). Amma wannan ma mu’awiya bai cika shi ba, saboda yana son ya shafi mabiyansu a duk inda suka a duniya.

Mau’awiya ya takurawa mabiya iyalan gidan manzon All..(s) a lokacin, har sai da suka rasa inda zasu sa kansu. Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa basu bata sanin wata al-umma daga cikin al-ummomin da suka gabata sun sha wahala kamar yanda yan shia mabiya Amirul muminina da iyalan gidan sun sha irin wahalar da suka sha ba.

Babu wadanda suka sha wahala a hannun Mu’awiya dan Abusufyan kamar Mutanen kufa, saboda su suka fi kowa sanin Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a), su suka fi sanin iyalan gidansa.

Sun dandani adalcin da ya shimfida a cikin shekaru kimani 5 da yayi yana shugabancin al-ummar Musulmi. Amma duk da haka su tsiraru ne idan ka kwatantansu da sauran mutanen kufa.

Mu’awiya sai da ya bisa a duk inda zai samesu ya kashe wasu, ya daure wasu ya rusa gidanjen wasu ya hansu hakkinsu, yashafesunayensu a diwanin musulmi.

Da farkon Mu’awiya ya sanya Ziyad dan Abihi a matsayin walinsa a Kufa bayan mutuwar Mughira dan shuba, wanda ya san shi’ar amirul muminina Aliyu dan abitalib (a) tunda dama yana daga cikinsu.

Ya kashesu a duk inda ya samesu, ya yayyanke hannayensu da kafafuwansu, ya zakulo idanunsu daga kawukansu ya jefasu a waje, ya tseresu a kan turakub dabino, kamar yanda yayiwa Matham Attammar, ya koresu ya tarwatsasu daga kasa.

Bayan al-amura suka tabbata a gareshi, Mu’awiya ya rubutawa ma’aikatansa wasika irin guda ya aika masu inda a ciki yana cewa : Ku dubi duk wanda dalilai sun tabbata a kansa kan cewa shi masoyin Ali da iyalan gidansa ne (a), ku shafe sunansa daga diwani, ku hana shi abinda ake bashi, da kuma arzikinsa. Sannan ya biye da wata wasika ta biyu inda ya umurcesu da cewa : duk wanda kuka tuhumashi da son wadannan mutane, ku azabtar da shi ku rusa gidansa. .

Imam Muhammad  Bakir (a) ya bayyana irin wahalhalun da limamai masu tsarki daga ahlubaitin mazon All..(s) da mabiyansu suka sha a zamanin Mu’awiya dan abu sufyan yana cewa {An kashe shi’armu a dukkan garuruwa. An yayyanke hannaye da kafafuwansu bisa zato, wanda yayi Magana kan son Ahlulbaiti(a) da komawa garemu sai an daure shi, ko a kwace dukiyarsa, ko kuma a rusa gidansa.} Nahjul Balagha 11:43.

Tun bayan da dan Hindu ya karbi iko da shugabancin musulmi mabiyan iyalan gidan Manzon All..(s) suka fara fuskantar matsaloli, na siyasa da zamantakewa da tattalin arziki. An kashe, an wulakanta, an rusa gidaje an kuma kori wasunsu daga gidajensu da kuma kasashensu.

Matsin lamba ta kai ga cewa son iyalan gidan Manzon All…(s) ya zama laifi, kuma shi ne laifi mafi munin da wani masoyin ko mabiyin iyalan gidan Manzon All..(s) zai aikata.

Al-amari saida ya kai son Ahlulbaiti(a) a cikin al-ummar Manzon All..(s) kafirce ne, ficewa daga addini ne ko zama majusu ne. dangane da hakan Al-Kumait ya hakaito hakan a cikin wata kasidarsa inda yake cewa:

Suna nuni da hannaye gareni, kuma zancensu*Itace, wadanda masu nuni sun tabe, mummunan tabewa.

Wata jama’a ta kafirtani, saboda sonku*wata kuma tace mai aikata laifi ne mai zunubi.

Suna aibatani, saboda yaudarassu da aka yi, da batarsu*bisa sonku, kai harma suna isgili suna mamaki.

Suna cewa yana son ;Abu Turabi; ra’ayinsa kuma*Da wannan ake kirana a cikinsu ana mani lakabi.

Ina son Muhammadu So mai tsanani*Da Abbasu, da Hamzatu da wasiyyi

So wand ana sameshi tun bayan kafuwar ginshikin Islama bai sauya waninsa ba

Yayan ammin annabi kuma kuma mafi kusancinsu*mafi soyuwan munane a gareni gaba dayansu.

Idan sonsu ya kasance son su shiriya ce nayi muwafaka*Kuma bai yi kuskure bai dan batace.

Abdullahi ibn Kathir Assahami, idan wani ya aibata shi da son iyalan gidan Manzon All..(s). sai ya mayarmasu da wannan kisidar yana cewa:

Idan laifin mutum ya zama *son Annabine, wallahi bam ai zunubi bane

Kuma Yayan baban Hassan da mahaifinsu*sune wadanda suka tsarkaka a cikin cikunan iyaye da tsosho.

Shin ana ganin laifi ne in so su?* Sai dai sonsu kaffarar zunubi ne.

Kan wannan hanyar sauran sarakunan banu umayya da Abbasiyawa daga baya, suka bi suna zaluntar shi’ar iyalan gidan Manzon All..saboda rashin dama zamu takaita.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted