Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttari, ko kuma cikin littafin Mathnawai na maulana jalaluddin Rumi ko kuma dai ciki wasu littafan da fatan masu sauraro za su kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar shuwagabannin samarin Aljanna, Alhassan da Alhussain(a) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar yadda aka yi jana’izar Zahra (s) a asirce a cikin dare. Kuma an yi haka ne saboda wasiyyar da ta bari, kan kada wasu wadanda suka cutar da ita su yi mata sallah.
Sannan mun ji irin yadda rayuwar Amirulmuminina Aliyu dan Alitalib (a) ya kasance bayan wafatin ko shahadar Zahra (s), inda ya bar fitowa daga gidansa gaba daya, sai zuwa sallar Jama’a ko kuma ziyarar kabarin manzon All..(s).
A cikin yan kwanakin da yake zaman makokin Zahra(s), Ammar dan Yasir (r ) ya shiga wajesa, ya kuma same shi yana kuka, Alhassan da Alhussain (a) suna zaune tare da shi, a dama da hagunsa. Sai ya ce masa. Ya shugabana: Ku kuke fada mana, mu yi hakuri a kan musibun da suka samemu, amma menen baci kincin mai tsawon da kuke yi, kan rashin Zahra(s). Sai ya ce masa: Ya Ammar samuwar Zahra (s) shi yake sa mu hukuri kan rashin Manzon All..(s). Don maganarta, kamar maganar manzon (s) ne, sannan tafiyarta kamar tafiyar manzon All..(s), don haka wafatin ta ne ya sa mun fahinci cewa manzon All..(s) ya yi wafati.
A cikin shirimmu na yau zamu fara magana dangane da matsayin Fatimah Azzahra (s) a ranar kiyama. Da kuma daukakar da All..zai yi mata a gaban mutane a ranar kiyama.
Duk da cewa wasu sun kaskantata(s) a nan duniya, sun ki kuma kula da matsayin da take da shi a rayuwarta ta duniya, musamman bayan wafatin mahaifinta manzon All..(s), amma All… T ya kiyaye mata matsayinta a duniya da Lahira.
Wasu basu kiyaye mata matsayin da All..T ya bata a cikin ayoyin alkur’ani mai girma ba. Daga ciki har da Ayar tsarkakewa, wacce ta bayyana matsayinta da na mijinta da kuma yayanta (s) na tsarki daga aikata zunubi. Da ayar Mubahala, wacce ta bayyana matsayinsu gaba daya a wajen All..T. Da suratu Hal’ata, da (ayar mawadda), ko son dangi na kusa da sauransu.
Kamar basu ji zancen mahaifinta manzon All..(s) inda yake cewa, “Ana kiyaye hakkin mutum ne, ta ‘ya’yansa’. Ko kuma inda yake cewa “Fatimah tsokace daga garenim wanda ya cutar da ita ya cutar da ni’.
Da wasu hadisai da dama, wadanda manzon All..(s) ya yi wasiyya ga al-ummarsa dangane da diyarsa tilo, da ya bari a bayansa, amma ba’a kiyaye masa hakkinsa a cikin al-amarinta a bayansa ba.
Amma All..T ya kiyaye mata matsayinta, ya kuma daukakata darajarta, a duniya da Lahari. Ya sanyata shugaban matan duniya da kuma aljanna a Lahira. All…T zai bayyanawa mutane darajojinta a ranar kiyama. Daraja wacce Hatta Maryam diyar Imrana (s) mahaifiyar annabi Isa (a) bata kai matsayin ba. A ranar da All..T zai tada azzalumai da kuma fir’aunoni, a gaban halittu gaba daya, suna kaskantattu, a rannan ne, zai bayyana matsayinta (s).
Ga wasu daga cikin hadisan da suka bayyana matsayinta a ranar kiyama.
01-Hakim Nishaburi ya kawo a cikin littafinsa ‘Mustadrak Assahihaini’ JZ na 3 shafi na, 153, tare da isnadinsa zuwa wajen Aliyu dan Abitalib (a), Yace: na ji manzon All..(s) yana cewa: (Idan an yi ranar kiyama, mai kira (a baye) zai yi kira Yace: Ya ku taron ma’abuta Kiyama!, ku runtsa idanunku daga barin, Fatimah diyar Muhammad zata wuce”.
Daga Aliyu (s) daga manzon All..(s) ya na cewa: Idan ranar kiyama ta kasance, wani mai kira zai yi daga, boyayyen wuri, a cikin al-arshi: Ya ku masu taron kiyama, ku runtsa idanunku, don Fatimah diyar Muhammad(s) ta wace. Zata wauce, tare da riga wacce aka jikata da jinin Alhussain (s). Sai (Fatima ta rike wani ginshiki daga ginshikan al-arshi sai tace: Ya All.. kai ne Al-jabbaru, mai adalci, ka yanke hukunci tsakanina da wadanda suka kashe da na, sai All..ya yi hukunci da sunnata.’
Sannan ta sace, Ya Ubangiji ka bani ceton wanda ya yi kuka kan kisansa, sai All..T ya bata cetonsu.
Sannan zarandi ya kawo a cikin littafin, Nazmul Durarul Simtaini, da kuma Muttaki hindi a cikin ‘Kanzul Ummal, da sabbag Al-maliki cikin ‘Fusul-Almuhimma’, duk sun kawo wannan hadisin.
02-A wani hadisi daga Abu Ayyubar Ansari, ya na cewa manzon All..(s) yace: Mai kira zai yi kira, a wani wuri a boye daga ginshikin al-arshi, yana cewa: Yaku masu tsayuwar kiyama, ku sunkuyar da kawukanku, ku runtsa idanunku saboda Fatima diyar Muhammad(s) ta wuce kan siradi. Sai yace: sai ta wuce da hurul aini 70,000 kamar walkiya.
Wannan kadan Kenan daga cikin hadisan da suka zo dangane da matsayin Fatimah (s) a ranar kiyama.
Yanzun kuma sai hadisan shafa’ar da zata yi a ranar kiyama. Wadanda suka zo cikin littafan sunnan da shi’a.
01-Da farko an karbo hadisi daga Abu Ayyubal Ansari ya na cewa na fadawa Baban Jaafar Imam Muhammad Bakir (a): Raina fansarka, ya dan manzon All..(s), bani labarin falalar kakanka Fatimah(a) wacce idan na fadawa shi’anku zasu yi farinciki da shi.
Sai baban Jaafar (s) yace: Babana ya fada mani, daga kakana manzon All..(s) ya na cewa: Idan ranar kiyama ta kasance za’a kafawa annabawa da manzannin mimbarori daga haske, sai ya kasance mimbari na ya fi sama da nasu daukaka].
Sannan All..ya ce na yi khuduba, sai na yi khuduba, wacce annabawa da manzanni basu taba jin irinta ba.
Sannan a kafawa wasiyyan (annabawa da manzanni) mimbarori na hasake, sannan a kafawa Wasiyyi na Aliyu dan Abitalib Mimbari, a tsakiyar mimbarorin wasiyai, sannan mimbarinsa zai kasance sama da nasu.
Sannan a ce: Ya Aliyu ka yi khuduba, sai yayi khuduba wacce ba’a taba jin wani wasiyi yayi irinta ba.
Sannan a kafawa yayan annabawa da manzanni mimbarori, a nan sai a kafa mimbarori ga yayana, kuma jikokina, furen idanuna a lokacin rayuwata, mimbarori daga haske, sai a ce masu suyi khuduba, sai suyi khudubobi wadanda ba’a taba jin irinsu daga yayan annabawa ba.
Sannan wani mai kira zai yi kira, kuma shine mala’ika Jibriru ya ce: Ina Fatimah diyar Muhammad(s)? Sai ta tashi,…har zuwa inda yake cewa… Sai All..mai girma da daukaka ya ce: Ya ku taron kiyama, waye mai dauka a yau? Sai Muhammad da Aliyu da Alhassan da Alhussain (s) su ce: tana ga All..makadaici mai buwaya.
Sai Ubangiji ya fadawa mutanen taron kiyama: Lalle ni na sanyawa Muhammad da Fatimah da Aliyu da hassan da Hussain daukaka.
Sannan Ya ce: Ya masu taron kiyama, ku sunkuyar da kawukanku, ku runtsa idanunku, ga Fatima nan, za ta wuce zuwa Aljanna.
Sai mala’ka Jibrilu ya zo mata da taguwa daga cikin taguwowin Aljanna, wadanda aka kawata fika fikansa da lulu’u, sai ta hau sannan a hada ta da, mala’iku 100,000 ta dama da wasu dubu 100 ta hagunta. Sai su tashi da ita har su kaita kofar aljanna, a nan sai ta waiwaya, sai All..T ya ce mata ya diyar masoyina me yasa kika waiwaya, ga shi, na ce a kai ki aljanna, Sai ta ce ya ubangiji ina son a san matsayina a wannan ranar.
Sai All..T yace: Ya diyar masoyina! Ki koma ki duba ki gani, duk wanda , ya ke sonki ko yake son yayanki ki shigar da shi aljanna.
Sai Baban ja’afar (a) ya ce: Na rantse da All..ya Jabir, a wannan ranar za ta tsamu shi’arta da masoyanta, kamar yadda tsuntsu yake stintar kwayoyin hatsi masu kyau daga marasa kyau. Idan dukan shi’armu sun kasashence a kofar aljanna, sai a sanya masu tunanin waiwayawa, idan sun waiwaya, sai All..T ya ce: Ya masoya na, ! me ya sa kuka waiwaya? Ga shi kun sami ceton Fatimah diyar masoyi na?
Sai su ce Ya Ubangiji,! Muna son a san matsayimmu a wannan ranar!. Sai Ya ce: Ya masoyana!, ku koma ku duba, ku gani, daga cikin wadanda suke sonku don son Fatimah (a).
Ku dubi, wanda ya ciyardaku don Fatimah(s), ku dubi wanda ya tufatar da ku don son Fatimah(s), ku dubi wanda ya shayardaku kanfata guda, don son Fatimah(s), ku dubi wanda ya kare mutuncinku a gaban mai giibarku sau guda saboda son Fatimah(s). Ku kama hannayensu ku shigar da shi Aljanna.