Kasashen turan nan guda uku da ake wa lakabi da E3, sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake tsakanin Iran da Amurka.
Ministan Birtaniya mai kula da yammacin Asiya Hamish Falconer ne ya bayyana hakan inda ya ce Birtaniya tare da Faransa da Jamus na goyon bayan sasanta batun nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya.
A cikin sakon da ya wallafa, Falconer ya yaba da tattaunawar da akayi a babban birnin kasar Oman na Muscat a matsayin “muhimmiyar mataki na farko.”
Kuma a cewarsa “Birtaniya, tare da kawayenta na E3, a shirye suke don tallafawa tattaunawar.
A cikin 2018 a lokacin mulkinsa na farko, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma a baya kan shirin nukiliyar Iran da kuma lafta mata tsauraren takunkumai amma kuma ya nuna aniyar kulla sabuwar yarjejeniya don maye gurbin waccen ta 2015.