A bayanin da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar a yau, ta yi tir da harin da sojojin na “Isra’ila” su ka kai wa kauyen Beit-Jin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13.
Bayanin ya kara da cewa; Harin, yana a matsayin keta hurumin shugabancin kasar Syria da kuma dokokin kasa da kasa.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Qatar ta kuma ce, abinda “Isra’ila” take yi yana kara yawan zaman dar-dar din da ake ciki a wannan yankin.
Da safiyar yau Juma’a ne dai sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kutsa cikin garin Beit-Jin a gefen birnin Damascuss, inda ta bude wuta akan mutanen kauyen da ya kai ga kashe 13 daga cikinsu da jikkata wasu.
Ita kuwa ma’aikatar harkokin wajen kasar Jordan ta bayyana cewa; Abinda ya faru keta hurumin kasar Syria ne da kuma dokokin duniya.
Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Jordan, Fu’ad al-majali ya ce, harin na Isra’ila wata tsokana ce mai hatsarin gaske da zai kara matsala akan wacce ake da ita a wannan yankin.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Jordan ta bayyana cewa, dole ne a kawo karshen hare-haren da Isra’ilan take kai wa akan kasar Syria, da komawa aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta ta 1974.