08-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirummu na Al-adu da ci gaban musulunci a tarihi. Shiri wanda yake kawo maku ci gaban da addinin musulunci ya samu tun bayyanarsa ya zuwa yanzu. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///…Madalla, masu sauraro a cikin shirimmu da ya gabata mun tsaya inda muka yi Magana kan cewa, manzon All..(s) a matsayinsa na shugaban al-ummar musulmi a madina wacce kuma ita ce daular musulunci ta farko, yayi ayyuka na da farko tabbatar da akidun da aka dora addinin musulunci a kansu, wanda Kalmar tauhidi ita ce ta farko, kuma yayi amfani da ikon da yake da shi a daular Musulunci ta farko don yin hakan.
Har’ila yau mun yi maganar yadda ya rarraba rassan hukuma ko daular musulunci a lokacin, amma kuma dukka ko mafi yawansu a masallaci, inda nan ne kotun da yake alkalanci, nan ne makarantar da yake karantar da addinin musulunci ya kuma fadawa musulmi sabbin dokokin da All..ya saukar masa. Ya ayyana masu kula da al-amuran kudaden gwamnati wadanda suka hada da tattarasu a Madina da wajensa, da rubuta tu da kuma nau’oinsu. Zakka ne, Ko Ganimar yaki, ko kyauta ko Khumusi da sauransu.
Hakama ya samar da wasu mutane masu kula da arzikin da yake rabawa sahabbansa, na kudade da filayen noma ko gidaje da sauransu. Har’ila yau masallaci ne wajen tattara mayaka wadanda zasu je yaki, ya kuma kodaitar da su zuwa yakin.
Sannan akwai bangaren masu leken asiri, da kwamandojin sojojinsa. Da kuma bangaren yada labarai da sanarwa.
Sannan yana da bangaren tattara wasiku da takurdun yarjeniyoyi wadanda ya rubutawa sarakuna ko ya cimma da shuwagabannin wasu kabilu, ko kasashe da sauransu.
Bayan dukkan wadan nan tsare tsare manzon All..(s) ya fara aikin yada addinin musulunci da kuma fadada daular musulunci, wadanda suka hada da kulla yarjeniyoyi da kabilun larabawa. Malaman tarihi a wannan zamanin sun tabbatar da cewa tsarin tafiyar da gwamnati wanda manzon All..(s) ya samar a Madina a lokacin, wani cikekken tsari ne na tafiyar da gwamnati wanda bai bar wani bangare na rayuwa wanda bai yi magana a kansa ba. Kuma wani abin lura a nan shi ne dukkan wadan nan tsare tsare sun tabbata a aikace cikin dan karamin lokaci.
Daga ciki bayan sauya al-kiblar da musulmi suke sallah daga masallacin Al-Aksa zuwa Haramin Kaaba, aka saukar da azumin watan Ramadan, sannan aka kammala sauko da hukunce hukuncen sallah, da zakkan fidiri. Hukunce hukunce kamar kisasi, da diyyah, da jihad, rabon ganima, gado, haramcin shan giya, hukunce hukuncen aikin hajji da umra da sauran hukunce hukunce da suka biyo baya duk suka sauka suka kuma sauya rayuwar larabawa gaba daya. Sun kuma samar da hadin kan da ba’a taba tsammani ba a cikinsu.
A cikin shekaru 10 da yayi yana shugabancin daular musulunci ta farko manzon All..(s) ya shiga yaki da makiya har sau kimani 80 da yan kai. A cikin wadan nan yake yake, wani lokaci yakan fita daga madina ya kuma jagoranci yake yaken da kansa ko kuma ya aika wani daga cikin sahabbansa ya jagorancesu.
Banda haka malaman tarihi sun maida hankali kan yanda manzon All..(s) yake gudanar da wadan nan yake yake, inda yakan shawarci sahabbansa a wasu lukuta, ya kuma ji ra’ayinsu ya kuma yi amfani da ra’ayinsu. Sannan a wasu lokutan kuma kai tsaye ya fadi yanda za’a yi yakin, ko yanda za’a tsara shi.
Sannan hakkinsa ne, yanke shawara ta shiga yaki ko kuma sulhu daga karshe. Masali a yankin Uhudu, duk da cewa yana da wani ra’ayi daban, amma ya amince da ra’ayin mafi yawan wadanda ya shawarcesu kan yakin. Wanda kuma shi ne fita wajen Madina.
Yaduwar addinin musulunci a kasashen larabawa makobta da madina, ko tsibirin larabawa, ya sa musulmi sun hadu da mutane daban daban, masu al-adu da halayen da basu sani ba.
Da haka kuma al-adun larabawa suka hadu da al-adun wasu kabilun da kuma halayensu, amma a duk lokacinda wata al-ada ko halaye na wasu kabilun suka yi karo da addinin musulunci sai a yi watsi da ita, sannan wadanda basu saba ba a karbesu.
Bayan fatahohin da aka samu, wadanda suka fafada daular Musulunci, musulmi suna gudanar da su dai dai yansa manzon All..(s) ya umurcesu su yi, sannan sukan saurari umurninsa, a duk lokacinda wani al-amari ya shige masu duhu.
Sannan bayan wafatin manzon All..(s), musulmi sukan dauka matakan da suka ga ya dace, su dauka don fahintar sabbon al-amuran da suke shige masu duhu daga wadanda suka sani, a wasu lokuta.
A zamanin daulolin Banu Umayya da kuma Abbasiyawa, daular musulunci ta yi fadi yadda ana iya kwatantashi da kasashe 50 ko fiye da haka a zamanin da mukeciki. Don haka wadannan, cibiyoyin gudanarwa, sun fadada kuma an samar da wasu sabba mai kama da su a wasu sabbin fannonin da aka samar saboda tafiyar da harkokin mulki yanda ya dace.
Sai dai wani abu mai muhimmanci a wanda kuma dole a fade shi , shi ne, an sami inhirafi, ko karkata a cikin ainihin tsarin da manzon All..(s) ya barwa al-ummansa, wanda daga cikin, an sami sako sako ko kuma yin watsi kwata kwata da hakkin iyalan gidan manzon All..(s) a bayansa. Sai dai wannan bai fidda daular da kuma al-ummar ta zama ba al-ummar musulmi ba.
Don daga baya an sami wasu shuwagabannin da aka yi wadanda suka sanya rayuwar jin dadi da wasanni da kuma fuskantar shuwagabannin da malamai rayuwar duniya, suka karanta tunani da kuma sanin lahira. Don haka a irin wannan halin a wasu lokuta makiya sun kutsa cikin al-amuran gudanarwa na al-ummar musulmi suka kuma jirkita masu lamura da dama.
Har’ila yau, wannan bai hana ci gaba da kuma yaduwar addinin musulunci a duniya da kuma fadadar daular musulunci ba.
Banda haka an ci gaba da tarjamar wasu ilmomi daga wasu kasashen da suka ci gaba kafin musulunci, don musulmi su amfana da ilminsu ko al-adunsu wadanda basu sabawa musulunci ba. Kuma ilmin da aka tarjama sun yi tasiri a cikin rayuwar musulmi daga bayana, wasu alkairi ne wasu kuma, sun gurbata al-adun musulmi, sun lalata hattaakidunsu a wasu lokutan.
Don haka muna iya fadar cewa, ilmi da kuma rubutu suna daga cikin al-amura wadanda ba’a taba samun wani addini ko kuma al-ada a baya wadanda suka karfafa su kamar yanda addinin musulunci ya karfafa su, ya kuma kodaitar kan nema da kiyayesu ba.
A wani bangare muna iya cewa, Al-kur’ani mai girma da hadisan manzon All..(s) da kuma ma’asumai, da waliyan All..a duk tsawon zamani, da kuma addinan da suka gabata gaba daya sun yi kira zuwa ga amfani da hankali a cikin al-amura inda ake bukatarsa.
Wannan saboda imani ido a rufe ba karbebbe bane a wajen All..madaukakin sarki. Hankali yana taimaka mana wajen sanin All..yana taimaka mana wajen fahintar wasu daga cikin sifofin All..wadanda hankali suna iya fahintarsu, kamar kadaicinsa.
A cikin aya ta 67 na suratul Anbiya inda All..yake cewa
{ “Tir da ku, da abin da kuke bauta wa, wanin Allah! Shin, bã kwa hankalta?”}
yana daukar yin tarayyar da shi rashin hankali ne, ko rashin amfani da hankali ne. All..yana aibata mutum jahili, kuma yana daukar jahilci a matsayin nakasa.
Ma’anar jahili a nan ba yana nufin wanda bai iya rubutu da karatu ba! Saboda, sau da dama muna ginin wadanda suna da ilmi mai yawa a zahiri, amma a hakika su jahilai ne. Su masana ne a zahiri idan ka ga ko ka ji yawan ilminsu, amma a kwakwalwansu ilmin ne kawai, amma basa tunanin abubuwan da suka shafi rayuwar duniya da kuma lahira da gaskiya.
Mutum ko menen yawan ilminsa, amma yana ganin, akwai bambanci tsakanin addinin da sauran ilmi, a addinin musulunci, ko da yana riya sanin addinin bai da matsayi a cikinsa. Babu abinda ya rage masa sai dai yayi shiru.
Babu wani addinin All..a baya, ko wani al-amari a cikin addinin musulunci wadanda suke adawa ko kin ilmi ba.
Manya manya manyan malaman addini da aka yi bayana bayyanar addinin musulunci, kamar Jabir dan Hayyan, Muhammada dan Musa Khawarizmi, Mohammad dan Zakariya Razi, Farabi, IbnHaitham, Ibn Sina, Ibn Rushdi, da wasu da dama, wadanda bamu ambata ba, duk sun nuna yanda addinin musulunci ya himmatu da ilmi da kuma Hikima a ko ina suke.