Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan wata makaranta a zirin Gaza inda mutane sama da 100 suka rasa rayukansu.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta yi Allah wadai da harin da kakkausan murya tare da jaddada “bukatar dakatar da kisan kiyashin” a data danganta da bala’in da ba a taba ganin irinsa ba saboda ci gaba da keta dokokin kasa da kasa.
Ita Qatar ta hanyar ma’aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah wadai da harin tana mai bayyana shi a matsayin “mummunan kisan kiyashi da kuma mummunan laifi kan fararen hular da ba su da kariya,”
Masar, ma ta yi tir da harin, tana mai cewa “kisan” na da gangan da Isra’ila ta yi wa al’ummar Falasdinu da ba su dauke da makami ya tabbatar da rashin kyakywar niyyar gwamnatin kasar na kawo karshen yakin Gaza.
Turkiyya, kuwa ta ce harin wanda abun Allah wadai ne, na a matsayin wani sabon laifi na cin zarafin bil’adama.
Ita ma Iran ta bakin Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Nasser Kan’ani ya yi Allah wadai da harin bam din da Isra’ila ta kai a makarantar da ke yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta yi Allah-wadai da mummunan harin da Isra’ila ta kai a makarantar Gaza, inda ta ce irin wadannan hare-haren na kawo cikas ga kokarin da kasashen duniya ke yi na dakile yakin, da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta cikin gaggawa da kuma musayar fursunoni.
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi Allah wadai da harin tana mai dangata shi a matsayin “tsawaita kisan kiyashi da Isra’ila ta yi na tsawon fiye da watanni goma a zirin Gaza.”
Tarayyar Turai, ta bakin Babban jami’in kula da harkokin waje na kungiyar Josep Borrell, ya ce “ya firgita” da hotunan harin na Isra’ila, inda ya kara da cewa an kai hari a kalla makarantu 10 a cikin makon da ya gabata.
“Babu wata hujja ga wadannan kisan kiyashin,” in ji Borrell akan X.