Kasashen duniya 22 sun bukaci Isra’ila da ta dawo da agaji gaba daya a Gaza

Kasashen duniya 22 sun bukaci Isra’ila da ta gaggauta dawo da cikakken tallafin da take baiwa zirin Gaza. Tireloli tara na taimakon jin kai na

Kasashen duniya 22 sun bukaci Isra’ila da ta gaggauta dawo da cikakken tallafin da take baiwa zirin Gaza.

Tireloli tara na taimakon jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ne aka ba su izinin shiga zirin Gaza a ranar Litinin, wanda ake wa kallo a matsayin digo ‘’ digo a cikin teku,” in ji shugaban kula da ayyukan jin kai na MDD, Tom Fletcher.

Al’ummar Zirin Gaza suna “fuskantar yunwa” kuma “dole ne su sami taimakon da suke bukata,” in ji ma’aikatun harkokin waje na kasashen Australia, Canada, Denmark, Estonia, Finland, Faransa, Jamus, Iceland, Ireland, Italiya, Japan, Latvia, Lithuania, Luxembourg, Netherlands, New Zealand, Norway, Portugal, Slovenia, Spain, Sweden, da United Kingdom.

Kasashen da suka rattaba hannu kan bukatar sun ce, “Bai kamata a rika siyasantar da taimakon jin kai ba.”

Isra’ila ta sake farmawa zirin Gaza ne a ranar 18 ga watan Maris, bayan karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta cimma da kungiyar Hamas.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a ranar Litinin cewa Isra’ila za ta “karbe ikon gabadayen” yankin zirin Gaza.

Ko a jiya Hukumar kare fararen hula a Gaza ta sanar cewa Isra’ila ta kashe mutane 91 a rana guda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments