Iran Da Kasashen Larabawa Sun Yi Tir Da Hare-Haren Isra’ila A Kan Kasar Siriya

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai

Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana.

A cikin bayani da ya fitar a jiya jumaa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghai ya jadda game da hakkin kasashe a yammacin asiya na kare martabar su da yankunansu game da wuce gona da irin Isra’ila.

Har ila yau yayi suka game da kasa tabuka komai da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan hare haren da isra’ila ke kai wa kan wasu kasashe kamar labanon da siriya wanda hakan keta hurumi da mutuncin kasahen ne.

Kakakin yayi barazanar cewa yanayi da ake ciki yana da matukar hadari ga zaman lafiya da tsaro na duniya, don haka yana kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin da ya dace wajen shawo kan alamuran tun kafin allura ta hako galma.

Ana sa bangaren ministan harkokin wajen kasar Qatar yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki matakin gaggawa na dakatar da Isra’ila ci gaba da hare-haren da take kaiwa domin kare fararen hula.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments