Rahotonnin sun bayyana cewa: Yayin da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila take fama da matsalar tattalin arziki bisa la’akari da hare-haren wuce gona da iri kan Gaza, kasashen Larabawa na kara yawan kayayyakin da suke fitarwa zuwa gare ta.
Hukumar Kididdiga ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Kasashen Larabawa biyar sun kara yawan kayayyakin da suke fitarwa zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila tun daga ranar 7 ga watan Oktoban bara.
Bayanan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a hukumance sun bayyana cewa: Kasashen biyar da suke karfafa haramtacciyar kasar Isra’ila a fuskar tattalin arziki duk da bullar yakin Gaza sun hada dakasar Hadaddiyar Daular Larabawa, Masar, Jordan, Moroko da Bahrain.
Bayanai a hukumance daga mahukuntan haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Kayayyakin da kasashen biyar din suke turawa zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila sun zarce kudi dalar Amurka biliyan biyu a cikin watanni takwas da suka gabata.
Kamar yadda Hadaddiyar Daular Larabawa ita ce kasar da ta kara habaka huldar kasuwanci da gwamnatin mamayar, sai Masar, sai Jordan, sannan Moroko, sannan kasar Bahrain a matsayar kasa ta karshe.