Kasashen Iran Da Tunusiya Sun Jaddada Karfafa Alaka A Tsakaninsu A Bangarori Da Dama

Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi Ministocin harkokin

Ministan harkokin wajen kasar Iran da takwaransa na Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falasdinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi

Ministocin harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tunisiya sun jaddada cewa: Warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamaya da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu.

Wannan dai na zuwa ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi da ministan harkokin wajen kasar Tunisiya Mohamed Ali Nafti suka yi a ranar Laraba a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar ‘yan ba ruwan mu ta NAM karo na 19 a birnin Kampala na kasar Uganda.

A yayin wannan ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan ci gaban da aka samu a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da suka hada da shirye-shiryen taron hukumar tattalin arziki ta hadin gwiwa, tare da tabbatar da aniyar kasashen biyu na karfafa alaka da hadin gwiwa a dukkan fannoni.

Har ila yau, sun yi musayar ra’ayi kan abubuwan da ke faruwa a yankin yammacin Asiya da kuma mamaye Falastinu bisa fahimtar da aka cimma a Masar na dakatar da kisan kare dangi. Sun jaddada nauyin da ke wuyan kasashen da ke ba da tabbacin hana yahudawan sahayoniyya karya yarjejeniyar da aka cimma.

An jaddada cewa warware matsalar Falastinu na bukatar kawo karshen mamayar da ake yi da kuma tabbatar da hakkin al’ummar Falastinu na cin gashin kansu, sannan kuma wajibi ne a bin doka da oda da kuma wajibi kasashe su goyi bayan al’ummar Falastinu wajen aiwatar da wannan muhimmin hakki da ‘yantar da kansu daga mamaya da kuma kangin fuskantar nuna wariyar al’umma da kuma mulkin mallaka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments