Kissoshin rayuwa Sirar Fatima Azzahra 66

KAssalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahad Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai cikin wasu littafan.  Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, mun yi maganar yadda Fatima (s) ta yi mafarki da mahafinta manzon All..(s) sannan ya fada mata cewa yana shaukin ganinta, sai ta amsa masa cewa, ita ta fi shukin son ganinsa. Daga karshe ya fada mata cewa. Zata hadu da shi a wannan daren.
A lokacinda ta farka sai ta sai taji dadi, sannan ta tashi daga shimfidarta ta kuma fara tunanin abinda ya zama wajibi ta yi a cikin yan sa’o’in da suka rage mata. Daga nan sai ta tashi ta je inda suke ajiye ruwa a cikin gidan, ta fara wanke tufafin yayanta, bayan haka sai ta fara wanke kan yayanta. A cikin wannan halin ne sai Amirul muminina (a) ya shiga wajenta, sai ya ganta tana aikin gida, sai ya fara tunani me ya fidda ita daga kan gadonta, sai ya tambayeta abinda ya fidda ita, daga inda take, sai ta fada masa cewa yau ne ranarta ta karshe a nan duniya, sai ya tambayeta inda ta sami labarin hakan, sai ta fada masa mafarkin da ta yi.
Daga nan Zahra(s) ta fara tunanin wasiyoyinta, ga mijinta. Lokaci yayi da zata bayyana masa, abinda ta boye a cikin zuciyarta, na wasiyarta, don ya aiwatar da su ko menen hakan zai kasance.
Don haka a lokacinda ta kammala ayyukanta na cikin gida, sai ta koma kan gadonta, ta fara Magana da mijinta Amirul muminina, ta ce masa: Ya dan ammina, hakika an bani labarin wafatina, kuma ina ganin ba abinda ya rage, zan hadu da mahaifi na, a cikin yan sa’o’i masu zuwa, ina son in yi wasiyya da wasu abubuwa da suke cikin zuciyata. Sai Imam Ali(a) yace mata, ki yi mani wasiyyar duk abinda kika ga dama, ya diyar manzon All..(s). Sai ya zauna a kusa da kanta, sannan yace wa duk wadanda suke cikin dakin su fita.
Sai ta ci gaba da cewa: Ya dan ammina, baka taba sani na da karya ba,  ko kuma kha’inci b, kuma ban taba saba maka tun da na hadu da kai ba. Sai Ali (a) yace: All..ya kiyaye! Kina daga cikin wadanda suka fi sannin All.., suka fi biyayya gareshi da tsoronsa, har’ila yau da kuma girma a wajensa. Kina cikin masu tsoron All..wadanda suka fi karfin in ce kin saba mani. Kuma hakika ina jin zafin rabuwa da ke da kuma nisantarki. Sai dai ita rabuwa, al-amari ne ba makawa daga gareshi.
Kuma wallahi, kin sabonta musibar wafatin manzon All..(s) gareni, hakika wafatinki da rashinki ya girma a cikin zuciyata, “In lillahi wa inna Ilaihi Raji’un”. Musiba, mai girma, kuma mai tsananin zafi, wacce ta fi bacin rai zafi.
Sannan suka yi koka gaba daya, sai Imam Ali (a) ya dauki kanta ya ajiye a kan kirjinsa, sai ya ce: Ki fada mani duk wasiyyan da kike so, da yardar All..zaki sameni mai cika alkawari, kuma mai aiwatar da duk abinda kika umurceni gaba daya
Sai tace: All..ya saka maka, da mafi alkhairin sakamako. Ya dan ammina, ina maka wasiya da farko, ka auri diyar kanuwata Umamah a bayana, don zata kasance ga yayana kamai ni, don lalle mazane ba makawa sai sun yi aure.
Ina maka wasiyya kan kada ka bar ko da daya daga cikin wadanda suka zalunceni su halarci jana’iza ta.
Ya dan ammina! Na san cewa ba zaka iya zama ba tare da aure a bayana ba, idan ka yi aure ka sanyawa matar yini da dare, sannan ka sanyawa yaya na yini da dare.
Ya baban Hassan! kada ka juya masu fuska, sai su zama, marayu, baki, wadanda aka karyawa zuciya, don sun rasa kakansu a jiya, sannan gashi a yau kuma zasu rasa mahaifiyarsu, wuta ta tabbata ga wadanda zasu kasasu, ko kuma su fusatasu. Sai ta rera kasida inda a cikinta take makokin kanta da kuma na yayanta.
An karbo hadisi daga Imam Aliyu Zainul Abidina (a) ya na cewa: Lalle Fatimah (s) a lokacinda take son yiwa Amirulmuminina(a) wasiyya, tace masa: Ya baban Hassan: Lalle manzon All..(s) ya yi mani alkawari, ya kuma fada mani cewa, nine na farko daga cikin iyalan gidansa wanda zai sadu da shi, babu makawa daga abinda ya zama dole. Ka yi hakuri da al-amarin All..ka yarda hukuncinsa.
An karbo hadisi daga Imam Sadik (a): A lokacinda mutuwa ta zowa fatimatu (s) sai ta yi kuka, sai amirulmuminina (a) ya ce, mata: Ya shugaba na, me yasa kike kuka? Sai tace: Ina kukan abinda zaka gamu da shi a bayan na. Sai yace mata: Kada kiyi kuka, na rantse da All..lalle wancan kadan ne a wajena, da zatin All…”. A wani hadisin tace wa Amirulmuminin(a): Ya baban Hassan! ina da wata bukata a wajenka, sai yace: Za’a aiwatar da ita a yake, ya diyar manzon All.., Sai tace: Na hadaka da All…da hakkin manzon All…(s) ka da ka Abubakar da Umar su yi mani salla.
A wani hadisin daga Aliyu dan Abitalib (a) yana cewa: Fatimah (s) ta yi mani wasiyya, ta ce: Idan sun yi mani sallah zai kai kararka a wajen babana, kamar yadda zan kai kararsu a gaban shi.
Wannan kadan kenan daga wasiyoyin Zahra (s), wadanda suke nuna Iran wahalan da ta sha a hannun wasu daga cikin shuwagabannin da suka kwace iko daga hannun iyalan gidan manzon All..(s) bayan wafatinsa. Har’ila yau suna nuna irin yadda take kyamar wasu daga cikinsu, ha ya kai ga bata son su zo kusa da ita, tana rai har ko kuma bayan wafatinta. Ta kai matsayinda ta bukaci a boye inda kabarinta yake, don kada, ko da bayan wafatinta su zo kan kabarinta.
Da wannan dalilin ne kuma har zuwa yau, ba wanda ya san inda kabarin Fatima (s) yake a Madina, don wannan ya zama hujja, kuma shaida kan irin wahalarda ta sha a hannun wasu daga cikin sahabban manzon All..(s)  bayan wafatinsa.
Wannan duk tare da cewa ya fada masu tun yana da rai, kan cewa yardarta yardarsa ne, fushinta fushinsa ne, fushinsa fushin All.., sun san da haka sun kuma tabbar da hakan a gaban jami’a, amma kuma wannan bai hana su cutar da ita ba, sun kwace hakkinta, wanda ya zo a cikin Alkur’ani mai girma.
Banda haka ta yi wasiyya kan a binne gawarta mai tsarki a cikin dare, don kada wani ya gani ya je ya fadawa makiyanta su zo kanta. Sannan ta kebance khalifofi biyu na farko, a wannan al-amarin saboda yadda suka jagoranci cutar da aka yi mata, kuma su ne gaba da gaba a hakan, manzon All..ya fada masu matsayinta amma suka saba masa.
Sannan ta bukaci Asma’u diyar Umais (a) matar khalifa na farko, ta je wani wuri a cikin dakin ko gidan ta kawo mata abinda ake kira ‘Khanud’, wato magariya da kafur wato ragowar wanda aka yiwa manzon All.. Khanud da shi.
A lokacinda ta kawo sai tace a ajiye shi kusa da kanta.  An ruwaito hadisi daga Imam Ali(a) yana cewa: Yana daga cikin wasiyata, a bani ‘Khanud’ (wato magariya da kafur). Manzon All..(s) ya kirani kafin wafatinsa da kadan, sai yace: Ya Aliyu! Ya Fatimah ! Wannan ‘khanud’ na aljanna ne, wanda mala’ika Jibirilu ya bani, yana kuma sallama a gareku, sanna yana fada maku cewa: ku raba shi, sannan ku ware nawa da naku, Sai Fatima (s) tace: Ya babana, kada da thuluthi, 1/3. Sa.  Sannan ya kasance, mai kula da sauran shi ne Aliyu dan Abitalib (a).
Sai manzon All..(s) ya yi kuka, sai ya rungumeta, sai yace: All..yayi maki muwafaka, ya shiryar da ke, ya saki a hanya, ya kuma yi maki ilhami. Sai Yace: Ya Aliyu! Ka yi Magana dangane da sauran.  Sai yace: Rabin wanda ya rage na ta, sannan sauran rabin kuma duk wanda ka ga dama ya manzon All..(s). Sai manzon All..(s) yace, Nake ne. A cikin wannan halin ne sai Zahra(s) ta kira, Salma matar Abu Rafiu, maulan manzon All..(s): Ta ce mata, ki hada mani Ruwan wanka. Sai tace a kawo mata sabbin kayakinta, ta yi wanka sannan ta sanyasu, sannan tace a yi mata shinfida a tsakiyar gida.
Wasu suna cewa: ta yi wanka ne, irin wankan mamaci, don bata bukatar wanka bayan wafatinta. To amma wannan ba gaskiya ne ba, don ana wankan mamata ne bayan mutuwarsu ba kafin mutuwa ba. Wadanda suke wankan mutuwa kafin mutuwarsu sune, wadanda aka yankewa hukuncin kisasi, wato za’a kashesu. Amma al-amarin Zahra (s) ba haka bane. Don haka bamu san dalilin da ya sa ta yi wanka jim kadan kafin wafatinta ba. Mai yuwa don ta wanke wuraren da aka ji mata ciwo a kwanakin da aka shiga gidanta da karfi. Mai yuwa kuma tana son ta boye su daga wadanda zasu yi mata wanka. Tabbas Aliyu dan Abitalib (a) shi ne mijinta, kuma shi ne yayi mata wanka bayan wafatinta(s).
To masu sauraro a  nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum warahamatullahi wa barakatuhu.issoshin rayuwa 66
Download

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments