Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da kai hare-hare har sau 20 akan Sanaa da Hudaidah, tare da Amurka da Birtaniya.
Tashar talabijin din HKI ta 12, ta ce HKI tare da Amurka da Birtaniya sun kai hare-haren ne a cikin zango uku akan wuraren mabanbanta da su ka hada runbunan karkashin kasa na boye makamai masu linzami da kuma jiragen sama marasa matuki.
Kafafen watsa labarun na HKI sun ce an kai hare-haren ne da jiragen yaki 20 an kuma jefa bama-bamai 50.
A can Yemen tashar talabijin din ‘almasirah’ ta ce hare-haren wuce gona da irin da aka kai, sun shafi cibiyar samar da wutar lantarki a birnin San’aa, haka nan kuma dandalin “Sab’in’ da dubun dubatar mutane kan taru domin yin tir da yakin Gaza.