Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da war haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane rastan na Aya. Shahida Murtada Muttahari, ko cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin romi. Ko kuma cikin wasu littafan. Da fatan masu saurarozasu kasan ce tare da mu.
///..Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a shikin shirimmu da ya gabata, mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Hassan (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga cikin jikokon manzon All..(s), dagadiyar Fatimah diyar manzon All..(s).
A cikin shirimmu da ya gabata mun yi Magana, kan irin yadda manzon All..(s) yake son Imam Hassan da kuma kaninsa Imam Hussain (a). Ya kuma bayyana cewa sonsu, sonsa ne, sonsa son All..ne sannan son All..zai kai mutane ga Aljanna. Haka ma kinsu kinsa ne, kinsa kuma kin All..ne wanda yake kin All..kuma za isa shi a wuta.
Sannan mun ji irin baiwar da All..yayiwa Imam Hassan (a), na haddace duk abinda yaji wajen kakansa manzon All..(s), sannan jikansa yakan yi karkarwa, idan ya karanta wasu ayoyin Alkur’ani mai girma. Wannan ya nuna cewa ba karatun ne kawai ya haddace ba, sai dai yana fahintar ma’anoni a ayoyin Alkur’ani mai girma, musamman wadanda kakansa ya yi bayayi a kansu.
Banda haka ya fadawa mahaifiyar kan cewa akwai wanda yake kula da shi, wanda kuma alamace wacce take nuna yadda All..yakan aiko da mala’ikunsa su kula da shi su kuma sa shi a hanya a ko wani lokaci. Kamar dai yadda ya faru da manzon All..(s) kamar yadda yazo a cikin wata Khuduba ta Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a)..
Inda yake cewa mazon All..(s) (…All..ya hada shi da babban mala’ika da cikin mala’ikunsa yana nuna masa abinda yakamta yayi da kuma halaye masu kyau… tun baayan an yaye shi..) .wato tun lokacinda yake wajen Halima Assadiyya.
Sannan malaman sunna da shi’a sun ruwaito hadisai da dama a wajen Imam Alhassan (a) wadanda suka shafi ibadu ko fikihu.
Littafin All..mai girma yayi magana mai yawa dangane da iyalan gidan manzon All..Sannan manzon All..(s) ya hadasu da alkur’ani mai girma tare da hukuncin da littafin All..yayi na girmansu da daukakans, da farko littafin All..T ya wajabtawa al-ummansa sonsu, da biyayya a garesu. Ga wasu ayoyin Alkur’ani da suka zo dangane da su, wadanda suke nuna girman darajarsu.
Kafin haka, wasu malamai sun bayyana cewa ayoyin alkur’ani wadanda suka sauka don nuna girma da matsayin iyalan gidan manzon All…(s) daga cikinsu har da Imam Alhassan dan Aliyu dan Abitalib (s), suna da yawa.
01-Ayar so da biyayya inda All..T yake cewa
{Kace: Ban tambayeku wata lada ba, saboda shi (musulunci da na kawo) sai so da biyayya ga makusanta na} Shoora 23.
An karbo hadisi daga dan Abbas, kan cewa a lokacinda wannan ayar ta sauka, sai wasu musulmi suka tambaye shi, suka ce: Ya manzon All..(s) su waye ne daga cikin danginka wadanda aka wajabta mana biyayya garesu?. Sai ya ce (s): Aliyu, da Fatimah da yayansu biyu wato (Alhassan da Alhussain (a). Tafsir Fakhrur Razi 7/406.
Abu Na’im ya ruwaito hadisi daga Jabir dan Abdullahil Ansaria: ya ce: Wani balarabe ya zo wajen Annabi (s), sai yace: Ya Mohammad(s), ka bayyana mani menene addinin musulunci. Sai yace (s): Ka shaida babu abin bauta da gaskiya sai All.., shi kadai bai da abokin tarayya, da kuma muhammadu bawansa ne manzonsa. Sai yace: Kana bukatar wata lada a wajena, ? sai yace(s): Babu, sai son dangi na kusa,. Sai yace: Danginka ko dangi na ? sai yace(s): Makusanta na. Sai yace: Kawo hannunka in maka bai’a, All..ya la’ani wanda baya sonka, kuma baya son dinginka na kusa. Sai manzon All..(s) yace: Ameen.
Sannan Imam Hassan (s) ya fito da wannan a cikin wasu daga cikin khudubobinsa kan cewa yana daga cikin dangin manzon All..(s) wadanda biyayya da sonsu wajibi ne, inda yake cewa(a): Kuma ni ina daga cikin iyalan gidan manzon All..(s) wadanda All..ya wajabtawa dukkan musulmi sonsu, All..tabaraka wa Ta’ala yana cewa
{Ka ce: “Bã ni tambayar ku wata lada a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta.” Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya.} Shuraa 23.
Hakim Nishaburi ya kawo wannan hadisin a cikin Mustadrak ninsa, 3/172.
Hakama, Imam Shafi’i shugaban mazhabara shafi’iyya, yana fada a wata kisidarsa, dangane da wannan ma’anar.
Ya Ahlubaitin manzon All..Sonku = Farilla ne, daga All..ya sauko da shi cikin Alkur’ani.
Kamar mai sawaikul Muhrikah ya kawo Shafi 88.
Fakhrur Raji ya kara kawowa cikin tafsirinsa kan cewa:
01-Idan wannan ya tabba, wato kan cewa ayar ta sauka kan Fatimah da Aliyu da yayansu biyu, ya zama dole ne, suna da wani karin girma fiye da kowa, kuma hakan yana nuni da wasu abubuwa da dama, daga cikinsu.
01-Ma’anar {Sai dangi na kusa}.. shi ne su iyalan gidan manzon All..(s), kuma sune al-amarinsu yake komawa gare shi, wadanda kuma al-amarinsu yake komawa gareshi, su ne Ahlul baiti, kuma ya tabbata cewa Fatima da Aliyu da Alhassan da Alhusain (a) sun kowa kusanci da manzon All..(s). kuma wannan yana nan kamar Nassi ne tawaturi, (wanda babu wata shakka a cikinsa). Don haka dole ne sune Alulbaiti wadanda ya wajaba sonsu.
02-Mun san cewa manzon All..(s) yana son Fatimah (s), harma yana cewa (Fatimah Tsoka ce daga gareni, abinda zai cutar da ni zai cutar da ita). Har’ila yau ya tabbata kan cewa, manzon All..(s) yana son Aliyu da Fatimah da kuma Alhassan da Alhussaini(a). idan haka ya tabbata to dole ne a kan Al-umma gaba dayanta su so su.
03-Yan addu’a ga iyalan gidan manzon All..(s) wani matsayi ne, don haka sai All..ya sanya wannan addu’ar a karshen Attashahud ko tahiya, wato “All..humma salli Ali Muhamad (s) wa Alii Muhamad (s). wadannan gaba daya suna nuni ne kan cewa sonsu wajibi ne.
Daga nan zamu fahinci cewa so wanda yake tattare da biyayya ga Ahlu-Baitin manzon All..(s) yana daga cikin muhimman wajibobi a Musulunci, kuma yana daga cewa mafi tsarkin farillan addini, saboda a cikinsa akwai ladar isar da manzancin manzon All..(s). Banda haka sadar da zumuncin ne ga manzon All..(s).
Kuma godiya ce a gareshi saboda wahalar da ya sha wajen isar da wannan addinin ga talikai, daga ciki har da kai mai sauraro. Har’ila yau hakkinsa ne ga musulmi su jibinci al-amarin musulmi.
01-Ayar Tsakakewa. Wannan tana daga cikin ayoyin da suka tabbatar da tsarkin iyalan gidan manzon All..(s) daga zunubi, daga kuma aikata ba dai-dai ba. Da wannan ayar kuma suka zama ma’asumai wadanda basa sabon All…T. All..yana cewa:
{…Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa.} Al-Ahzab 33.
Wannan ayar a fili take, tana bayyana isma, ko hanuwa daga aikata zunubi ko laifi.
Kuma duk wanda yake son sanin dalilan hakan zai fahinci yadda All..ta’ala ya kebesu, da kalmar (inna ma), yana daga cikin kalmomi masu karfi wajen kebewa. Don haka All..ya kebe wadanda yake nufi da iradarsa, kan cewa su tsarkakakku ne daga daudar zunubi da kuma sabon sa. Sannan shigar harafin lamu a cikin kalmal “Labari” har’ila yau da kuma maimaita kalmar, “tathira” wannan yana nuni ga kebencewa ta musamman, ga wanda ya san, sana’ar harshen larabaci.
Sannan kowa ya sanin ‘Iradar All..’ mustahili ne ya saba masa. .
A wata ayar yana cewa
{Abin sani da Al-amarinsa, shi ne, idan yana so ya faru, sai ya ce Kasance sai ya kasance}. Da haka kuma muka tabbatar da tsarkin iyalan gidan manzon All..(s) daga aikata ba dai-dai ba ko zunubi.
Amintattun malamai masu ruwaito hadisi, sun hadu a kan cewa, wannan ayar ta sauka dangane da manzon All..(s) da kuma Amirulmuminina (a) da Fatima da kuma Hassan da Hussain (s).. Kuma ba wanda yayi tarayya da su a cikin wannan falalar.
Hakika, Hakim Nishaburi ya ruwaito daga Ummu salma (r ) tana cewa, a daki na wannan ayar ta sauko,
{..Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa}
Ta ce: Manzon All..(s) ya aiko a kira masa Fatima da Aliyu da Hassan da Hussain (s) , sai yace: Ya Ubangiji! Wadannan sune iyalan gida na, sai Ummu salma tace: bana cikin Ahlulbaiti ? sai yace: Lalle kina kan Alkhairi, kuma wadannan sune Ahlubaiti na. Ya Ubangi Alhlubaiti na suka fi cancanta.
A wani hadisin Umma Salma tace: A cikin daki na ne, wannan ayar ta sauka
{..Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa}
A cikin dakin akwai Fatimah Ali da Hassan da Hussain (s) sai manzon All..(s) ya lullubesu da wata borgo tare da shi , sannan yace: Wadannan sune Ahlubaiti na, ka tafiyar da dauda daga garesu, tafiyarwa.
Wani dalilin da yake tabbatarwa wannan ayar ta sauka don su kadai ne, a kebe, shi ne hadisin da Dan Abbas ya ruwaito yana cewa: Na shaida manzon All..(s) ya dauki watanni 9 a jere, yakan zo kofar gidan Aliyu (a) ya na cewa: Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu, Ahlul baiti.
{..Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa} Salla All..ya jikanku, sau biyar a ko wace rana sau biyar.
A wata khudubarsa Imam Hassan (s) yace: Kuma ina daga cikin iyalan gidanda Jibirilu yanzulu alaina, sannan ta tashi daga wajemmu, kuma ina daga cikin Ahlul baiti wadanda All..ya tafiyar da dauka daga garesu ya kuma tsarkakesu tsarkakewa.
Hadisai da dama ingantattu sun zo dangane da hakan, kuma duk wanda ya lura zai fahinci cewa, manzon All..(s) ya yi haka ne, don ya tabbatar da cewa su ake nufi da wannan ayar ba wasu ba.
Su ne aka tsarkaka ba wasunsu ba, matansa basa daga cikin wadanda aka tsarkaka daga zunubi ko aikata laifi kamar yadda wasu suke kokarin nunawa. Tare da kafa hujja da siyakin ayoyin da suka zo kafin da kuma bayan wannan bangare na aya ta 33 a cikin suratul Ahazab.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kai mu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu. =====