Wadanda suke shirya Italian Expo Sun ki gayyatar HKI kasuwar baje kolin kasar wanda za’a gudanar a cikin watan satumba mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya bayyana cewa a lokacinda kasar amurka tana bawa HKI dukkan tallafin da suke bukata, amma masu zanga-zanga a kasashen yamma suna kara karfi, sannan hukumomi da dama a kasashen yamma suna nisantar wannan gwamnatin mai kashe jarirai.
Labarin ya kara da cewa a dai-dai lokacinda HKI tare da tallafin Amurka ke ci gaba da kissan kiya shi a gaza, inda ya zuwa yanzo ta kashe akalla mutane 62000 sannan tana kara kashesu da yunwa, manya-manyan mutane da kuma wasu gwamnatocin kasashen yamma sun fara daukar matakan kauracewa gwamnatin yahudawan ko ta ina. Za’a gudanar da Italian Expo ne a ranakun 13-21 na watan satumba mai zuwa.