Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’aini mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da lattafin Dastane Rastan na Shahid Ayatullahi Murtdha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
////…. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra(s) diyar manzon Allah(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) da muke mawo muku, mun yi Magana dangane da yadda aka kwace iko da kuma khalifancin manzon All..(s) daga hannun Aliyu dan Abitalib (a).
Banda haka an yi kokari tilastawa Aliyu dan abitalib (a) yin bai wa Khalifa Abubakar da karfin tuwo, wanda hakan ya sa Zahra(s) ta yi barin cikinta na Muhsin, sannan an ji mata ciwo a fuskanta da kuma saman hannunta, sannan wasu kusoshin na kofar gidansu sun ji mata ciwo a kirginta.
Amma duk da haka a lokacinda suka fito da Aliyu (a) zuwa masallaci don tilasta masa bai’a, Fatima (s) ta tara hashimawa mata suka rakata zuwa masallacin manzon Allah (s) inda ta je ta sami cewa ana tsare da shi tare da barazanar kashe shi idan bai yi bai’a ba. Bayan jayayye mai yawa ta sami nasarar kubutar da shi daga hannun Khalifa a Abubakar.
Amma bata kare a anan ba, ko kuma zamu ce a yanzu ne masu iko a madina bayan wafatin manzon All..(s) suka fara daukar wasu matakan kan iyalan gidan manzon All..(s), inda zamu fara Magana dangane da kwace gonar Fadak ta Zahra (s) wanda ya kai ga ta je masallacin babanta manzon All..(s) ta yi khuduba wacce ake kira Fadakiyya, inda a cikin ta ta yi maganar khalifancin mijinta kadan, sannan ta yi maganar gadon ta da kuma wasu al-amura da suka shafi makomar al-ummar babanta manzon All..(s).
Kafin mu karanta wani bangare na Khudubar Zahra (s) a masallacin manzon All..(s) a gaban khalifa Abubakar da kuma sahabban manzon All..(s), akwai bukatar mu yi wata shinfida ko kuma gabatarwa wacce ta zama wajibi don mu fahinci abubuwan da suka sa tayi khudubar daki daki.
Da farko zamu bude wannan maganar ne da aya ko ayoyin Al-kur’ani mai girma inda All..T yake cewa
{Sabõda haka ka bai wa mai zumunta hakkinsa da miskĩnai da ɗan hanya, wannan shĩ ne alhẽri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan sũ ne mãsu sãmun babban rabo.} Rum 38.
Wannan ayar umurni ce daga All..madaukain sarki ga manzonsa Muhammad (s) na ya bawa mai kusanci hakkinsa. Wa ye makusanci wanda All..yake nufi a wannan ayar? Kuma menen hakkinsa wanda All..T yace a bashi?
A cikin wasu wurare a shirye-shiryemmu da suka gabata, mun bayyana cewa, makusanta a cikin ayar -Mawaddah- sune Iyalan gidan manzon All..(s) makusantan manzon All..(s) kuma sune Fatimah, Ali, Alhassan da Alhussain (a). Don haka ma’anar ka bawa ma’abucin kusanci hakkinsa, shi ne ka bawa wadannan hakkinsu.
An karbo hadisi daga Abi sa’idinil Khuduri da waninsa kan cewa a lokacinda wannan ayar ta sauka ga manzon All..(s) ya bawa Fatima (diyarsa(s) gonar Fadak ya kuma mika mata ita.
Haka ma an ruwaito wannan hadisi daga Imam Albakir (a) da kuma Imam Sadik (s). Banda haka hadisin mashahuri ne a cikin malaman shi’a. Sannan malaman Ahlussu sunna da dama sun ruwaito shi ta hanyoyi da dama, daga cikinsu akwai Kanzul Ummal, a cikin Mukhtasar dinsa wanda aka yi rubutu a hamishinsa, da kuma Musnad na Ahmad dan Hambal a lokacinda yake magana dangane da ‘sada zumunta’ a cikin Babin (Alkhlaq) daga Abi sa’idil-khuduri yace: a lokacinta ta sauka -wato ayar zal-Kurba) hakika manzon All..(s) ya ce wa -diyarsa Fatimah (s) gonar fadak taki ce.
Sannan yace: Al-Haakim Nishaburi ya kawo cikin tarihinsa. Haka ma ya zo a cikin Durrul Manthur na Suyudi a shafi na 177, ya ce Bazzaaz da Abu Yaala da dan Abi Hatam da dan Mardwee daga Abi Sa’idinil Khuduri yace: A lokacin da wannan Ayar ta sauka, -Ka bawa ma’abucib kusanci hakkinsa- sai manzon All..(s) ya bawa Fatimah (s) Gonar Fadak.
Ibn Abil Hadid Al-Mutazili ya kawo cikin Nahjul Balaga, ya kuma nakalto daga hanyoyi da dama, banda ta Abu Sa’idinil-khuduri yana cewa. Lalle a lokacinda wannan Ayar ta sauka -Ka bawa ma’abucin kusanci hakkinsa- manzon All..(s) ya kira Fatimah (s) ya bata Fadak.
Amma da farko (01)-me mecece gonar Fadak?
02-Shin gonar Fadak ta manzon All..(s) ne ko ta musulmi gaba dayansu ?
03-Shin manzon All..(s) ya bawa Fatimah (s) Fadak Kyauta a rayuwarsa ne ko ba haka ba?
04-Shin ana gadon manzon All..(s) ko kuma ba haka ba?
05-Shin Fatima (s) ta kasance tana amfana da gonar Fadak a rayuwar manzon All..(s) ne ko ba haka ba.?
Amma amsar tambaya ta farko shi ne. Fadak wata gone ce ta yahudawan Fadak, a lokacinda suka ga irin nasarar da manzon All..(s) ya samu a kan ganuwowin yahudawan Khaibara, sanan ya yi kofar rago da uku daga cikinsu, amma suka nemi sulhuntawa da shi, sai suma (wato yahudawan Fadak) suka Aikawa manzon All..(s) sakon neman sulhuntawa da su sai ya amince. Sai suka bashi gonar Fadak don ya barsu a kan addininsu. Sai ya ce ya amince.
Don haka gonar Fadaka mallakin manzon All..(s) ne, kamar yadda ya zo cikin aya ta 6-7 a cikin suratul Hashr (59) inda All..T yake cewa:
{Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga Manzon Sa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da Manzannin Sa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.} *
{Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa daga mutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa, da kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya (matafiyi) ne, dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku, kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku karbe shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah, da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.} Suratu Hashar 59.
A cikin wadannan ayayoyi biyu, ma’anar (Afa’allahu) wato All..T ya mayarwa manzon All..(s) daga hannun yahudawa. A cikin wannan ayar yana cewa, duk abinda musulmi suka samu na ganima, ba tare da sun yi amfani da makamansu da kuma da dawakansu ba, to rabon All..T ne da manzonsa (s) da makusanta da marayu da talakawa da matafiya wadanda guzurinsu ya kare.
Don haka a lokacinda aka bawa manzon All..(s) Fadak, sahabban manzon All..(s) su na ta magana a tsakaninsu, ko zai raba masu,? Sai All..ya saukar da wannan ayar wacce ta mallakarwa manzon All..(s) a kebe irin wannan ganiwar. Wannan ita ce amsar tambaya ta biyu.
Amma ta uku, kun ji yadda manzon All..(s) ya bawa Fadimah (s) diyarsa gonar Fadak bayan saukar ayar –Ka bawa ma’abucin kusanci hakkinsa).
A wani hidisi wanda Ibn Hajar Al-Askalan ya fitar a cikin Sawa’iqul Muhrika, ya ce Umar yace: Lalle zan fada maku dangane da wannan al-amarin, Lalle All.. ya kebe manzonsa (s) da wannan dukiyar, bai bawa wani ba, wannan hakkin sa ne a kebe….kamar yadda ya zo cikin aya ta 6 a cikin suratul Hashar.
Don haka atakaice, Fadak gona ce, wacce ta kasance mallakin manzon All..(s) ne, sannan tare da umurnin All..T ya bawa diyarsa Fatimah (s), kyauta a rayuwarsa. Kuma Fatimah (s) ta amfana da albarkar wannan gonar a rayuwar manzon All..(s) kamara yadda zamu gani a cikin shirimmu na gaba, idan All..ya kaimu.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kai mu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.