Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya.Shahida Muttahari, ko kuma littafin Mathnawi, na maulana Jalaluddin rumi. Ko kuma dai cikin wasu littafan da fatan. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///….Madallaha, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Abu Mohammad AlHassan dan Aliyu dan Abitalib (a), da mukla fara kawo maku. Mun kawo maku yadda haihuwar sa ta kasance a ranar 15 ga watan Ramadan shekara ta 3 bayan hijira. Mun ji yadda manzon All..manzon All..yayi farin ciki da haihuwarsa, sannan Mahaifinsa Imam Ali (s) ya ki ya rada masa sunan kafin manzon All..(s). Sanya haka shi ma manzon All..(s) ya ce ba zai rada masa suna Ubangijinsa ba.
Daga nan ba’a dade ba sai ga mala’ika jibriru ya sauko tare da umurnin All… T ya taya murnan haihuwar da aka yimasa, ya ce a sanya masa suna Alhassan, wanda ya kasance suna ne daga cikin sunayen ‘ya’yan Annabi Harun(s) yayan annabi Musa (a).
Har’ila yau mun bayyana cewa Imam Hassan Almujtaba (a) shi ne jikan manzon All..(s) na farko daga Fatimah(s), sannan malaman tarihi sun bayyana cewa manzon All..(s) ya yi kiran sallah a kunnensa na dama sannan ya yi Ikaamaa a kunnensa na hagu, sannan ya yanka masa raguna biyu a ranar 7 da haihuwarsa.
Har’ila yau ya bada sadaga gwagwadon nauyin gashinsa da aka aske masa kansa, sannan bayyana cewa, shi ne na farko daga cikin jikokin manzon All..(s) daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidansa.(s).
Amma a cikin shirummu na yau zamu fara magana danagne da rayuwarsa(s) tare da kakansa manzon All..(s) wanda ya kasance na tsawon shekaru 7 daga lokacin haihuwarsa (s).
Da yardar All..a cikin shirye-shiryemmu na gaba, zasu fara maganar rayuwarsa(s) da kakansa manzon All..(s) da mahaifayarsu na tsawon shekaru 7, sai yan watanni da suka rayu tare da mahaifiyarsu, amma abubuwa da dama sun auku a wannan dan karamin lokacin da ta rayu bayan manzon All…(s). inda aka karkatar da addinin musulunci daga yadda manzon All..(s) ya barshi. An zabi wani ba wanda manzon All..(s) ya ayyana a matsayin khalifansa a bayansa ba.
Sannan an wahalar da iyalan gidan manzon All..(s) kan hakan, har sai da suka zama kaskantattu bayan da a lokacin rayuwar Manzon All..su daukakku ne a cikinta.
Da farko ayoyin Alkur’ani mai girma da dama sun sauka dangane da shi Imam Alhassan (a) da kuma iyalan gidan manzon All… (a). Kuma mun kawo mafi yawansu a cikin kissar mahaifiansu Zahra (s) da muka kammala.
Da farko Imam Alhassan ya na daga cikin wadanda aka tsarkaka a Ayatul Tathir (wato aya ta 33, cikin suratu Ahzaba. Inda All..T yake cewa.
{..Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazanta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa.}
Akwai maganganu da dama dangane da ma’anar wannan ayar, shin tana nufin Matan manzon All..(s) kamar yadda sigar ayar tazo ne, wato a tsakiyar ayoyi wadanda suke magana dangane da matan sa(s).?
Ko kuma ayar ta kebe wasu mutanen ne ba matan manzon All..ba? Ko kuma dai matanne har wasu wadanda ba su ba, kamar yadda wasu malaman suka tafi a kai?. Sannan wata tambaya it ace, me yasa wannan aya ta 33 a cikin surar a kuma tsakiyar magana kan matan manzo All..(s) ya canza daga lamirin mata (kunna-kunna) amma a wannan ayar sai ta kuma (kuma -kum)
Amma don amsa wadannan tambayoyi, na farko ayar a karan kanta ta nuna cewa wadanda ake nufi da wannan ayar ta tsarkakewa daga daudar zunubi, maza da mata ne, ko maza zalla, saboda shigar (kum) da ya zo, idan matan manzon All..(s) suna ciki, to hadisan manzon All…(s) ne zasu bayyana haka.
Amma bamu da wani hadis, ko guda ingantacce wanda yake fadar cewa matan manzon All… suna daga cikin wadanda aka tsarkaka daga zunubi.
Sannan babu wata mata daga cikin matan manzon All..(s) wacce tace tana daga cikin wadanda All..ya tsarkakasu daga dauda kamar yadda wannan ayar take fada. Da ayar tana nufinsu da zamu ji daga wajensu. Don haka tunda ba haka ba, basa cikin wadanda ayar nan ta ke nufi.
Na biyu kuma duk da cewa ayar ta zo tsakiyar ayoyi wadanda suke Magana kan matan manzon All..(s), a gaba da bayanta, amma ba ta hada da su ba.
Akwai ayoyi irenta da dama a cikin akur’ani, kamar ayar gado a karshen suratun Nisaa aya ta176.
Sannan ,um sam cewa manzon All..(s) ne yake bayyana wa musulmi ma’anar ko wace aya a cikin alkur’ani mai .
Kuma hadisai wadanda suka kai haddin tawaturi sun tabbatar da cewa a lokacinda wannan ayar ta sauka manzon All..(s) ya tara Ali da Fatima da yayansu Alhassan da Alhussain sannan ya rufesu da burgo yar yamen sannan ya ce: (Ya Ubangiji ! wadannan sune iyalan gidana, ka tarfiyar da dauda daga garesu ka kuma tsarkakesu tsarkakewa….) An ruwaito wannan hadisin da sigoginsa daban daban daga Ummu Salama da A’isha da kuma daga Fatimah diyar manzon All..da wasu da dama.
A hadisan Ummu Salma, bayan taji yayi addu’ar sai taka bugon zata shiga, ya manzon All..ina daga ciknku sai ya hanata shiga, y ace mata kina kan alkhairi.
Sannan abu na ukku shine, wasu daga cikin ayoyin alkur’ani sun fito fili sun bayyana wasu matan manzon All..(s) suna aia aikata laifi. Har sai da All..T ya bukaci su tuba, kamar yadda ya zo a cikin suratut tahrim. Inda yake cewa:
{Kuma a sã’ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: “Wãne ne ya gaya maka wannan?” Ya ce: “Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini.” Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle All… Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã’iku a bãyan wancan, mataimaka ne.} Attahrim 3-4..
Mafi yawan malaman tafsiri sun tafi a kan cewa “ uwayen muminai A’isha da Hafsa ne, ake nufi da wannan ayar. Babu daya daga cikinsu, wacce ta musanta hakan, ko kuma ta ce, tana daga cikin wadanda ayar Tathir take nufi.
Banda haka da Aliyu da Fatimah, da yayanta Alhassan da Alhussai gaba dayansu, sun bayyana cewa wannan ayar su take nufi, ba wani ba. Suna daga cikin wadanda All..ya tsarkaka daga aikata zunubi da kuskure ya kuma tsarkakesu tsarkakewa.
Don hake ne, da wannan tsarkin da suke da shi, shugabancin Al-ummar musulmi bayan kakansu manzon All..(s) ya tabbata da farko ga babansu, sannan garesu. Don babu yadda za’a yi wanda ba ma’sumi ba. Wanda yake kuskure ya jagoranci wadanda basa kuskure.
Dawannan dalilin ne a wani hadisi manzon All..(s) ya fada dangane da Alhassan da Alhussain (s) kan cewa:
[Wadannan limamai ne sun zauna ko sun tashi}.
A wani hadisin yana fada dangane da Alhussain (a) ya na cewa
(Kai limami ne, dan limami, dan uwan limami , kuma mahaifin limamai guda 9).
A nan yana nufin kai Imam Hussain (s) shugabane, kuma dan shugabane wato babansu Imam Ali(a), kuma da’uwan shugaba ne, wato Alhassan (a), sannan Baban limamai guda tara.
Anan yana nufin yayan Alhussain (s) da jikokinsa 9 daya na bin daya, Kuma suna:
Aliyu bin Hussain Zainaul Abidee(a), Muhammad bin Aliyu (a) Wanda akewa lakabi da Bakir, da Jaafaru dan Muhammad (a) wanda akewa lakabi da Sadik (a), sai Musa dan Jaafaru,(a) wanda akewa lakabi da Kazim sai Aliyu dan Musa (a) wanda akewa Lakabi da Ridha, sai Muhammad dan Aliyu (a) wanda akewa lakabi da Jawad, sai Aliyu bin Muhammad (a) wanda ake wa lakabi da Naki, Sannan Hassan dan Ali wanda akewa lakabi da Al-askari, sannan na taransu, kuma nakarshensu Imam Muhammad dan Hassan(a), wanda akewa lakabi da Mahdi.
Kuma shi ne All..T yayiwa alkawali zai cika duniya da adalci bayan cikarta da zalunci, daga cikin yayan Fatimah(s).
Don haka kunga yadda ma’anar wannan hadisin ya fita a fili. Mafi yawan malaman sauran mazhabobi sun yi Imani da Imam Mahdi (a) sai dai, kawai sun yi iamani da cewa zai fito daga cikin yayan Fatima (s).
Sannan shi dimma, za’a haifeshi a karshen zamani daga yayan fadima(s).
Banda wannan manzon All..A wani hadisin ya na fada dangane da Imam Alhassan da Alhussain (a) kan cewa: su ne shuwagabannin samari al-janna. Amma duk da cewa hadisan da suka fadi haka suna da yawa, sai dai, ba zaka ji cikin malamai daga sauran Mazhabobi suna Magana kan cewa suna cikin wadanda aka yi wa bushara da aljanna ba.
Banda wadan nan ayoyi da kuma hadisan manzon All.. da suka fassarasu, akwai wasu ayoyin da dama wadanda suka yi Magana dangane da darajar da All..T yayi masu. Sai dai ba zamu iya kawo su a nan ba.
Daga cikin Ayoyin, akwai ayar Mubahala, a cikin suratun Ma’isa aya ta 20.
{To, wanda ya yi musu da kai a cikinsa, a bãyan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: “Ku zo mu kirãyi, ‘yã’yanmu da ‘yã’yanku da mãtanmu da mãtanku da kanmu da kanku, sa’an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa’an nan kuma mu sanya la’anar, Allah a kan maƙaryata.} Ali-Imrana :20
Sai suratu Hal’ata daga aya ta 5-22, inda a ciki All…Ta’ala ya ambici ni’imomin da yayiwa bayinda nagatattu, annan sune iyalan gidan manzon All.. (s). ya ambaci da dama daga cikin ni’imomin Aaljanna, amma banda mata. Sannan All..T daga karshe ya ce. “kokarinsu ya kasance abin godiya ne”. wato sun sami yardar All..T, kuma sun sami aljannar sa.
A wani hadinsin wanda Allama Mufid ya kawo a cikin littafinsa Al-Irshad yana cewa,
Fatima (s) a cikin rashin lafiyarsa(s) ta karshe, ta dauko Alhassan da Hussain(a), ta je su wajensa, sai ta ce masa: Ya manzon All..!(s), ga yayanka biyu nan, ka gadar da su daga halayenka. Sai ya ce : Ga Hassan na gadar da shi kamanni na da kuma da halayena masu kyau, sannan Alhussain kuma na gadar da shi kyautata da kuma jaruntata.}
An ruwato cewa manzon All..(s) yakan fita da jikansa Imam Alhassan (a) zuwa masallaci ya yi sallah yana kusa da shi: Don haka a wasu lokutan yakan haw kan wuyar manzon All..(s) ya na ta wasansa, sai manzon All..(s) ya tsawaita sujudarsa har sai Imam Hassan(a) ya sauka daga wuyarsa, Sannan ya tashi daha sujada.
Wata rana aka tambaye shi abinda yasa ya tsawaita sujadarsa, sai ya ce: Alhassan ne (s) ya hau kan wuyarsa yana wasa, ni kuma banan son in ynake masa wasansa.
Sai kuma hadisi na gaba: Manzon All..(s) yana cewa: Alhassan da Alhusaini (s) yaya nane, wanda ya so su ya soni, wanda kuma ya so ni All..zai so shi, wanda All..yake sonsa kuwa zai sa shi a Aljanna. Wanda kuma ya ki su, ya ki ne, wanda ya kini yaki All..wanda All…ya ki shi zai shigar da shi wuta.}
Awani hadisin yana cewa: Alhasan da Alhussain shuwagabannin samarin aljannane, amma babansu ya fi su alkhairi.
A wani hadisin an tambayi manzon All..(s) waye daga cikin iyalan gidanka kafi so, sai yace, Alhassan da Alhussain (a). Yakan fadawa Fatimah: Ki kira mani yayana, sai ya sumbancesu ya kuma rungumesu a kirjinsa(s).
Awani hadisin daga Ya’ala dan Murra ya na cewa: wata rana mun fita daga gida tare da manzon All..(s). mun je bakwanta a wani wuri. Muna tafiya sai manzon All..(s) ya ga Hussain (a) yana wasa a kan titi, daga nan sai manzon All..(s) ya zo gaban mutane, ya bude hannayen sa biyu, yana son kama shi, sai yayi ta nan da can, yana kauce masa, duk suna dariya, har daga karshe ya kama shi … sai ya rungumeshi ya sumbance shi, daga nan sai yace:
Husain daga gareni ya ke, ni kuma daga gareshi na ke, All..ya so wanda ya so shi, Alhassan da Alhussain jikoki na ne daga cikin jikoki}.
Masu saurarro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All…ya kaimi. Wasssa