Kissoshin Rayuwa Fatima Azzahra(s) 77

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo makun kissoshi wadanda suka

Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo makun kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma sikin wasu litafan wadanda suka hada da littafin Datane rastan na Aya. Shaheed Muttahri, ko kuma littafin Mathnawai na Maulana Jalaluddeen Rumi, ko kuma wasu littafan daban. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au.

///.. Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun fara kawo maku, takaitaccen sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s), sannan mahaifiyar Alhasan da Alhussain shuwagabannin samanrin Aljanna.

To masu sauraro a ci gaba da kawo maku taikaitaccen abubuwan da muka yi magana a kansu a sirar Fatima Azzah (s) mun bayyana yaddda manzon All..(s) yake girmamata, sannan yana tashi tdaye a duk lokacinda ya shigo wajenta, ya sumbanci hannut ko gohinta sannan a jiyeta a inda ya tashi.

Wannan irin girmamawan da kuma son, basu taso saboda soyayyar dake tsakanin mahaifi da diyarsa ba, sai dai don irin matsayinda take da shi a wajen All..T. da kuma cikin al-ummar mahaifinta manzon All..(s).

Sannan mun bayyana cewa manzon All…(s) idan zai yi tafiya mai nisa, wato zai bar Madina zuwa wani wuri inda zai yi kwanaki ko watanni, to yakan, sanya Fatima mutum na karshe wacce zai yi sallama da ita, daga nan sai ya kama hanya, haka ma, idan ya dawo daga Tafiya yakan sanya itace na farko da zai fara haduwa da ita su gaisa, ya kuma fada mata ya dawo.

Sannan munji cewa  a shekara ta 7 bayana hijirta manzon All..(s) ya yaki yahudawa Khaibara, ya kuma sami nasara a kansu, sannan yahudawan Fadak, bayan sun ga irin nasaran da manzon All…(s) ya samu kan yahudawan Khaibara, sai suka tsorata, suka aikawa manzon All..(s) sako a kan cewa suna son sulhuntawa da shi kada ya yake su, sai ya amince. Don haka a cikin sulhun da suka yi dashi sun bashi gonar dabono ta Fadak.

A lokacinda hakan ya faru sai All..ya saukar da ayoyi na rabon dukiya, sai ya sanya dukkan dukiyan da ya shiga hannun manzon All..ba tareda yayi amfani da makami don samunsa ba, kamar yadda ya faru da gonar fadak to na manzon All…shi kadai sauran mumunai basa da rabo a cikinsa.

Don haka sai gonar fadak ta zama da manzon All..(s). sannan daga bayan All..ya saukar da watan aya inda yake umurtan manzon All..(s) ya bawa makusanta hakkinsu.

{Wa ati zalkurba hakkahu}, bayan haka a lokacinda manzon All..(s) ya koma madina sai shigo wagen Fatimah (s) kamar yadda ya saba. Sai ya fada mata ya sami gonar Fadak, a matsayin dukiyarsa shi kadai banda sauran mumunai, sannan ya fadawa Zahra na baki gonar, gareki da kuma zurriyarki. A wani hadisin an cewa, ya ce mata, Khadiza mahaifiyarki yana bi na sadakinta har ta yi wafati ban biyata ba, don haka ki karbi gonar Fadak a matsayin sadadin mahaifinki Khadiza (s) .

Don haka zahara ta na samun amfanin wanan gunar shekaru kimani 3 kafin wafatin manzon All..(s), amma bayan wafatinsa Khalifa na farko ya kwace gonar ya ce, na manzon All..(s) ne, kuma ta zama ta jama’a.

Don haka bayan wafatin manzon All.,..(s) matsaloli da dama suka tasawwa Zahra, gashi an kwace, khalifanci a hannun mijinta, sannan gas hi an kwace gonarta ta fadak, kuma duk kokarinta tayi na su dawo mata da hakkinta sun ki amincewa.

Daga nan ne sai Ta yi shahrerren khudubarta a masallacin manzon All..(s). A gaban khalifa na farko, inda a cikin ta tabo batun gonar fadak, ta tabo batun gadonta, ta tabo batun khalifancin mijinta da aka kwace.

Sai  dai an fi sanin khudunar da “Fadakiyya” saboda ta yi maganar gonar fadak a cikinta.

Sannan ta fita tare da mijinta da kuma Yayanta Alhassan da Alhussain (s) a cikin wasu darere suna bin gida-gida na sahabban manzon All..(s) suna neman taimako a wajensu, kam khalifancin mijinta da aka kwace da kuma dukiyarta da aka rike. Ba wadanda suka amsa kiranta sai yan kadan.

A nann ne sai ta koma gina tana koka dare-dare da rana, har sai mutanen Madina suka kai korafinsu ga Aliyu dan Abitalib (a) kan cewa ta hanasu barci da dare, ta hanasu nutsuwa da rana. A lokacinda ya fada mata, sai tace ba zata bar kuka ba dare dara, amma sai Aliyu (a) ya gina mata rumfa a makabartan Bakiyya, inda take yini tana kuka a wajen da rana sai ta dawo gida da dare tare da yayanta Alhassan da Alhussain.

Sannan a lokacinda dukkan wadannan al-amura suka faru, sai ta kamu da rashin lafiya ta karshe a rayuwarta, ta rame, har sai da ta zama kasusuwa da fata.

A ranar da zata yi watafi, sai tayi mafarko ta ga manzon All…(s). inda a cikin mafarkin ta ga babanta a cikin wata fada wacce aka ginata da duwatsun lulu’u, yana fada mata, ya diyata, ina shaukin ganinki, sai ta bashi amsa da cewa, ya babana ni nafi shukin haduwa da kai. Sai yace mana to kina tare da mu a wannan daren. Sai ta farka  daga mafarkin.

Daganan kuma ta tabbatar da cewa zata mutu a daren babu wani shakku a cikinsa. Sai ta samu kuzari da karsfin tashi daga kan shamfidanta, tana dafa bongo ta fita, ta je inda suke ajiye ruwa a gidan, sai ta ja wasu daga cikin kayakin yayanta tana wankewa, sai ta kari yaynta tana wanke kawukansu.

A wannan halin ne sai Imam Ali (s) ya shigo wajenta, sai ya sameta a waje tana ayyukan gida, sai yayi mamaki. Sannan sai ya tambayeta, me ya tadake daga shimfidarki, sai ta bashi amsa, kan cewa yau ce ranata ta karshe a duniya, sai ya tambayeta, daga ina kika samu wannan labarin sai ta fada masa mafarkin da ta yi.

Dagan a sai ta koma kan gadonta, ta fara tunanin abinda zata yi na yan sa’o’iin da suka rahe mata.

Da farko ta kira mijinta Aliyu dan Abitalib (s), ta ce zata yi masa wasiyyan wasu abubuwan da zai yi mata bayan wafatinta. Sai Aliyu (s) ya zo ya zauna kusa da kanta, sannan yacewa duk wadanda suke cikin dakin su fita.

Daga nan sai ta fara fada masa wasiyunta, da farko ta, idan na mutu, na san cewa dole ka yi aure, don haka ina son ka auri Umamah diyar yaruwata, don zata kula da yayana kamar yadda zan kula da su. Aliyu (s) ya amince.

Kafin mu je gama, mun fada maku cewa Imam ya Aurei Umama kamar yadda matarsa Zahra (s) ta yi masa wasiyya, kuma sun rayu da ita har zuwa shahadarsa, yana khalifan musulmi a shekara ta 40 bayan hijira.

Sannan a lokacinta ya ga cewa zai bar duniya ya kira Umamar ya fada mata cewa, idan zaki yi aure a bayana to ki auri Mugira dan Naufal na Haritha dan Abdul muttalib. Wanda ya kasance dan amminsa ne Haritha dan Abdul muttalib(a).

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa Ummah ta haifammasa da wanda ake kira Muhammaduk Ausad. Wasu kuma suka ce bata haifu ba.

Wasu malaman tarihi sun bayyana cewa Imam Ali yayi haka ne don kada Mu’awiya dan Abisufyan ya aureta bayansa, don jikar manzon All..(s) ce, ta diyasa Zainab(s). yayi amfani da wannan auren don cimma wasu bukatunbsa a duniya.

Wasu sun ce kamar yadda Imam Ali yake zata, haka ya faru. Wato Mu’awiya dan abisufyan bayan ya kwace iko da daular musulunci ya aika mata kan cewa yana son aurenta sai ta ki. Sannan ta je wajen Mugira ta fada mata abinda Imam Ali ya fada mata ko ya aureta har ta mutu a shekata ta 60 bayan  hijira.

Bari mu koma kan wasiyyar Zahra(s), inda ya cewa Imam Ali(s), kuma ina so idan ka yi aure a bayana k aka sanya yini ga matarka sannan yini kuma wajen kula da yayana.

Sannan ta ci gaba tana cewa, bana son ka bar wadanda suka cutar da ni su sallace gawata, musamman Khalifa na farko da kuma Khalifa na biyu. Sannan ka boye inda kabari na yake banason tsaya ko kan kabarina. Da sauran wasiyanta mai tsawo wanda muka kawo masku.

Sannan munji yadda, Zahra (s) bayan ta kammala wasiyanta tace a hada mata ruwa ta yi wanka, bayan haka ta sanya wata sabuwar riga da take da shi, sannan ta ce a yiu mata shimfida a wani, wuri , ta je ta kwanta a wurin tana jiran mala’ikar mutuwa. Tare da ita a lokacin akwai Asma’u diyar Uamais matar Khalifa na fako a lokacin, sannan matar Jaafar dana bi talib kafin haka, sannan matar Aliyu dan Abitalib (s) bayan mutuwar Khalifa na farko.

Sannan ta bawa Asma’u diyar Umais umurni kan cewa idan ta mutu kada ta bar wasu daga cikin matan babanta manzon All..(s) su zo kanta daga ciki har da ummil A’isha. Amma tace a fadawa ummil muminian Ummu salma idan ta rasu.

Kuma haka ya faru, asma’u ta Hana Ai’isha shiga wajenta bayan wafatinta, ta kai karenta wajen babanta Khalifa nafarko, ya zo ya tammayi Asma’u , sai tace wasiyyar Zahra ce (s). sai ya ce mata ta bi umurnin Fatimah (s).

Sannan a lokacinda mutuwa ta zo mata, sai tana fadawa Asma’u da wadanda suke tare da ida, abinda take gani, na al-amuran lahira, mala’ika jibrulu da babanta da wasu al-amura gaibu sai irinsu zasu gani sanan ta yi addu’o’inta na karshe aka ga ta yi shiru.

Har’ila yau mun bayyana cewa a lokacinda ta rasu Aliyu dan Abitalib da yayansa Alhassan da Alhussain (s) basa wajenta.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au, sai kuma a cikin shirimmu na karshe, zamu kammala abinda ya rage na sirar Zahra (s). wassalamu alikum wa rahamatullhi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments