Kashim Shettima Ne zai wakilci Najeriya a babban taron M D D

mataimakin shugaban najeriya ne zai wakilci kasar a taron babban zauren majalisar dinkin duniya karo na 3

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da cewa ba zai halarci babban taron Majalisar Dinkin Duniya na 81 da za a gudanar a New York na Amurka ba, inda ya bukaci Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya.

Kashim Shettima zai yi tattaki New York domin wakiltar Najeriya a babban taron da muhawarar shugabannin kasashe da za ta gudana daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Satumba.

Sanarwar mai taimakawa mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai Stanley Nkwocha, ta canza abin da aka sanar tun farko, bayan da jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Jimoh Ibrahim, ya ce Tinubu ya amince da halartar taron tare da gabatar da jawabi.

Wannan zai kasance karo na uku a jere da Shettima ke wakiltar Tinubu a babban taron na Majalisar Dinkin Duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted