Kissoshin Rayuwa Imam Hassan (a)

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahida Murtdha Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na Maulana Jalaluddin Rumi. Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu. A cikin shirimmu nay au.

///…Masu sauraro, a cikin shirimmu na yau zamu fara kawo maku, sirar Abu Mohammad Imam Hassan dan Aliyu da abitalib kuma jikan manzon All..(s) na farko daga diyara Fatima (s).

Shi ne jika na farko wato  “sibdu” , wanda hasken wasiyanci ya hadu da hasken annabci daga diyarsa Fatimah (s). mai yawan hakuri a duk tsawon rayuwarsa, malaman tarihi sun gamu a kan cewa shi mai yawan hakuri ne, bai taba sakawa wani wanda ya munana masa da mummuna ba. Haka ma taba sakawa mai zunubi da zunubinsa ba.

Mahaifisa Fatima (s) tana karkashin kula na mahaifinta manzon All..(s) sannan ya shayar da ita ilmi da hikima da kuma tarbiyyan da ya samu daga All.. da kuma mala’ika Jibirilu wanda yake yawan ziyartar gidansu. Fatimah (s). don haka ko da Fatima (s) mahaifiyar Alhassan (s) ta bude midonta ta sami cewa gidan mahaifinta gidan annaci ne, gida ne wandamala’iku suke zuwa.

Don haka ta tashi a gidan da ba’a sabo, babu abinda yake cikin gidan sai Alkhairi, don haka ta sami tarbiyya wanda babu wanda ya sami irinsa sai mijinta kamar yadda zamu gani. Don haka ta tashi da zuciya mai tsabta da tsarki, duk wani abu na dauka da datti baya kusantar gidansu.

A lokacinda mahaifinta manzon All..(s) ya yi hijira zuwa Madina, ya tafi tare da ita, ya ci gaba da tarbiyyanta, don ta zama mahaifi mafi albarki a cikin mata, don itace zata haifi hujjojin All…a bayan kasa, da farkon shi Imam Hassan (a) da kuma dan uwansa Imam Hussain (a) daga nan sai sauran hujjojojin All..daya bayan daya har sai sun cika 11 kamar yadda All..ya so.

Don haka a lokacinda ta kai, aure wadansu sahabban manzon All…(s) suna tsammanin su kyfu;inta na, sai suka agabatarda kansunms gsbsns msnxon All..(s), amma sai yana maida su. Yakan fada masu al-amarin aurenta yana hannun All…

Amma alokacinda kufu’inta ya gabato wato Aliyu dan Abitalib (a), sai manzon All..Ya ce mata Yak e Fatimah, na roki All…ya aura maki, mafi soyuwar halittun All..a bayan kasa, ga Aliyu nan wanda kika sani ya zo yana neman aurenta,  sai ta yi shiru, wanda ta nuna amincewarta da yardarta.

Amma Aliyu dan Abitalib, sun tashi a gida guda, sai dai kawai ya rikata zuwa duniya, don shi a gidan annanbcin ya giram har yaya wayo. Ka sance baya rabudawa da manzon All..(s) don bayan yaye shi. Yana nuna masa halaye masu kyau da kima sanar da shi ilmin annabci. Don haka ya tashi da tsarkinsa, kuma a gabansa aka haifi matarsa Zahra(s). don haka tafi kowa saninsa.

A wani hadisan an ji manzon All..(s) yana cewa: ba don Aliyu ne da zahra’u (s) bata da kufu’I wato wanda zai aureta a bayan kasa. Saboda masumiyya bata aure sai masumi irinta. Amma ma’asumi na maji, yana iya uren wacce ba ma;asumiya ba, saboda maza su ne ake bi.  

Don haka bayan Aure sakamakon auren shi ne haihuwar da mai Albarki, jika na farko ga manzon All..(s) sannan hujjar All..a bayan kasa. Wanda kuma shi ne muke son mu ji sirar rayuwarsa, tun daga haihuwa zuwa shahadarsa, wadanda yake cike ta manya-manyan al-amura a tarihin musulunci.

Don haka aka yi aurensu a shekara ta 2 bayan hijira, kuma kafin shekara guda ta  a ranar 15 ga watan Ramadan shekara ta 3 bayan hijira aka haife shi. A lokacinda Fatimah (s) ta haifeshi. Ta kawoshi ga mahaifinta ta ce masa ka yi masa suna, sai amsa da da cewa ba zai rika manzon All..rada masa suna ba/ Sannan a lokacinda manzon All..(s) ya shigo gidan kuma ya karbeshi ya gani, sai yace wa mahaifinsa, ka sanya masa suna? Sai yace ba zan rikaka bay a manzon All..(s). sai shima yashe b azan rika Ubangina rada masa suna ba. Sai ga mala’ika Jibirilu ya sauko yana cesa ka sanya masa suna, da sunan yayan Haruna wizirin Musa.  Shibar da Shubai, saboda mahaifinsa kamar yadda Haruna yake a wajen musa ne, sai yace masa ni balarabe ne.

Sai yace ka sa masa suna Hassan. Sai yasa masa suna Alhassan. Ya nade shi farin kyalle, sannan ya yi kiran salla, a kunnensa na dama sannan yayi ikama ta kunnensa na hagu. A lokacinda ya cika mako guda a duniya ya aske masa gashin kansa sannan ya yanka masa raguna biyu a rana ta 7 da haihuwarsa.

Manzon All…(s) yayi mutukar farainciki da haihuwar Imam Hassan, saboda shi ne dan Fatimah na farko, kuma shi ne wanda yake dauke da hasken annabci da kuma walaya na farko, shi ne jikansa ta wajen Fatimah (s) na farko.

Banda haki shi ne hujjar All..na farko bayan babansa Aliyu dan Abitalib(s). ko kuma mu ce shi ne wasiyyin manzon All..na farko daga cikin jikokinsa, wadanda All..T ya yiwa alkawali sune fitillo masu hasakakawa al-ummarsa hanya idan sun yarda suka yi biyayya a gareshi.

Da al-ummar kakanksa sun bashi dama ya jagoranci wannan al-ummar bayan shahadar Mahaifinsa, da All..ya ciyar da su ta sama da kasa ko ta karkashin kafafuwansu. Duk haka suke, da shi da babansa da kaninsa da jikokin kaninsa 12, da wannan al-ummar ba ta su damar jagoranci da sun ji dadi a duniya sannan mafi yawansu zasu shiga aljanna.

Amma babu wanda suka bawa damad aga cikinsu saibabansa, shi ma na shekaru 4 da watani. Kuma ta ga yadda ya kyautata rayuwarsu a cikin wadannan shekaru 4, amma basu bawa Imam Hassan bas ai watanni kimani 6 bayan shahadar mahaifinsa..

Manzon All..(s) yayi farinciki da haihuwar Imam Alhassan (s), amma kuma a lokaci guda ya san cewa zai mutu shahidi a hannun ashararan mutane a bayansa. Don haka tun bayan haihuwarsa, yana bayyana masu darajarsa, kamar  inda yake fada dangane da shi da kuma dan uwanda Imam Alhussain, su ne shuwagabannin samarin Aljanna. Su ne jin dadin idonsa. Wata rana yana .

Sai dai Imam Hassan da sauran wasiyyan manzon All..(s), duk matakin da daya daga cikinsu ya dauka to sauran ne aka Sanya a matsayin sauran ba zasu sauya matakin da ya dauka ba.

Don haka sulhun da Imam Hassan (s) yayi da Mu’awiya dan Abisufyan, shi ne ya kare addinin musulunci dafa bacewa, don abinda zai kubutar da musulci da kuma wadanda suke rike da gaskeya a lokacin shi ne sulhuntawa.

Kuma da Imam Hussain (s) shahida Karba ne, yake matsayin yayansa Imam Hassan da matsayi guda zai dauka na sulhuntawa da Mu’awaya dan abi Sufyan. Haka ma da Imam Hassan ne ya zo a zamanin Imam Hussain (a) ba abinda za iyi sai yakarYazid dan Mu’awiya. Don kubutar addinin yana a cikin bada jininsu don kare shi.

Har’ila yau zamu jiyadda Imam Ali(a) yake girmama yayansa Imam Hassan da Imam Hussain (a), don haka zamu ga rawar da Imam Hassan ya taka a rayuwa tare da mahaifin a cikin shekaru 25 na zamanin khalifofin da suka gabace shi. Sannan da kuma irin yadda yake rayuwa da su a cikin shekaru 4dayan watanni da yake rikeda khalifancin musulmi.

Sannan rayuwarImam Hassan (a) bayan shahadar mahaifinsa da kuma yadda ya jagoranci al-ummarmusulmi wadanda suke karkashinta na watanni 6 bayana shahadar mahaifinsa. Sannan rayuwarsa bayan yayi sulhu da mu’awiya dan abisufyan. Da yawan ilminsa da hakurinda da wasu halayensa masu kyau. Sannan zamu ji yadda ya aure wacce zata kashe daga baya, Jadata diyar kais kindi. Da kuma yadda ta kashe shi (s) .

Rayuwar ma’asumai (s) yana ciki da darussa, don haka zamu duba mu ga irin darussan da zamu iya dauka a cikin rayuwar Imam Alhassan (a). Kuma suna da yawa.

Wani abu mai muhimmanci a rayuwar Imam Hassan da Imam Hussain (a) shi ne cewa zuriiyarsu ne kawai suka rayu a cikin daga cikin zurriyar manzon All..(s). wato daga garesu ne All..ya fitar da Alkhairi da yawa wanda ya fada a cikin suratul Khauthar. Sai dai limami masu tsarkisun takaita a cikin zuriyyar Hussain (a) ta baza. Amma a bangaren mata zuriyyarsu guda biyu sun hadu a wajen sauran limamai da suka zo bayansu(s).    

Sannan daga karshe zamu ji yadda wasu musulmi suka nasabta kiyayya ga iyalan gidan manzon All..(s) duk tare da ayoyin alkur’ani mai girma masu yawa da suka sauka wadanda suka wajabata sonsu. Banda hadisan manzon All..(s) wadanda suka zo cikin wajabcin sonsu, da kuma yadda shiriyar al-ummar musulmi zai samu ne kawai tare da biyayya garesu.

Zamu kammala shirimmu na yau da hadisin manzon All..(s) inda yake cewa : Musulci ba zai gushe ba yana da daukaka har zuwa khalifofi 12.. har zuwa karshen }. Idan mun dubi wannan hadisain wanda iangantacce ne, kuma sun zo a cikin littafai masu muhimmanci a bangarorin biyu.

Mu dubi wannan hadisin sannan mu dubbi yadda musulunci da musulmi suka kaskanta, me yasa al-ummar Falasdinu Musulmu suka kasance kaskantattu a gaban yahudawa suna kashe su kamar kisan kaji? Shin da gaskiya mun bayyana wadannan shuwagabanni 12? Wanda Imam Alhassan yana daga cikinsu. ?

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu  a yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barkatuhu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments