211-Assalamu alikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmi na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma sirar Imam Al-Hassan Al-Mujtaba (s) dan Fatimah (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo mako, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da magana dangane da ziyarar Imam Al-Hassan (a) zuwa kasar Sham da kuma munazarorin da ya yi da mu’awiya da mutanensa.
Mun kuma bayyana yanda, wasu daga cikin fadawan Mu’awiya wadanda suka hada da Amru dan Asi da Walidu dan Uqba, da Marwan dan Hakam, da kuma Mughira dan Shuba suka tashi suka zagi Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) da kuma Shi Imam Al-Hassan sannan suka dora masa dukkan laifuka daga ciki har da kissan Uthman dan Affan.
Sannan mun fara jin matarnin Imam Al-Hassan (a) inda ya fara da Mu’awiya dan Abusufyan, ya tabbatar da muninsa, da kuma fifikon mahaifina Amirulmuminina (a) kansa a jahiliyya da musulunci.
Yayi sallah mu’awiya da mahaifinsa suna kafiyar, basu shiga musulunci ba sai a matsayin ‘Mu’allafatu kulubuhum, wato wadanda ake kodaityar da su, da basu kudade don su kyautata imaninsu. Banda haka Amirul muminina (a) yayi sallah a kiblolin biyu, yayi bai’a biyu, rindhwan da fatahi, ya rike tutoshin manzon All..(s) a badar da Uhud da Ahzab, a lokacin Mu’awiya da babansa kafirai ne.
Nun tsaya inda yake cewa, {.. na hadaku da All..shin baku san cewa shi ne wanda yake rike da tutan manzon All..(s) a badar ba ? Sannan tutar mushrikai tana hannun Mu’awiya da kuma babansa? Sannan tana tare da shi ya sake haduwa da ku a ranar Uhud da Ahzaba tutar manzon All..(s) tana hannunsa ba ? Kuma tutar Mushrikai na hannun kai Ma’awiya da babanka ba? Kuma ko wanne All..h yana bashi nasara yayi budi ta hannunsa,?. Ya kuma tabbatar da hujjar All..ta hannunsa, All..ya yada addininsa, ya kuma gasgata zancensa, sannan manzon All..ya na mai yarda da shi, sannan yana fushi da kai da kuma babanka ya Mu’awiya?.
Shin ya Mu’awiya ka manta ne, wata rana babanka ya zo yana kan jan rakumi, kai kana korashi, sannan dan uwanka Utbatu wannan yana jansa, sai manzon All..(s) ya ganku, sai ya ce: {Ya Uabangiji ! Ka la’ani mahayi da mai ja da wanda yake koran rakumi}.
Shin ka manta, Ya Mu’awiya! Da wata kisidan da ka rubutawa mahaifinka a lokacinda yake son musulunta kana hana shi yin hakan?.
Kana cewa:
Ya Harbu lalle kana ka taba mika kai- Bayan kissan mai nikawa da aka yi Badar.
Kawuna, da Ammina da ammin mahaifiya na ukkunsu- Da kuma Hanzalar mai Alkhairi, wanda ya daukaka mu.
Kada ka karkata zuwa wani al-amarin da zaka kallafa man- Al-hali masu rawa mata a Makka, sun tarwatsae.
Mutuwa ta fiye maka, kan fadin Kalmar kiyayya- Dan Harbin ya karkata daga daukaka, idan har yayi hakan.
Wallahi ! abinda na boye a cikin al-amarinka, (ya Mu’awiya) ya fi yawa kan abinda na bayyana.).
{Na hadaku da All.. Yak u wadan nan Mutane, shin ko kun san cewa Aliyu (a) ya haramtawa kansa sha’awowan duniya a cikin sahabban manzon All..ba wanda ya kama kafarsa, sai All..ya sauko da aya a cikin al-kur’ani yana fada masa cewa .
Ya ! Ku wadanda kuka yi Imani, kada ku haramtawa kanku dadadan da All…ya halatta maku. ?
Kuma lallei manzin All..(s) ya aiki manya manyan sahabbansa, wajen yahudawan Banu Kuraiza, suka sauka a wajensu, amma sai suka koresu suka dawo wajen manzon All..(s). Sai ya aiki Aliyu (a) da tuta ya ji ya tilasta masu amince da hukuncin All..da manzonsa (a). Haka ma ya aikata a Khaibara.
Sai yace, Ya Mu’awiya! Kana tsammani ban sani ba, kan cewa manzon All..(s) ya aika maka ka zo ka rubuta masa wasika zuwa Banu Khuzaima, sai ka ki zuwa saboda kana cin abinci sai yayi addu’a a kanka yana cewa, Ya ce Ubangiji kada ya s aka koshi har ka mutu ba ? .
Ya ku wadan nan Jama’a! Ina hada ku da All.., shin baku san cewa manzon All..(s) ya la’ani Abusufyan a warare 7 ba? Wanda baku isa ku yi inkarinsu ba ?.
Na farko ranar da ya je Ta’ifa yana son kiran kabilar Thaqif zuwa ga addini, sai ya hadu da shi a wajen Makka, ya zage shi, ya wawaitar da shi, ..ya karyata shi, yayi alkawalin cutar da shi, kuma ya so ya dake shi, sai All..da manzonsa suka la’aneshi, suka kyale shi.
Sai ranar Ayarin Abusufyan, a lokacinda ya fito da ita daga sham, sai Abusufyan ya kaucewa masa ya bi ta bakin ruwa, ya kubuce masa, sai manzon All..(s) ya la’aneshi, sai kuma saboda ita aka yiyakin Badr.
Sai kuma na uku! A Uhudu, a lokacinda manzon All..(s) yana samansa, shi kuma yana kasan dutsen yana ta nanata cewa: Daukaka Hubal, dauka hubal, sai manzon All..(s) yala’ane shi sau 10 sannan musulmi ma suka la’aneshi.
Sai kuma na hud, ranar da Rundunoni suka zo da Gadafan, da yahudu, sai manzon All..(s) ya la’aneshi ….
Sai na biyar, a ranar da manzon All..(s) ya zo masallacin Harami, tare da hadaya wanda aka hana shi isa inda za’a yankasu, a hudaibiyya, sai Manzon All..(s) ya la’ani Abu Sufyan, ya la’anci shuwagabannin da mabiya, yace: La’amammu ne gaba daya, babu muminini ko daya daga cikinsu.
Sai aka ce masa, Ya manzon All..(s) shin ba fatan cewa ko da daya daga cikinsu zai musulunta, yaya batun la’antarsu da kayi ? sai yace: La’ana ta ba zata shafi mabiya ba, amma ba wanda zai tsira daga shuwagabanni.
Sai kuma na 6 ranar Jan rakumi.
Sannan na 7, ranar da suka tsaya a Akaba don su ingiza taguwar manzon All..(s) ta yi jifa da shi cikin rami, su kashe shi, su 12 ne, daga cikinsu akwai Abu sufyan}.
Da wadannan kalaman Imam Al-Hassan (a) ya saukar da Mu’awiya daga fadarsa zuwa kabarinsa, daga kujerar sauransa zuwa makaransa, ya barshi cikin bakin ciki da kuma fushi.
Sannan Imam (a) ya juya zuwa wajen Amru dan Asi yana cewa:
{Kai kuma Ya dan Asi ! Mahaifiyarka ta haife ka bata san waye ubanka wanda ta yi zina da shi ba, don haka mutane hudu suka yi jayayya a kanka, sai mafi kissan mutane daga cikinsu, mafi munin nasaba daga cikinsu, mafi munin matsayi daga cikinsu, ya sami rinjaye a kan sauran. Sannan babanka ya tashi yace: Lalle makiyi na Muhammad (a) marasa baya ne baya haihuwa, sai All..ya saukar da abinda ya saukar a kansa na ayoyin Alkur’ani.
Ka yaki manzon All..(s) a dukkan yake yakensa, ka aibata shi, ka kuma cutar da shi a Makka. Ya kulla masa kaidi iri –iri, kana daga cikin mutanen da suka fi karyanta shi, da kuma adawa da shi.
Sannan ka fita ka bi ma’abuta jirgin ruwa a wajen Najashi, don ka dawo da Jaafaru da mutanensa zuwa Makka, a lokacinda ka rasa abinda kake kauna, All..ya dawo da kai a tabe, …. kai makiyin banu Hashim ne a jahiliya da Islam.
Banda haka ka sani, kuma wadan nan da suke tare da kai sun sani, kan cewa ka aibata manzon All..(s) da baituka 70.
Ka aibata shi, har sai da yace: Ya Ubangiji ! ni bana tsara wake, ka sani, bai kamata in yi haka ba! Ya Ubangiji ka la’aneshi da dukkan harafinda ya tsara kasidarsa. Don haka tare da haka All..ya la’aneka, la’anar da babu iyaka.
Amma abinda ka ambata dangane da Uthman, kai ne ka rura masa wuta a duniya, sannan ka arce zuwa Falasdinu, A lokacinda labarin mutuwarsa ya zo maka , sai kace, (ni ne baban Abdullah, idan an ji wa wani rauni, sai na sa raunin ya zubar da jini). Sannan ka kai kanka wajen Mu’awiya ka saida addininka da duniyarsa,
Bama aibataka da kiyayya a garemu, haka ma bama zarginka da rashin sommu, Amma na Rantse da All..baka taimakawa Uthman yana da raiba, baka kuma baka taba yin fushi saboda kisansa ba.
Kaitonka ya dan Asi! Shin ba kaine ka fada dangane da Banu Hashin ba, a lokacinda kake kan hanyarka zuwa wajen Nashishi kana aibata su ?. }.
Sannan Imam (a) ya bashi amsar kisidar da yayi yana aibata Banu Hashin, inda a cikinta ya bayyana yanda Amru dan Asi ya kasance makiyi ga musulmi da musulunci, a jahiliya da kuma bayan samun ikonsa. Da kuma tabbatar da cewa yana da hannu cikin zubar da jinin Uthmanu, a yayinda yake zargin shi da kuma mahaifinsa da yin haka, butani da karya. Sannan daga baya ya koma bangaren Mu’awiya don son duniya.
Daga nan sai Imam (a) ya koma kan Walid dan Uqbah yana cewa: