Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawai na maulana jalaluddin Rumi ko kuma dai ciki wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar shuwagabannin samarin Aljanna, Alhassan da Alhussain(a} da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi magana, kan matsayin Zahra(s) a lahira.
Wannan duk tare da cewa wasu musulmi sun wulakantata a duniya, basu kiyayewa manzon All..(s), wasiyansa dangane da ita ba. Basu kuma kiyaye wa All..T matsayin da ya bata a duniya da lahira ba, amma a ranar kiyama, All..T zai bayyana matsayinta, ya kuma bayyana hakinta da daukakar da yayi mata, a cikin al-ummar mahaifinta manzon All..(s).
Daga ciki, mun kawo wasu ayoyin alkur’ani mai girma, wadanda All..T ya sauko da su a cikin alkur’ani mai girma, wadanda su ke bayyana matsayin da take da shi a wajensa. Daga cikin wadannan ayoyi, akwai ‘Ayar tsarkakewa, da ayar mubahala, da ayar wajibcin son makusantan iyalar gisan manzon All..(s). Da suratul Hal’ata, da suratul Kauthar da wasu da dama.
Mun kawo hadisai da dama wadanda suka tabbatar da cewa wadannan ayoyi sun sauka ne don Zahra (s) da mahaifinta da kuma mijinta da yayanta. Ayara tsarkakewa ta wankesu daga yin kuskure ko aikata sabon All…T. Kuma All..baya maida addu’arta, kamar yadda ya faru a ayar Mubahalah, sannan All.. yayi masu Bushara da Aljanna a cikin suratu Hal’ata.
Sai kuma suratu Kauthar wacce take nuna cewa zuriyyar manzon All…(s) ta wajen Zahra (s) ne ne kadai zata wanzu, don haka shi ba mai yankekken baya ne, kamar yadda mushrikan Makka a lokacin suke fata ba. Sai dai All..T ya Sanya zurriyarsa za su cika duniya, ta yayan Zahra (s).
Banda haka mun ji wasu daga cikin hadisai wadanda suka yi Magana dangane da matsayinta a ranar kiyama, sannan da irin ceton da zata samu na kubutar da shi’arta da masoyanta daga wutan jahannama zuwa Aljanna.
Sannan hatta su shi’anta, (s) za su sami damar yin ceto a ranar kiyama.
An karbo hadisi daga dan Abbas, Abdullahi ( r) yace:
Ya ji Amirulmumina Aliyu dan Abitalib (a) yana cewa: wata rana manzon All..(s), ya shiga wajen Fatimah (s) ya sameta cikin bakin ciki, sai yace mata, : Menene bakin cikinki ya diyata?
Sai tace: Ya babana, ranar kyama ce nake tunani, da yadda mutane zasu tsaya tsirara, a rannan.
Sai yace: Ya diyata Lalle rana ce babba. Amma mala’ika Jibril ya fada mani, daga All..mai girma da daukkaka, kan cewa, mutum na farko wanda za’a tsaga masa kasa ya fito shi ne ni, sannan mijinki Aliyu dan Abitalib (s),
Sai All..ya aiki mala’ika Jabra’il, tare da mala’iku dubu 70, su kafa kubbobi guda 7 na haske, a kan kabarinki, sannan mala’ika Israfil, ya zo maki da rigunan guda ukku, sai ya tsaya inda kanki, ya kiraki ya ce: Ya Fatimah diyar Muhammad(s) ki tashi don ranar kiyamah.
Sai ki tashi ki na cikin nishadi da aminci, babu tsoro, sanna za ki tashi a suturce, sannan Israfil ya mika maki kayan kawarki ki sanya su.
Sai mala’ika Rufa’il ya zo maki, da zabebben abin hawa ko doki wanda aka halicceshi daga haske, an yi masa linzami da danyen lulu’i. Tare da wurin zama a kanta, daga zinari, sai ki hau dabban, sai mala’iki Rufa’il ya ja ragamarta. A gabanki akwai mala’iku 70,000 suna rike da tutocin tasbihi,
Sannan idon kin fara tafiya, zaki hadu da hurar’in 70,000, wadanda zasu kasance tare da ke, suna jin dadi da kallonki. Ko wannensu tana rike da kaskon turare, suna watsa turare ba tare da an sa musu wuta ba.
Sannan a kan ko wannensu daga cikinsu akwai, hular sarauta wacce aka Sanya mata koriyar lulu’ii.
A wani hadisi daga Imam Bakir (a) daga manzon All..(s) yana cewa: A ranar kiyama za’a kawo diyata Fatima kan wani rakumi daga cikin rakuman aljanna, … har zuwa inda yace…, tare da ita akwai mala’iku 70,000 daga damarta, sannan da wasu dubu 70,000 daga hagunta, Sai jibirilu ne zai ja linzaminta, sannan ya yi kira da babban muryansa, yace: Ku sunkuyar da kawukanku. Fatima diyar Muhammad(s) za ta wuce’. A lokacin babu wani annabi ko manzo ko salihin bawa, ko shahidi, sai ya sunkuyar da kansa har ta wuce.
Sannan sai ta ce: Ya Ubangiji na! kuma mai jibintan al-amari na! ka hukunta tsakanina da wadanda suka zalunce ni. Ya All.. ka hukunta tsakanina da wadanda suka kashe da na, sannan za’a ji murya daga wajen All..T mai girma na cewa: Ya masoyiyata, diyar masoyi na, ki roki abinda kike so zan baki.
Ki yi ceton duk wanda kika ga dama zan baki cetonsa. Na rantse da ikona da kuma buwayata, ba zan bar wani zaluncin wani azzalumi ba.
Sai tace: Ya Ubangijina kuma majibincin al-amari na, ina son ceton zurriyata, masu bi na, da wadanda suka bi zurriya ta,! Da kuma wadanda suke so na, suke kuma son zuriyyata.
Sai murya ta zo daga Ubangija tana cewa: Ina zurriyar Fatimah(s) da kuma wadanda suka bita, da wadanda suke sonta suke son zurriyarta. Sannan za su fito, sannan mala’ikun rahama su kewayesu. Sannan Fatimah(s) za ta jagorancesu zuwa aljanna.
6-An karbo daga manzon All..(s) danagne da zance All..T inda yake cewa: {Bã su jin sautin mõtsinta alhãli kuwa sũ madawwamãne a cikin abin da rãyukansu suka yi marmarinsa. Firgitar nan mafi girma, bã zã ta baƙantã musu rai ba. Kuma malã’iku na yi musu marãba (sunã cẽwa) “Wannan yininku nẽ wanda kuka kasance anã yi muku wa’adi da shi} Anbiya Aya ta 101-102.
Sai yace: Sai Fatimah diyata, ta shiga Aljanna, da zurriyarta, da shi’arta da kuma ‘ya’yansu wadanda aka san basa cikin shi’arta. Sune All..T yake cewa {Firgici babba ba zai sa su bakin ciki ba} sai yace: Ita ce ranar kiyama. {Kuma suna dawwama a cikin abubuwan da ransu ke sha’awa}:
Ita ce, Fatimah da zurriyarta da shi’arta, da wasu daga cikin ‘ya’yansu wadanda ba shi’arta ba.
Amma duk tare da wadannan ayoyin Alkur’ani da ingantattun hadisai daga manzon All..(s) wadanda muka kawo, wadanda kuma suka tabbatar da cetonta a ranar kiyama, sai da aka sami wasu wadanda suke cewa ba wanda zai cece wani, ceto na All..me kawai,
Muna iya cewa, akwai wasu wadanda suke ganin cewa, waliyyan All..T ba zasu yi ceto ba, kai hatta manzon All..(s) ba zai yi ceto ba a ranar kiyama a wajensu.
Suna kuma kafa hujjoji da ayoyin Alkur’ani wadanda suka fahincesu a hakan. Sunan cewa ay neman ceto daga wanin All..T shirka ne, ko kuma ya sabawa tauhihi. Kamar ceto yana kira ne zuwa ga shirka.
A halin yanzu ka karanta Ayoyin alkur’ani mai girma, wadanda suka yi magana akan ceto. Sannan ka yi hukunci da kanka.
{Wa zai yi ceto daga wajensa in ba da izininsa ba?}Anbiya 25, a wata ayar, yana cewa.
{Ba zasu ceci wani ba sai wanda ya amince} Maryam 87, a wata ayar, yana cewa.
{Ba bu wani mai ceto sai da izininsa} Bakara 255, a wata ayar, yana cewa.
{Basu mallaki ceto ba, sai wanda ya sami alkawali daga mai Rahama} Yunus 3. a wata ayar, yana cewa.
{A rannan, ceto ba zata yi amfani ba, sai ga wanda Mai Rahama ya yi wa izini} Taha 109, a wata ayar, yana cewa.
{Ceto ba zata yi amfani a wajensa ba, sai ga wanda ya yi wa izini} Sabah 23, a wata ayar, yana cewa.
{Cetonsu ba zai amfana da kome ba, sai bayan All..ya bada izini ga wanda ya ga dama} Annajam 26.
Dubi wadannan ayoyi zaka ga a fili, suna tabbatar da ceto ga wadanda All..ya basu izinin yin haka, don haka akwai masu ceto wadanda ba All..ba, amma da izininsa zasu yi ceto.
Shin a gaskiya, wadannan ayoyi basu isa su tabbatar da cewa waliyyan All..suna ceto a ranar kiyama ba?, suna ceto hatta kafin ranar kiyama kamar yadda zamu gani a nan gaba.
Idan muka koma kan ceton bayan All..da waliyyansa, ga wasu bayinsa masu sabo a duniya, ko kuma su yi masu addu’a, da nemawa masu sabo gafara daga All.., suma suna da yawa.
Da farko ga wadannan ayoyin alkur’ani mai girma dangane da hakan.
{Kuma dã dai lalle sũ a lõkacin da suka zãlunci kansu, sun zo maka sa’an nan suka nẽmi gãfarar Allah kuma Manzo ya nẽma musu gãfara, haƙĩƙa, dã sun sãmi Allah Mai karɓar tũba Mai jin ƙai.} Annisa 64.
Wannan ayar a fili take, kan cewa idan wani musulmi ya zalunci kansa, sannan ya tuba, sannan ya zo wajen manzon All..(s) ya kama kafa da shi ya nemi cetonsa, sannan manzon All..ya nemam masa gafara, to tabbas zai sami All..mai yawan gafara ne mai rahama.
Da a ce, tawassuli da manzon All.. (s) shirka ne, da kuwa, ba zasu sami All..mai yawan gafara kuma mai jinkai ba. Don All..baya gafartawa wadanda suka yi shirka da shi.
02-Zancen All..T ya na bada hikayar annabi Ya’akubu (a) da yayansa a lokacinda suka aikata laifi na sayda Yusuf (a). inda suke cewa
{Ya babammu! Ka nema mana gafarar zunubammu, Lalle mun kasance masu kuskure}.
Da kuma zancen Ya’akub (a) ga yayansa kan cewa {Da sannan zan nemam maku gafarar Ubangijina} wannan a fili yake, ‘Ya’yan annabi Ya’akub (a) sun roki babansu, sun kuma kama kafa da shi, sun yi tawassuli da shi, sannan shi kuma ya amince, ya nemam masu gafara daga Ubangijinsa.
A nan, inda tawassuli ko neman ceto daga bayin All..T shirka ne, da annabawa da manzanni basu yi su ba.
3- A wata aya, All..T ya umurci manzonsa (s) ya yi istikfari ga kansa ga kuma muminai, inda yake cewa
{Ka nemi gafara ga zunubanka, ga kuma muminai}, a nan zamu ce manzon All..(s) baya zunubi, istigfarinsa kara daukaka ne a gareshi, sannan ya nemam wa muminai gafara, ya na nufin ceto, ya na nufin tawassuli da shi don neman afwa da kuma gafarar zunubansu daga wajen All..T.
Da haramun ne ga bayin All..su nemi gafara ga wasu masu zunubi daga All..T laifi ne! ko kuma shirka ne, da All..bai umurcesu da haka ba.
4 –A wata ayar yana cewa:
Ka yi salati a garesu don lalle salatinka nutsuwa ce garesu}. Salati a nan yana nufin addu’a. don haka All..T ya umurci manzonsa (s) yayi addu’a ga mumunai, addu’a kuma ta hada da istigfari da waninsa. Don haka kamun kafa ko neman ceto daga bayin All..don samun gafararsa ba laifi ne ba. Da laifi ne da All..T bai umurcesu da su ba.
05-a wata ayar yana cewa {Wanda yayi ceto, ceto mai kyau, zai sami rabo a cikinta}
A wannan ayar a fili yake, All..T yayi amfani da Kalmar ‘shafa’a’, wacce suke inkari, yace duk wanda yayi ceto mai kyau yana da rabo a cikin ceton da ya yi.
Idan da yin ceto laifi ne da All..ba zai yabesu ya kuma basu lada da rabo mai yawa a kansa ba.
Wannan kadan ke nan daga cikin ayoyin Alkur’ani mai girma wadanda suka halatta ceton, masu zunubi, a duniya ko a lahira, kamar yadda muka gani a hadisan shafa’ar Zahra (s) a ranar kiyama.