Kissoshin Rayuwa, Fatima Azzahra (s) 65

65-Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo

65-Assalamu alaikummasu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahad Murtadha Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana Jalaluddeen Ruma ko kuma dai cikin wasu littafan.  Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Fatimah Azzahra (s) diyar manzon All..(s) sannan mahaifiyar Alhassan da Alhusain (a) shuwagabannin samarin Aljanna, da muke kawo maku, mun bayyana yadda Khalifa na farko da na biyu suka zo gidan Zahra(a) bayan sun sami labarin cewa ba ta da lafiya, don neman afwarta, amma taki da basu izinin shiga wajenta.

A wasu hadisan an bayyana cewa sun yi ta zuwa sau da dama, amma ta ki amincewa su shiga wajenta. Daga karshe dai sun yi tawassuli da Amirul muminina (s) don ya shigarda su wajenta, inda ya yi masu alkawalin zai shigar da su, sai dai a lokacinda ya shiga wajenta (s) ya kuma fada mata cewa suna son shiga wajenta sai taki amincewa, sannan ya ce mata, amma na yi masu alkawali zan shigo da su wajenki. Da ta ji haka, sai tace to, tunda ka yi masu alkawali za ka shigo da su, gida-gidanka ne kuma mata suna bin mazaje ne, ni kuma ba zan saba maka cikin wani al-amari ba. Don haka ka shigo da wanda kaga dama.

Daga nan Imam Ali (s) ya shigo da su wajen Zahra (s), a lokacinda ta gansu sai ta juya fuskanta ta bongo, sun yi sallama amma taki amsa sallamarsu. Amma suka matsa, sai tace masu idan na fada maku wani abu da kuka ji wajen manzon All..(s) zaku gasgata ni, sai suka Eee: Sai tace masu: shin baku ji manzon All..(s) ya ce : Fatima diyata, tsoke ce daga gareni, wanda ya fusatata ya fusatani, wanda ya nemi yardarta ya nemi yardata…har zuwa karshen hadinsin. Sai suka amsa: Ee, sai ta ce:

Ya Ubangiji, ka shaida, wadannan sun fusata ni, basu nemi yardarta ba…har zuwa karshen addu’ar da ta yi, sannan ta ce zata yi uddu bayan duk wata sallah da tayi a kansu.

A nan sai suka fita daga wajenta, Khalifa Abubakar yana kuka , a yayinda Khalifa Umar kuma yana zarginsa da rashin cancantar shugabanci, saboda yana kuka saboda maganar abinda ya kira (macce), don ta yi fushi da shi.

Daga karshe, mun bayyana cewa, a gaskiyar al-amarin ba su zo neman yardarta da gaske ba, saboda basu mayar mata abinda suka kwace daga hannunta ba, wanda kuma ita ce gonar Fadak, basu kuma bata gadonta daga manzon All..(s) da ta nema ba. Sannan basu mayarwa mijinta Aliyu dan Abitalib (a) hakkinta na shugabancin al-ummar manzon All..(s) da suka kwace ba, ta yaya suke son ta gafarta masu?

Daga nan sai Ummu sallam, matar manzon All..(s) ta ziyarceta a lokacinda ta fara rashin lafiya ta karshe. Wani abu dangane da Ummu Salman ( R) matar manzon All..(s) shi ne, tana daga cikin matan manzon All..(s) mafi daraja a wajensa (s) a lokacin rayuwarsa da kuma bayan wafatinsa(s). Don haka ita kadai ce, daga cikin matansa (s) wacce a fili, ta ke bayyana goyon bayanta ga iyalan gigan manzon All..(s) a bayan wafatinsa (s).

A shirimmu na baya kun ji maida martaninta, ga khalifa na farko bayan khudubarsa a masallacin manzon All..(s) inda a ciki ya ke aibata,  da kuma mijinta Aliyu dan Abitalib(s), saboda rikita masa al-amura bayan da al-amuran shugabanci bayan sun tabata a gareshi.

Ummu Salma (r ) ta ce masa. Ta yaya manzo All..(s) zai san cewa su annabawa ba’a gadonsu, amma kuma bai fadawa wacce itace kadaice za ta gajeshi in banda matansa.?

Sannan a wannan karon ma ita kadaice, a abinda ya tabbata a garemu, wacce ta ziyarci Zahra(s) a lokacinda take rashin lafiya ta karshe. A lokacinda ta shiga wajenta sai tace mata : Ina kwanakinki ya diyar manzon All..(s)?,  sai ta amsa da cewa: Na wayi gari cikin bakin ciki da bacin rai, an rasa Annabi (s) kuma an zaluncin wasiyyinsa,  

 Na rantse da All..an keta hurumin wanda shugabancinsa ya zama wajibi a kan mutane, ba tare da wata hujja ta shari’a wanda aka saukar ba, ko manzon All..(s) ya Sanya shi sunnan a cikin tawilin alkur’ani ba, sai dai al-amarin hasada ce na abinda ya faru a yakin Badar, da kuma daukar fansar abinda ya faru a yakin Uhudu. Wanda zukatan munafukai suka  tabbata a kansu ..) har zuwa karshen maganarta (s).

Kamar yadda muka fada, a iya sanimmu, Ummu Salma ce kadai daga cikin matan manzon All..(s) suka ziyarci Zahra (s) a lokacin da labarin rashin lafiyarta ya watsu cikin madina. Ko me yasa saura basu zo ba, bamu sani ba. Fatima (s) ce kadai manzon All..(s) ya bari daga cikin yayansa maza da mata, sannan ita kaidai ce ta haifu daga cikin yayansa.

Banda haka, nan gaba zamu gani kan cewa, Fatimah (s) ta bar wasiya, kan cewa a fadawa Ummu Sallam (r), labarin wafatinta idan ta rasu.

Sai kuma A’isha diyar Talha ta ziyarci Zahra (s) a lokacin rashin lafiyarta ta karshe, a lokacinda ta shigo wajenta, sai ta same ta, tana koka, sai ta ce: Iyayena fansaki! Me yasa kike koka? Sai Tace: Kina tambayata kan wace masifa ce ta hana tsuntsu tashi, ta kuma hana mazaje tafiya?  Wannan al-amarin wanda aka kai shi sama?, Sannan aka sanshi sosai a kasa?.

Su biyu, sun amince da Baban Hassan a baya,  amma duk da haka sun boye kiyayyarsu  gareshi, matukar iyawarsu, basu bayyana shi ba. Amma bayan da hasken addinin ya dushe, tare da wafatan annabi (s) amintacce, suka bayyana abinda suke boye a cikin zukatansu, suka bayyana mummunan kiyayyarsu, suka kwace gonar Fadak, bone ya tabbata ga wanda ya kwace gonar Fadak, Lalle (gonar Fadak} kyauta ce daga Ubangiji mai daukaka ga manzonsa(a) amintacce, sannan ya bani ita, don kula da bukatun zurriyarsa daga yayana, kuma lalle wan nan, yana daga cikin ilmin All..da kuma shaidar manzonsa(s) amintacce, don haka idan sun dauke ta daga gareni, abinda ya kasance na kula da bukatun yayana,? suka hanani ita, zan nemesu da ita a ranar kiyama, kuma a nan ne Lalle zasu fahinci cewa, sun cinye narkekken karfe ne, wanda yake kuna a cikin wutan jahannama.’.

Sai kuma Abbas dan Abdulmuttalib (r ), ammin manzon All..(s) ya yi kokarin ziyartar Zahra(s), a lokacin rashin lafiyarta ta karshe. Amma a lokacinda ya zo sai aka ce masa, tana cikin wani halinda ba za ta iya Magana da kowa ba. Sai ya koma gida, amma ya aiki wani dansakonsa zuwa wajen Amirulmuminina (a) ya fada masa cewa: Ya dan dan uwana, amminka yana sallama a gareka, kuma yana cewa: Na rantse da All..bakin ciki ya same ni da rashin lafiyar masoyiyar manzon All..(s), .. har zuwa inda yake cewa: Ina zaton itace za ta rika mu haduwa da manzon All..(s), ya zabeta, kuma zai kusanto da ita ga Ubangijinta.

Idan wani abu ya faru da ita, (wato ta rasu,) ka fada madi in tattara maka muhajirun da Ansar, don hakan zai kasance abu ne mai kyau ga addini.

Sai Aliyu (a) ya fadawa dan sakon Abbas dan Abdul-Muttalib (r ), wanda kuma shi ne Ammar dan Yasir, yace: Ka fadawa ammina, ina gaida shi sannan ka ce masa: Na gode da tausayinka, da gaisuwarka, kuma na fahinci shawararka,.. Lalle Fatimah diyar manzon All..(s), bata gushe ba, tana wacce aka zalunceta,  an hanata hakkinta, kuma an hanata gadonta, kuma ba’a kiyayewa manzon All..(s) wasiyarsa dangane da ita ba, ba’a kula da mutuncinsa a cikin al-amarinta ba, har’ila yau basu kiyayewa All..T..mai girma da daukaka a cikin al-amarinta ba.

All…ya isa mai hukunci, kuma shi zai dauki fansa, daga azzalumai, kuma ina rokonka, Ya ammina, ka bar batun shawarar da ka bani, don ta yi wasiya gareni kan in ‘boye al-amarinta.).

A lokacinda dan sakon Abbas ya fada masa sakon Aliyu (s) sai yace: All..ya gafartawa dan dan’uwa na. shi abin gafartawa ne, kuma ba’a sukan ra’ayinsa, don ba’a haifarwa Abdulmuttalib da wanda ya fi shi daukaka da al-barka kamar Aliyu ba, sai manzon All..(s).

Lalle Aliyu bai gusheba, shi ne wanda ya riga kowa daukaka. Kuma yafi kowa jihadi a kan makiya, sannan ba wanda ya fi shi taimakawa addinin gaskiya, kuma shi ne na farkon wande ya yi Imani da All..da kuma manzonsa (s).

A rana ta karshe, ga Zahra (s) a wannan duniyar, ta kasance a kwace kan gadonta, a rame, ba abida ya rage a jikinta sai kasusuwa.

A cikin wannan halin ne da rana, sai ta yi barci kadan, inda a cikin barcin ta ga mahaifinta manzon All..(s), mai yuwa shi ne ganinta a gareshi na farko tun bayan wafatinsa, a cikin barci.

Ta ga babanta a cikin wata fada wacce aka ginata da ‘farin lulu’u’, sai yace mata: Ya diyata ki zo gareni, ina shaukin ganinki.

Sai tace masa: Ai wallahi, ni nafi shaukin haduwa da kai(ya babana). Sai ya ce mata: kina tare da ni a cikin wannan daren.

Daga nan ta farka daga birci, sai ta fara Shirin tafiya zuwa lahira. Saboda ta ji daga mahaifinta, mai gaskiya, abin gasgatawa, kan cewa (wanda yayi mafarki ya ganni, to ya ganni da gaskiya), ta ji labarin wafatinta daga bakin mahaifinta, don haka babu wata shakka ko kokwanto a cikin gaskiyar abinda ta ji ta kuma gani.

A cikin wannan halin ne, Zahra(s) ta bude idanunta, tana tunanin abinda za ta yi a cikin dan lokacinda ya rage mata, ta gabatar da abinda ya zama lazimi ta yi kafin ta tafi, ta bar wannan duniyar, wacce take cike da bakin ciki. Banda haka ta tuna da kalaman mahaifinta, kan cewa, su iyalan gidan manzon All..(s) kaskantattu ne a bayansa, kuma wadanda za’a zalunta ne.

Don haka ta fara tunanin mijinta wanda zata bari a nan duniyar, da bakinciki, da ci gaba da kasancewa cikinta. Tana tunanin wacece zata maye gurbinta, wacce zata goya masa, baya kamar yadda ta kasance.? Sannan ga yayanta nan, har yanzun basu girma ba, girmanda zasu iya yiwa kansu kome ba.?

Tana irin wannan tunanin sai ta mike daga kan gadonta, sai ta nufi waje, tana jingine a kan bonkon dakin,  har ta je inda suke ajiye ruwa a gidan, sai ta dauki wasu daga cikin tufafin yayanta ta fara wankesu, sannan ta kira yayanta, ta fara wanke kansu. Sannan ta kira yayanta sana wanke kansu. A cikin wannan halin ne sai Amirul Muminina Aliyu dan Abitalib (s) ya shigo wajenta, sai ya ga abinda take yi, sai ya fara tunani me yasa Zahra (s) ta tashi daga gadon ta, a cikin wannan halin na rashin lafiya?, Sai ya tambayeta, me yasa ta tashi daga shimfidar .? Sai ta amsa masa da cewa: Yau ne rana ta, ta karshe a duniya, sai ya tambaye ta daga ina kika samo wannan labarin, sai ta fada masa mafarkin da ta yi.

To masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau, sai kuma wata fitowa idan All..ya kai mu, wassalamu aikum warhamatullahi wa barakatuhu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments