Francesca Albanese, yar rahoton MDD ta musamman a kasar falasdinu da aka mamaye ta sha suka daga kasashen turai bayan wani jawabi mai zafi da tayi a birnin Doha na kasar Qatar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wata kungiya mai suna Aljazeera Org. ce ta shirya taron.
Albanese ta soki HKI kan kissan kiyashin da ta aikata a gaza take kuma ci gaba, sannan ta hada har da kasashen da suke bada makamai da taimako a kan ayyukan laifuka da ta aikata take kuma ci gaba da aikatawa.
Kasashen Faransa Jamus, Austria da Italia wadanda suke goyon bayan HKI ido a rufe sun bukaci Albanese ta sauka daga mukaminta a MDD saboda aibata HKI da ta yi. Da kuma aibatasu wadanda suke goyon bayanta da kuma taimaka mata kan wannan ta’asar da ta aikata a Gaza.
A cikin Jawabinda yar rahoton ta kira HKI da kalamar ‘common enemy’ wato makiyin kowa.
Giovanni Russo-Spena tsohon dan majalisar dokoki na turai, ya ce a dai dai lokacinda ake kara fallasa Asiran Esstein, shuwagabanin turai suke kara nuna goyon bayansu ga HKI musamman wadanda suke jin tsoron a fallasasu.