Kissoshin Rayuwa Fatimah Azzahra (s) 78

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo makun kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo makun kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma sikin wasu litafan wadanda suka hada da littafin Datane rastan na Aya. Shaheed Muttahri, ko kuma littafin Mathnawai na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma wasu littafan daban. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.

///.. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun fara kawo maku, takaitaccen sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s), sannan mahaifiyar Alhasan da Alhussain shuwagabannin samanrin Aljanna.

A cikin shirimmu na baya mun tsaya inda muka  takaita magana a kan aurenta da kuma haihuwar Alhassan da Alhussain (s). A yau zamu takaita masu abinda muka yi magana dangane da rayuwarta a cikin gidan mijinta, inda muka bayyana cewa sun amince tare da mijinta Aliyu dan Abitalib (s) kan ncewa duk abinda suke bukata a gidansu daga wajen to shi Aliyu (a) ne yake da alhakkin kawo shi, kama daga abinci ko muce alkama wanda shi ne mafi yawan abincinsu wanda ake bredi da shi, sannan sauran ayyukan cikin gida kuma ita Fatima (s) ce zata kula da su kama daga kula da tsabtar cikin gida da kuma hada abinci.

Mun bayyana cewa ana samun wasu lokuta wadanda basa da abinci a cikin gidan Amma Zahra (s) ba zata fadawa Aliyu(a) ba, sannan a lokacinda ya gano hakan sai yace mata me yasa ba za ki gaya mani ba, sai tace, ai babana yace kada an tambayeka kome. Sai shi kuma yayi shiri.

Don haka shugaban matan duniya da lahira tana girki ta kula kula da tsabtan gida da kuma kula da yayanta a lokaci guda.

Sai kuma matsayinta a wajen Alll..T da kuma falalolinta wadanda ayoyin Alkur;ani suka sauko don haka ko kuma manzon All..(s) ya fada mata ko sahabbansa, ko kuma mijinya.

Daga cikin ayoyi.

01-Ayar tsarkakewa suratul Ahzab aya ta 33. Inda All…yake cewa “All. Kawai yana nufin ya tafiyar da dauda daga gareku ya ku iyalan gida babba, ya kuma tsarkakeku tsarkakewa.} hadisai da dama wadanda suka kai haddin tawaturi sun tabbatar da cewa ma’anar Ahlulbaiti shi ne Manzon All..(s), da Aliyu da Fatimah da kuma Alhassan da Alhussain (s). sune All..ya tafiyar da dauda a gareku ya kuma tsarkake su tsarkakewa.

Wannan tsarkin yana nufin su ma’asumai ne basa sabon All..ba don kome ba sai don su ne hujjojin All..a bayan kasa duk abinda suka yi abinda All..yake so ne. sannan mun fada cewa wannan matsayin ya hada da yayansu 9 daga Imam Hussain(a).

Wasu sune, Aliyu dan Hussan, muhammadu dan Ali, Jaafar dan Muhammad, Musa dan Jaafar, Aliyu dan Musa, Muhammad dan Ali, Aliyu dan Muhammad, Hassan dan Ali da kuma Muhammad dan Hassan, wanda kuma ake kiransa Mahadi (s). sune khalifofin manzon All..tare da nassi daga All..da kuma manzonsa (s).

Banda Haka Zahra (s) tana daga cikin wadanda All..ya daukaka matsayinta ya kuma bayyana girmantya a yar Mubahala, inda Nasaran najran suka zo madina suka yi jayayya da manzon All..(s) kan annabi Isa, All..T ya sauka da ayoyi masu yawa a kan wannan jayayya, amma daga karshe basu amince da zancensa ba, kan cewa annabi Isa (a) bad an All,…bas hi bawan All.. ne wanda All..ya halicceshi kamar yadda ya halicci annabi Adamu, shi Adam(s) baida uba ko uwa, amma annabi Isa (s) yana da mahaifiya amma bai da mahaifi.

A lokacinda suka ki amincewa sai All..T ya sauka da aya ta {Idan Hujjace ka, ka ce masu ku zo mu kira yayammu ku kira yayanku, da matanku da matammu, da kuma kawukammu da kuma kawukanku, sai mu yi tawalu’I ga All..sai mu sanya La’anar All..a kan makaryata}  61-Ali –Imrana.

Sai manzon All..ya fito da Zahra da mijinta da yayanta Alhassan da alhussain (s) don yin la’anenniya da nasaran Najran. A lokacinda Nasaran Najran suka gay a fito da wadanda suka fi soyoyiwa a gareshi, kuma mafi kusa da shi, sai suka tabbatar da cewa idan sun yi Mubahala, ko la’anenniya da shi ta su zasu halaka. Don haka suka fasa yan mubahala da su.

Annan matsayin Zahra (s) a cikin wannan iayar shi ne –Matammu, wannan ya nuna cewa All..T ba zai maida addu’arta ba (s). banda haka wannan ya bayyana irin matsayin da take da shi a wajen All…da ita da yayanta 2 da kuma babanta.

Sai suratu Hal’ata, inda All..T ya girmamasu, ya kuma bayyana matsayinsu a lahari, yayimasu bushara da su tun tana duniya. Wannan kuam kamar yadda yazo a cikin wata ruwaya, Alhassan da Alhusain (s) sun yi rashin lafiya sai Aliyu (s) yayi nazara kan cewa idan sun warke zai yiazumi na kwanaki uku don godiya ga All..T.

Sannan a lokacinda suka warke, sai suka yi azumin gaba dayan gidan, wadanda suka hada da shi Imam Ali(a) da Fatima da kuma yayanta Alhassan da Alhussain da kuma kuyangarsu Faddatu. A daren farko sun zo bada baki wani miski ne ya zo suka bashi dukkan abincinsu, sannan a dare na biyu maraya ya zo suka bashi dukkan abincinsu, sai dare na ukku suka bada abincin buda bakin nasu ga fursinan yaki. Don haka sun jera kwanaki uku basu ci abinci ba sai ruwa.

Bayan da manzon All..(s) ya gansu da kuma yuwanwa da suke ciki sai ya bata ransa, amma sai All..ya faranta masa ciki da saukar suratu Hal’iata, –inda a karshen surar ya kawo nemomin aljanna da dama, amma bai ambaci mata ko kuma hurul’ini a ciki ba. Malamai sun bayyana cewa mai yuwa yayi haka ne, don girmama Zahra (s).

Don haka kunga gaba dayansu Al…T ne ya yi masu bushara da Aljanna.  Don haka Zahra (s) tana daga cikin wadanda All..T yayai mata bushara da Aljanna, amma mun karanta a wani wuri ba wai zata shiga aljanna kadaiba, zata ceci wasu da dama , daga cikin al-ummar Mahaifinta, daga wutan Jahannama, da shigo da su shiga aljanna tare da ita. (s).

Har’ila yau da suratu Kauthar, (wato inna atainakal Kauthar…). Shi wannan ayar ne ake mata lakabi da Kauthar (s).

Saboda sababin saukar wannan ayar shi ne, mushrikammu Makka, suna gori wa Manzon All..(s) kan cewa bai da yayan wadanda zasu gajeshi , don yayansa suna mutuwa tun suna kakana, Qasin, da Abdullahi, duk sun rasu suna kanana. Wannan ya sa suka ce (abtaru ne) wato mai yankekken baya, sai All..ya saukar da surar Alkauthar, wanda yake nufin albarka mai yuwa. Sannan a karshen ayarne zamu fahinci cewa Zahrau Ce ake nufi da Kauthar, don inda All..yake fadar cewa {Lalle makiyinka shi ne mai yankekken baya} wato bai da zaurriya.

Sannan mun san cewa manzon All..(s) bai da zurriya sai ta Fatimah (s). da kuma jikokinsa Al-Hasan da Al-Hussan (s).

Akwai wasu ayoyi da dama wadanda suke magana kan matsayin Zahra (s) a wajen All..T amma zamu takaita da wadannan.

Sai kuma hadisan manzon All..(s) wadanda suka bayyana matsayinta a wajen da kuma babanta. Manzon All..Yana cewa {Fatima tsoka ne daga gareni wanda ya fusatata ya fusata ne,} a wani hadisin (yana cewa Fatima tsoka ne daga gareni wanda ya cutar da ita ya cutar da ni].

A wani Hadisin yana cewa :Fatima ita ce shugaban Matan duniya na farko dana karshe, maryar mahaifiyar annbi Isa shugaban matan zamaninta ne.

A wani hadisin {Hurul inice a shifan mutum}. A wani hadisin yana cewa..idan na yi shaukin kanshin aljanna zai sunsuni wutar Fatimah. Ga wasu hadisai da dama.

Sannan munyi magana dangane da Fatima da matan manzon All..(s), wano lokacin wasu daga cikin matan manzon All..sukan mata mata rai, ko kuma su kaskanta mahaifinta Khadaiza (s) a gabanta su nena mata cewa ai sun fita daraja a wajen manzon All..(s).  sai ta yi kuka da hawayenta, amma manzon All..(s) sai yazo ya shiga tsakaninsu. Ya kuma cewa: All..bai bani mata kamar Hadiza ba, saboda ta yi Imani da ni a lokacinda aka kafice mani, ta bani kudanta a lokacinda kowa ya hana ne, sannan All..ya arzutani da yayanta ya haramta mani yayan sauran matan.

Idan muka yi maagana dangane da yawan iliminta kawo, zamu fahinci cewa ita malamace wacce baka bukatar wani ya sanar da ita, sai babanta. Da kuma ilhamin da take samu daga wajen All..kai tsaya ko wanda mala’iku suke sanar da ita.

Wata rana manzon All..(s) ya tambayi sahabbanta kan cewa me yafi dacewa da mace sai basu sani ba. Sai Imam Ali (s) ya je gida ya tambaye matarsa Zahra (s) sai tace masa: ai kada ta kalli maza kada maza su kalleta.

Ya koma ya fada masa, sau manzon All..(s) yace ita daga gareni take ni ma daga gareta nake.

Matan madina suna zuwa wajenta su tambayeta kan matsaloli na addini ta basu amsa. Hakama tana koyawa yayanta addini, kuma takan karanta littafai ko rubutu. Wata rana daya daga cikin yayanta Alhasan ko Alhusain ya yambayeta, kan cewa me yasa idan tana kunutu tana wa makobta da wasu mutane amma batawa kanta addu’a sai ta masa masa da cewa: Ya dana, makobta sannan gida.

Sai kuma dangane da ibadunta, mun ji yadda idan ta tsaya kan mahrabinta tana Sallah, ko tana ibada mala’iku a sama suna ganinta a matsayin wata tauraruwa a kasa. Wannan yana nuna matsayin da take da shi a wajen Ubangijinta, tana da matsayi babban a wajensa daga cikin bayinsa.

Albarkacinta ne aka samo tasbihatuz Zahra (s) wanda dukka musulmi mai sallah, ya sansu, wato a lokacinda mai sallah ya sallame daga sallar abu na farko da zai yi shi tasbihatus Zahra (s). wanda kuma sune, Allahu Akbar 34, Alhamdu lillahi 33 sannan subahanallahi 33. Kokuma akasin haka a wajen yan uwammu Ahlussuna.

An kawowa manzon All..(s) dukiya daga ciki har da bayi, sai Ali (s) yacewa Zahra ki je wajen babanki ki rokeshi ya baki kuyanga guda ta zo ta taimakeki a ayyukan gida , sai ta je ta same shi yana cikin shugullah da wasu mutane. Sai ta dawo gida. A lokacinda ya kammala ayyukansa sai ya zo gidanta (s) yace mata, kin zo dajun, kinason ki fada mani wani abu, amma kika juya kika dawo gine, me kike su.

Sai ta yi shiru, sai Aliyu (s) ya ce masa: Ay nine nace mata an kawo maka dukiya mai yawa daga ciki har da bayi da kuyanku, ta rokeka guda wacce zata taimaka mata a ayyukan cikin gida. Sai Manzon All..(s) yace masu: Ba zan baku abinda yafi haka ba., sai suka Ee : sai yace ku yi kabbara 34 , hamdaka 33, subhanallah 33 bayan duk wata sallar farilla da suka yi ya fi maku abinda kuka nema.

Har’ila yau munkaranta wasu daga cikin addu’o’inta da ta saba yi, kuma mun bayyana cewa suna da yawa wanda yak e son karin bayani sai dai ya koma manya manyan littafan addu’o’I don ginin abinda zai iya dauka daga cikinsu.

Sannan mun bayyana cewa manzon All..(s) yana sonta sosai, amma son da ya wuce, son mahaifi da diyarsa, so ne wanda yake da dangantaka da matsayinta a wajen All..T, duk da cewa shi ne mahaifinta amma yana girmamata matukar girmamawa. Daga cikin su, idan ta shigo wajenta yakan tashi tsaye yayi maraba da ita ya sumbanci hannunto ko kanta, sannan ya ijiyeta a inda ya tashi.

Ba ya son abinda ya bata mata rai.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau amma, zamu dora daga inda muka tsaya na takaitaccen sirar Zahra (s) da muka kawo maku. Wassalamu aliakum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments