Babban Daraktan Hukumar IAEA, Zai Ziyarci Iran ranar Laraba

Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  zai ziyarci Tehran a ranar Laraba mai zuwa. Ziyarar ta Grossi na zuwa ne gabanin sabuwar tattaunawar da za’ayi tsakanin Iran da Amurka a ranar Asabar mai zuwa kan batun shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin […]

Aljeriya ta yi barazanar korar jami’an diflomasiyyar Faransa 12

Rikicin diflomasiyya tsakanin Paris da Algiers na dada kamari, inda Aljeriya ta bukaci wasu jami’an diflomasiyyar Faransa 12 da su fice daga kasar cikin sa’o’i 48. Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya sanar cewa, Aljeriya ta bukaci jami’an diflomasiyyar Faransa da su fice daga kasar bayan kama wasu ‘yan kasar Aljeriya uku a Faransa. […]

Kasashen Turai na E3 sun goyi bayan tattaunawar Iran da Amurka

Kasashen turan nan guda uku da ake wa lakabi da E3, sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake tsakanin Iran da Amurka. Ministan Birtaniya mai kula da yammacin Asiya Hamish Falconer ne ya bayyana hakan inda ya ce Birtaniya tare da Faransa da Jamus na goyon bayan sasanta batun nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya. […]

Iran, Iraki Sun Karfafa Dangantakar Makamashi

Kasashen Iran da kuma Iraki sun kudiri anniyar karfafa alaka ta fuskar makamashi. A ganawar da suka yi a birnin Bagadaza, kasashen biyu sun jaddada fadada hadin gwiwar dake tsakaninsu a fannin mai da iskar gas, inda kasar Irakin ta bayyana matukar sha’awar yin hadin gwiwa a fannin fasaha da zuba jari da Jamhuriyar Musulunci […]

Gaza: Mutane 38 Sun Yi Shahada A Yau Litinin

Majiyar asibiti a yankin Gaza, ta ambaci cewa an sami karuwar shahidai a cikin sassa mabanbanta na zirin Gaza zuwa 38, 3 daga cikinsu a yankin Deir-Balah. Jiragen yakin HKI sun kai wasu hare-hare akan wata mota da take dauke da wasu ‘yan’uwa shakikai su 6, da hakan ya yi sanadiyyar shahadarsu baki daya. ‘Yan’uwan […]

A Kasar Gabon Brice Oligui Nguema Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda ya tsaya takarar shugabancin kasar, ya lashe zabe da kawo 90.35% kamar yadda sanarwar ma’aikatar cikin gida ta sanar. Brice Nguema ne dai ya jagoranci juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Ali Bango a watan Ogusta na shekarar 2023, ya kuma shiga cikin ‘yan takarar shugabancin […]

Sojojin Yemen Sun Kakkabo Jirgin Yakin Amurka Wanda Ake Sarrafa Shi Daga Nesa Na 19

Sojojin kasar Yemen sun kakkabo jirgin yakin Amurka wanda ake sarrafashi daga nesa samfurin MQ-9 na 19 a jiya Lahadi da yamma a sararin samaniyar kasar. Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ya bayyana cewa sojojin kasar ta Yemen sashen UAV wato masu kula da abinda ake kira ‘Drones’ sun bada sanarwan kakkabo jirgin […]

Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne […]