176-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahari ko kuma cikin littafin Mathnawa na Maulana Jalaluddin Romi. Ko kuma dai cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///…Madallah, Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan (a) dan Fatima (s) diyar manzon Allah (s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku abubuwan da Mu’awiya dan Abusufyan ya aikata a lokacinda al-amuran shugabanci suka koma hannunsa.
Daga ciki mun ambaci yadda hadisan karya wadanda aka jinginawa manzon Allah (s) na falalar mu’awiya da danginsa Banu umayya da kuma khalifofi 3 na farko da wasu sahabban, sun yi tasiri har suka raba kan al-ummar musulmi tun lokacin har zuwa yau.
Hadisan da Mu’awiya ya sa aka kirkirosu, sun kaskanta iyalan gidan manzon Allah (s), sun kuma katangance mafi yawan musulmi daga sanin matsayinsu da kuma darajarsu a wajen Allah da manzonsa (s). Sannan wadanda suke binsu sun sha wahala a hannun mu’awiyan da farko, kamar yadda ya kashe Hijir dan Adiy da sahabbansa saboda sun ki zagi ko la’antar Aliyu dan Abutalib (a).
Mun kuma ji yadda Ibnu Taimiyya wanda ya zo a karni na 6 ko 7 ya yada akidar “Khalifofi guda uku, wanda ya samo asali daga hadisin Abdullahi dan Umar, amma wasu malamai daga cikin malaman Ahlussunna suka yi masa raddi, suka kuma sanya Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) cikin khalifofi rashidina guda 4.
Mun ce wannan ya faru ne a zamanin sarki Harunar Rashid, wanda kafin haka yake da ra’ayin khalifofin rashiduna uku ne Abubakar, Umar da Uthman, amma sai wani malamin Ahmad bin Hambal wanda ake kira Abu-Muawiya ya farkar da shi, ya nuna masa cewa, masu yayata cewa khalifofi rashidina uku ne, sune dengin Khalifa Abubakar Taimawa, dangin Khalifa Umar Adiyawa da dangin banu umayya wato dangin Khalifa Uthman Umayyawa, amma banu Hashim dangin Abbasiyawa basu da rabo a khalifancin manzon Allah(s) a bayansa, sai Aliyu dan Abitalib (a). Amma abbasiyawan ko sarki Haruna ya koreshi daga khalifancin.
A nan ne sarki Haruna ya dawo cikin hayyacinsa ya gano abinda suke nufi, sai ya bada umurnin a sanya Aliyu dan Abitalib cikin khalifofi Rashidina, don haka sai ya zama khalifa na hudu tun lokacin a wajen Alussunna waljama’a.
Daga nan sai suka shiga maganar cewa, shin tsakanin khalifofi 4 Rashidina, wa ya fi wani daraja.
A nan ne sai Mohammad dan Idris Shafi;ii shugaban mazhabar shafi’iyyah ya bayyana cewa shi yayi Imani kan cewa a cikin sahabban manzon Allah (s) da kuma tabi’ai Aliyu (a) ne ya fi daraja bayan Abubakar da Umar da kuma Uthman. Kamar yadda ibn Hajar al-askalani dan mazhabar shafiiyya ya kawo a cikin littafinsa Fatahul Bari sharhin sahihul Bukhari JZ 7 SH21.
Haka ma Yahyah dan Mu’in, daya daga cikin manya-manyan malaman ahlussunnah na farko yana ganin, Imam Ali (a) ya fi Uthman daraja, kuma shi ne Khalifan musulmi na 4. Sannan yana cewa dukkan shuwagabanni Ahlussunna sun amince da cewa shi ne khalifa na hudu, sannan ya aibata wadanda ba su amince da Aliyu dan Abitalib (a) a matsayin khalifa na 4 ba.
Aliyu bin Ju’uda (wanda ya rayu daga shekara ta 134-230 bayan hijira) kuma daya daga cikin manya-manyan malaman Ahlussunnah, ya yi watsi da hadisin Abdullahi dan Umar, da akidarsa ta Ukkunta Khalifofi Rashiduna. A lokacinda aka karanta masa hadisin Abdullahi dan Umar, ya yi fushi ya kuma aukawa Abdullahi dan Umar, yana aibata shi yana cewa: Ku dubi wannan yaron wanda ko sakin matansa bai iya ba, wai yana cewa: Mun kasance…sai ya kawo hadin da Abdullahi dan umar ya kirkiro na cewa Abubakar da Umar da Uthman ne kawai suka fi kowa a a zamanin manzon Allah (s) duk sauran sahabbai daya suke).
Hakama Ibn Abdulbar Qurdubi, shi ma wani babban malami daga cikin malaman Ahlussunna, tare da riko da Ijma’in malaman Ahlussunna, wadanda suka hada da malaman fikihu da malaman hadisi, suna ganin Ali(a) shi ne yafi darja a cikin sahabbai gaba daya, amma bayan Uthman. Kuma ba wani daga cikinsu da yake shakkar hakan.
Amma sabanin da ke cikin malamai shi ne, wasu daga cikinsu suna fifita Aliyu dan Abitalib(a) kan Uthman. Sannan wasu daga cikinsu, suna ganin Ali(a) ya fi hatta Abubakar da Umar daraja a wajen Allah da manzonsa (s).
Sannan Ibn Hajar Al-askalani bashafi’e, kuma babban malamin Ahlussunnah, ya yi watsi da hadisin Abdullahi dan Umar, kuma ya yi imanin kan cewa hadisin nasa yayi karo da ra’ayin mafi yawan malaman Ahlussunnah, sannan ya kawo dalilai da dama na yin watsi da hadisin nasa, inda ya yake kafa hujja da hadisin Abdullahi dan Masa’udu, wanda yake cewa{Mun kasance muna fada kan cewa mafi daraja a cikin sabban manzon Allah (s) a Madina shi ne Aliyu dan Abitalib), ya ce wannan hadisin yana nuna fifikon Aliyu dan Abitalib (a) kan dukkan sahabban manzon Allah.(s).
Ibn Hajar Al-askalani ya ci gaba da cewa, wasu manya-manyan malaman Ahlussunnan kamar Yahyah dan mu’in, Sufyanu Thauri, ibn Khuzaima, duk suna ganin Ali(a) ya fi Uthman. Sannan wasu malaman kamar, Malik da Yahya Kattan da Ibn Hazim, su kuma suna ganin Ali(a) da Uthmai matsayinsu daya ne. ba wanda ya fi wani.
Amma abinda ya zo cikin tarihin musulunci na fifikon Aliyu (a) kan sauran sahabban manzon Allah (s), hatta da Abubakar da Umar, suna da yawa kuma ingantattu, har saida wasu sun yi kokarin boye falalarsa, daga cikin har da kirkiro hadisai daga bakin shi Imam Ali(a) da kansa da manufar kaskanta shi.
Daya daga cikin akwai hadisan da suka kirkiro, bisa karya suka kuma nasabta shi ga dansa Muhammad Al-Hanafiyya, daga Muhammad dan Isma’ila Albukhari ya karbo daga Muhammad dan Hanafiyya dan Imam Ali(a), ya ce: Na tambayi babana: Wa yafi bayan manzon Allah (s) ? sai babana yace : Abubakar. Sai na ce bayan Abubakar wa ya fi ? ya ce: Umar. Wai sai Muhammad dan Hanafiyya ya ce: na ji tsoron kasa idan na tambaye shi wa yafi bayan Umar ya ce, Uthmanu, sai na nace: Bayan Umar kam ai sai kai,? Wai sai mahaifinsa ya ce: Ai ni daya ne daga cikin musulmi, ba wanda na fi cikin mutane.
Idan zaku lura a cikin sanadin wannan hadisin akwai Muhammad ibn Kathir, da Mansur dan Dinar, wadanda suka kasance raunana. A wajen malaman tantance mazaje, kuma suna sukansu.
Sannan akwai Abu Yaalaa a cikin sandin ruwayar, idan suna nufin Shadda dan Aws ne, malaman tarjama sunce, idan Shaddad dan Aws ne, suke nufi! to bai ruwaito hadisi daga Muhammad dan Hanafiyya ba.
Don haka idan muka lura da hadisan da suka gabata, da kuma ra’ayin malamai a kansu, zamu fahinci cewa, sahabban manzon Allah (s) da Tabi’ina da malamai wadanda suka hada da malaman fiqihu da hadisi, duk sun gamu a kan cewa, Imam Ali (a) shi ne mafificin mutum bayan Khalifa Uthman sannan shi ne khalif ana 4 daga cikin khalafa Urrashiduna a wajen Ahlussunna waljama’a.
Amma dan Taimiya Al-Harrani al-hambali, yana shakka cikin khalifancinsa, kuma yana inkarin falalolinsa, yana tuhumarsa da neman duniya, da kuma zubar da jinin musulmi. Shin abin tambaya shi ne?, Ibnu Taymiyya sunni ne?, kuma yana bin salaf?.
Abinda ya tabbata shi ne, Ibnu Taimiyya ya biyewa banu umayya, wadanda suka yaki Imam Ali(a) da dansa Imam Hassan (a), suka kwace shugabanci daga banu Hashimawa, iyalan gidan manzon Allah (s). Don haka Mu’awiya ya yi ta neman laifuka da aibobin iyalan gidan manzon Allah (s), yayi ta yadawa, amma hakan bai tauyasu da kome ba, sai dai ya kara daukakasu ya kuma kara daga darajarsu, ba wanda ya yi asara sai wanda yake ganin zai iya kwace falala da daukakan da Allah yayi musu(s).
Dan Amir dan Abdullahi dan Zubair ya yi rashin ladabi ga Ali(a) ya kuma fadi wasu mummunan kalamai dangane da shi. Sai mahaifinsa Amir dan Abdullahi dan Zubair yayi wa dansa nasiha yana cewa: Ya da na! Ina maka nasiha kan ka daina neman laifi da kuma aibata Ali (a) ina maka nasiha ka daina wannan mummunan dabi’ar da kake yi, sannan ina son ka sani, kan cewa Banu uamayya sun dauki shekaru 60 suna kokarin tauya matsayin Imam Ali (a) amma sai gashi ko wacce rana Allah ta’ala yana kara daukaka shi. Wannan kamar yadda Baihaki ya kawo a cikin littafinsa ‘Almahasinu wal-Masawi’u JZ 1 SH 25. Da kuma littafin Masawi’u Man Aada Aliyu bin Abitalibin (a).
Amma malaman shi’a suna kafa hujjoji da ayoyin Alkur’ani mai girma daga ciki har da inda Allah (t) yake cewa {..da kawukammu da kawu kanku..} a cikin Ali-Imrana, da kuma daruruwan hadisai , ingantattutu daga manzon Allah (s), wadanda suka hada da, hadisin gashashen Tsuntsu, hadisin Ghadir, hadisin manzila da sauransu, kan cewa Aliyu dan Abitalib (a) ba tare da wani shakka ba, shi ne mafi daukaka a cikin sahabban manzon Allah (s) daga ciki har da khalifofi uku wadanda suka gabaceshi, kuma shi ne khalifansa ba tare da fasila ba.
Sannan bisa abinda ya tabbata a tarihin musulunci, wanda manya manyan sahabban manzon Allah (s) suka ruwaito, Imam Ali (a) shi ne, sahabin manzon Allah (s) na farko, don shi ya fara musulunta, tun lokacin fara saukar Wahayi, kuma shi ya fi cancanta da shugabanci kan dukkan sahaban manzon Allah (s).
Bari mu rufe shirimmu na yau da hadisin Khazaifa dan Yaman, daya daga cikin manya manyan sahabban manzon Allah (s) yana cewa (Na rantse da Allah, wanda ran Khuzaifa yake hannunsa, lada da aikin Aliyu (a) guda (wato kisan Amr dan Abdu wad, a yakin Khandak ya fi aikin dukkan al-ummar manzon Allah (s) har zuwa yanzun da nake Magana, kuma har zuwa ranar kiyama).
Wannan hadisin ya tabbatar da fifikon Aliyu dan Abitalib (a) kan dukkan sahabban manzon Allah (s) daga ciki har da Khalifofi da kuma dukkan al-ummar manzon Allah (s) kuma shi wasiyin annabi(s) na farko ne.