Ministan harkokin wajen kasar Katar Majid Bin Muhammad al-Ansari ne ya bayyana cewa;mun isa zango na karshe na kulla yarjejeniya akan Gaza,abinda ya saura shi ne matakai daya bayan daya akan yadda za a aiwatar da ita.
Ministan harkokin wajen kasar ta Katar ya kuma ce, muna fatan jin labari mai dadi dangane da yarjejeniyar ta Gaza, domin dai ya zuwa yanzu mun tsallake muhimman abubuwan da ake da sabani akansu da suke hana a cimma yarjejeniyar.
Ministan harkokin wajen na kasar Katar ya kara da cewa; Da zarar an gama cimma matsaya akan komai, to za mu sanar da fara aiwatar da ita.
Minista Majid Bin Muhammad al-Ansari, ya ce, a halin yanzu ana cigaba da tattaunawa a birnin Doha, don haka muna jiran samun sabon labari daga masu tattaunawar.
Haka nan kuma ministan na Katar ya ce, mun karbi daftarin tsagaita wutar yaki,kuma tattaunawar da ake ci gaba da yi a yanzu ta shafi cikakken bayanin karshe ne na yadda za a aiwatar da ita.
.